Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ƴan bindiga sun ce a ba su kuɗi su ciyar da ɗaliban da suka sace a Kaduna

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Halima Umar Saleh and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin sanin abubuwan da suka faru a duniya a ranar Laraba

  2. An samu ƙaruwa a yawan yaran da ake cin zarafinsu a Yammaci da Tsakiyar Afirka

    Asusun Kula Da Yara Na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce an samu matuƙar ƙaruwa a yawan yaran da ake cin zarafinsu a sasan Yammacin Afrika da Tsakiyar Afrika.

    Asusun na UNICEF ya ce kashi daya bisa uku na duk manyan laifukan da ake yi wa yara na faruwa ne a waɗannan yankuna.

    Asusun ya kuma ce an yi awon gaba da yara 500 a Najeriya a cikin makoni shida.

    An kuma samu rahotannin da ke cewa an ci zarafin yara sama da 3,400 a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo a farkon watanni uku na shekarar da muke ciki.

    Asusun UNICEF ya ce ya damu matuƙa da cewa matsalar cin zarafin yara za ta ƙaru a makonni masu zuwa kafin ruwan sama ya taƙaita zirga-zirgar mayaƙa masu riƙe da makamai.

  3. Trump ya maka Twitter da Google da Facebook kotu

    Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kai kamfanonin Twitter da Google da Facebook kotu kan toshe shafukansa da suka yi.

    Trump ya ce ƙarar kuma ta shafi shugabannin kamfanonin guda uku.

    A watan Janairu aka dakatar da shafukan Trump kan dalilai na kaucewa tunzura jama’a musamman bayan tarzomar Capitol da magoya bayansa suka yi har suka abka majalisa.

    A ranar Larabawa, Mista Trump ya kira ƙarar da ya shigar a matsayin “ci gaba mai kyau ga ƴancin fadin albarkacin baki.”

    Trump ya nemi kotu ta kawo ƙarshen tace bayanansa. Ya ƙara da cewa idan har za a iya dakatar da shugaban ƙasa, “za su iya yi wa kowa.”

    Zuwa yanzu kamfanonin ba su mayar da martani ba a ƙarar da aka shigar a kotun Florida.

  4. Ƴan bindiga sun ce ba su da abincin ciyar da ɗalibai sama da 100 da suka sace a Kaduna

    Ƴan bindiga da suka sace ɗalibai sama a 100 daga wata makarantar kwana a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Litinin sun ce suna buƙatar abincin da za su ciyar da yaran.

    Iyaye da ke cikin ɗimauta da damuwa sun ce ƴan bindigar sun faɗa masu cewa kuɗin fansa zai biyo baya.

    Shugaban makarantar sakandaren ta Bethel Baptist High School, Rabaran Ishaya Adamu Jangado ya ce ya yi magana da ƴan bindigar da wasu daga cikin ɗaliban da ake garkuwa da su a jiya Talata.

    Ya ce ana jin yaran suna kuka suna rokon a kuɓutar da su.

    Sama da ɗalibai 1,000 ƴan bindiga suka sace domin neman kuɗin fansa a Najeriya a bana.

  5. Muna goyon bayan kafa rundunar ƴan sanda ta jihohi - Dattawan Arewa

    Ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya wato Northern Elders Forum ta ce tana goyon bayan yunƙurin ƴan majalisar dokokin ƙasar ke yi wajen zartar da dokar da za ta bai wa jihohi ikon kafa rundunar ƴan sanda ta jiha.

    Tuni dai aka yi wa ƙudurin dokar karatu na biyu a majalisar wakilai.

    An dade ana taƙaddama a kan batun kafa ƴan sandan jihar, sakamakon zargin da wasu ke yi cewa gwamnoni za su yi amfani da su wajen yaƙar abokon hamayyarsu.

    Sai dai a tattaunawarsu da Ibrahim Isa, Kakakin kundiyar Dattawan Arewan, Dr Hakeem Baba Ahmed

    ya ce ƴan sandan za su taimaka wajen inganta tsaro idan aka bi tsari wajen kafa rundunonin nasu.

  6. Jirgin ruwan da ya tare Mashigar Suez ya bar Masar a yau

    A yau ne katafaren jirgin ruwan dakon kayan nan da ya rufe mashigar ruwa na Suez a Masar, har ya janyo cikas ga harkokin kasuwanci a hanyar, ya bar kasar.

    Jirgin ruwan na Ever Given ya bar Masar ɗin ne bayan an rattaba hannu kan wata yarjejeniyar biyan diyya da masu jirgin da kuma kamfanin da ya yi musu inshora.

    Shaidu sun ce jirgin ruwan ya bar tashar jirgin ruwan ne da misalin karfe 10.30 na safiyar yau ya nufi tekun Bahar Rum ana janye da shi.

  7. Mutum 200 sun kamu da kwalara a jihar Kano

    Kimanin mutum sama da 200 ne suka kamu da cutar amai da gudawa a ƙauyuka 16 da ke yankin karamar hukumar Rano a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Hukumomi a yankin karamar hukumar Rano sun alaƙanta bullar cutar da gurɓatacen ruwan sha da rashin tsaftar muhalli.

    BBC ta ziyarci ƙaramar hukumar kuma wakilinmu Khalifa Dokaji ya zagaya asibitoci don ganin halin da majinyatan ke ciki.

    A makonnin da suka gabata ne dai Ma’aikatar Lafiya a Kano ta ce daga watan Maris zuwa watan Yunin da ya gabata mutum sama da dubu uku ne suka kamu da cutar amai da gudawa a jihar, kuma mutum 100 daga cikinsu sun mutu.

    Faruwar wannan al’amari dai na nuni da cewar duk da matakan da ma’aikatar lafiya ke cewar ta dauka kan cutar ta amai da guda, a iya cewa al’amarin na ci gaba da fantsama zuwa karin wasu kananan hukumomin baya ga 33 da ta ce an sami cutar a watanin da suka gabata.

  8. Kotu ta ce Kemi Adeosun ba ta buƙatar shaidar NYSC don zama minista

    Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke hukunci cewa tsohuwar Ministar Kuɗi, Kemi Adeosun, ba ta buƙatar takardar shaidar kammala Hidimar Ƙasa (NYSC), don zama minista.

    Mai Shari'a Taiwo Taiwo ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba inda ya ce Adeosun - wacce ta yi murabus saboda ce-ce-ku-cen da ya ɓarke kan batun rashin shaidar yi wa ƙasa hidima a shekarar 2018 - ba ta buƙatar shaidar NYSC kafin ta karɓi wani muƙamin siyasa.

    A wannan shekarar an zargi ministar da gabatar da shaidar bogi ta NYSC a cikin takarun shaidar karatunta.

    Yi wa ƙasa hidima wajibi a Najeriya inda dukkan ɗaliban da suka kammala jami'a ke yi na tsawon shekara ɗaya. Bayan an kammala ne kuma ake ba su shaidar kammalawa.

    Sai dai ga waɗanda suka haura shekara 30 ba sa yin NYSC amma ana ba su shaidar cewa shekarunsu sun wuce na hidimar ƙsa don haka ba su yi ba.

    To da irin wannan lamari ne na ba da shaidar cewa shekarun mutum sun wuce yin NYSC aka zargi Adeousn cewa ta samu na bogi.

    Kotun ta kuma yanke hukuncin bayan da tsohuwar ministar ta gabatar da hujjar cewa tana da shaidar zama ƴar ƙasa ta Birtaniya, kuma kundin tsarin mulkim 1979 da ake amfani da shi a wancan lokacin ya nuna ba a buƙatar wanda ba a ɗan Najeriya ba ya yi NYSC.

    Mai Shari'a Taiwo Taiwo ya kuma ce kundin tsarin mulkin ba ya buƙatar ta gabatar da shaidar kammala digirinta na farko da suka haɗa da na NYSC, don karɓar kujerar minista.

    A watan Satumban 2018 ne Adeosun wacce tsohuwar ma'aiakaciyar banki ce ta yi murabus daga muƙaminta.

    Ta ce wasu mutane ne suka ruɗar da ita har ta amince cewa shaidar da ta karɓa bayan ta dawo Najeriya mai kyan ce.

  9. An kashe mutum 18 a wani hari a jihar Adamawa

    Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa kimanin mutum 18 ne suka rasa rayukansu a cikin wani hari da ake zaton ƴan kungiyar Boko Haram ne suka kai yau da safe.

    Lamarin ya wakana ne a ƙauyen Dabna da ke cikin karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

    Sanadiyar faruwar lamarin jama’a na ci gaba da barin yankin zuwa wasu garuruwan daban.

    Maharan sun shiga garin Dabna ne da sanyin safiyar asubahin wannan rana ta Laraba.

    A kalla mutum 18 ne aka sanar da rasa rayukansu a yayin da dama suka samu raunuka.

    BBC ta yi ta ƙoƙarin jin ta bakin jami’an tsaro na ƴan sanda amma ba a dace ba.

  10. Buhari ya yaba wa hukumomin tsaro kan kama Nnamdi Kanu

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yaba wa hukumomin tsaro da na leƙen asirin ƙasar kan kama jagoran fafutukar aware na Biafra IPOB, Nnamdi Kanu da kuma samamen da aka kai gidan Sunday Igboho, mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawa.

    Wannan ne karo na farko da shugaban ƙasar ya yi magana a kan kama Kanu, wanda ɗan Najeriya ne da kuma yake da takardun zama ɗan ƙasa a Birtaniya.

    A wata sanarwa, Shugaba Buhari ya ce hukumomin tsaron sun nuna matuƙar ƙwazo, da basira da kuma barin komai cikin sirri a yayin aiwatar da waɗannan ayyuka.

    Sai dai bai ce komai ba kan batun daga inda aka kama Kanu.

    Kazalika Buhari ya yaba kan samamen da aka kai gidan Sunday Igboho mai cike da ce-ce-ku-ce, inda har ƴan sandan farin kaya suka kashe mutane.

    Ya bayyana Mista Igboho a matsayin mai aiwatar da ayyukan ta'addanci da kawo cikas ga zaman lafiya da sunan yana kare al'ummar ƙabilarsa.

    Maganar da Buharin ya yi na zuwa ne a lokacin da Majalisar Dokokin Birtaniya take shirin fara muhawara a kan mayar da Kanu Najeriya.

    Majalisar ta ce za ta tatttauna batun da ke dabaibaye da mayar da Mista Kanu Najeriya da ma sauran batutuwa.

  11. An ɗaure mutanen da suka yi rigima da ƴar maɗigon da ta yi ɓatanci ga Musulunci a Faransa

    Wata kotu a birnin Paris ta yanke hukuncin daurin gyara halinka na tsawon watanni hudu zuwa shida ga wasu mutum 11, bayan samun su da laifin "muzguna wa" wata matashiya a shafin intanet.

    Matashiyar wadda yar maɗigo ce ta riƙa wallafa bidiyon ɓatanci na addinin Musulunci a kafofin sada zumunta bayan da aka rika zaginta a intanet game da yadda take rayuwa.

    Haka kuma matashiyar da ake kira Mira ta riƙa fuskantar barazanar mutuwa bayan da bidiyon ya bayyana a kafofin sada zumunta.

    Lamarin ya zama wata alama da ke nuni da rigimar da ake yi a kan ƴancin tofa albarkin baki da addini a kasar ta Faransa.

    Ya kuma ce sai da Miss Mila ta sauya gidan da take zama da makaranta don tsaron lafiyarta, kuma kuma an ba ta ƴan sanda domin su ba ta kariya.

  12. An fafata ƙazamin faɗa tsakanin Taliban da sojojin Afghanistan

    An gwabza ƙazamin faɗa a garin Qala e Naw da ke lardin Badghis yayin da sojojin Afghanistan ke ƙoƙarin fatattakar mayakan Taliban da suka kai hari.

    Gwamnan lardin ya ce mayakan Taliban sun shiga cikin garin ne daga wuri uku amma an tilasta musu ja da baya sannan ya musanta rahotannin da ke cewa birnin ya faɗa hannun 'yan Taliban.

    Wakiliyar BBC ta ce a duk lokacin da aka samu ɓarkewar faɗa irin wannan yana isar da saƙo ga sauran gundumomi da larduna a kan su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.

    Wannan ne hari na farko da aka kai wa babban birnin wani lardi tun bayan karuwar rikice rikice a Afghanistan sakamakon matakin da Amurka ta yanke na janye dakarunta daga kasar.

  13. Labaran ranar cikin minti ɗaya

    • Tare da Umar Mikail
    • An kashe Shugaban Ƙasar Haiti Jovenel Moise yayin wani hari da aka kai kan gidansa da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar. Firaministan riƙon ƙwarya Claude Joseph ya ce wasu 'yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka afka wa gidan shugaban da ƙarfe 1:00 agogon ƙasar - 6:00 na safe agogon Najeriya.
    • Wasu sojojin Najeriya biyu sun rasa ransu yayin da wasu 'yan fashi suka tare hanya a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Lawan Shisu Adam, ya ce an kashe sojan ne mai muƙamin manjo tare da wani kurtun soja a ƙauyen Dumdubus da ke Dutse, babban birnin jihar.
    • Shugaban Nijar Mohamed Bazoum zai kai ziyarar aiki Faransa cikin 'yan kwanaki masu zuwa karo na biyu bayan zama shugaban kasa. Mista Bazoum zai tattauna da Shugaba Emmanuel Macron sannan ya shiga taron tattaunawa na ƙasashen Sahel, wanda za a yi ta bidiyo ranar Juma'a.
    • A bangaren wasanni, da karfe 8:00 agogon Najeriya za san wanda zai bi sahun Italiya zuwa wasan karshe na gasar Kofin Turai tsakanin Ingila da Denmark.
  14. Majalisa ta amince Buhari ya ciyo bashin naira tiriliyan 2.3

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince wa gwamnatin Shugaba Buhari ta karɓo bashin naira tiriliyan 2.3 domin cike giɓin kasafin kuɗi na 2021.

    A watan Mayu ne Buhari ya nemi majalisar ta amince ya nemo kuɗin daga ɓangarori daban-daban ciki har da ƙasashe da kuma ƙungiyoyi masu bayar da rance.

    Kazalika, majalisar ta amince da kasafin kuɗi na musamman da Buhari ya gabatar mata na biliyan N895.842,465,917.

    Sai dai kwamitin da ya yi aiki a kan kasafin ƙarƙashin jagorancin Sanata Barau Jibrin ya ƙara yawansa zuwa N982,729,695,343.

    Gwamnati ta yi kasafin ne ƙari a kan babban kasafi na 2021 wanda majalisar ta amince da shi tun farko kan tiriliyan 13.5.

  15. Shugaban Nijar Mohamed Bazoum zai je Faransa a karo na biyu

    Shugaban Nijar Mohamed Bazoum zai kai ziyarar aiki Faransa cikin 'yan kwanaki masu zuwa, a cewar rahoton ActuNiger.

    Mista Bazoum zai tattauna da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Fadar Elysee sannan kuma ya shiga taron tattaunawa na ƙasashen Sahel wato G5 Sahel, wanda za a yi ta bidiyo ranar Juma'a.

    Ƙasashen ƙungiyar sun haɗa da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar.

    Wannan ne karo na biyu da Bazoum zai kai ziyara Faransa tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a watan Mayu.

  16. Ana ce-ce-ku-ce kan umarnin kama tsohon shugaban Afirka ta Kudu da kotu ta yi

    Wajibi ne tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya miƙa kansa ga 'yan sanda zuwa ranar Laraba ko kuma a kama shi, a cewar hukuncin da kotu ta yi a makon da ya wuce.

    Wata Kotun Tsarin Mulki ce ta samu Mista Zuma da laifin raina kotu. Sai dai babu tabbacin abin da zai faru da shi yanzu ganin cewa wa'adin ya kusa cika.

    Mai magana da yawun Gidauniyar Zuma, Mzwanele Manyi, ya faɗa wa BBC Focus on Africa cewa ba ya tunanin cewa za a kama Mista Zuma.

    "Ba ma tunanin za a kama shi saboda an jiyo wanda ya kamata ya kama shi yana cewa yana jiran a gama shari'ar," in ji shi.

    Mista Manyi ya ce Ministan Harkokin 'Yan Sanda Behiki Cele ya rubuta wa kotun cewa zai jira a samu cikakken hukuncin kotu wanda zai ba shi alƙiblar gudanar da kamen.

    Lauyoyin tsohon shugban sun ɗaukaka ƙara domin neman dakatar da umarnin.

  17. Labarai da dumi-dumi, An kashe shugaban ƙasar Haiti Jovenel Moise

    An kashe Shugaban Ƙasar Haiti Jovenel Moise yayin wani hari da aka kai kan gidansa da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar.

    Firaministan riƙon ƙwarya Claude Joseph ne ya bayyana hakan.

    Mista Joseph ya ce wasu 'yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka afka wa gidan shugaban da ƙarfe 1:00 agogon ƙasar - 6:00 na safe agogon Najeriya.

    Rahotanni sun ce an jikkata matarsa a harin.

    "An ɗauki dukkan matakin da ya dace na ci gaba da tafiyar da ƙasa," in ji shi.

    Jovenel Moïse mai shekara 53 ya hau mulki a Fabarairun 2017 bayan Michel Martelly ya ajiye muƙaminsa.

  18. Buhari ya saka wa Janar Farouk Yahaya anini

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saka wa Babban Hafsan Sojan Ƙasa, Manjo Janar Farouk Yahaya, anini a yau Laraba.

    Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo sun saka masa aninin ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    A ƙarshen watan Mayun 2021 ne Buhari ya naɗa Farouk Yahaya a matsayin jagoran rundunar sojan ƙasa bayan wanda ya gada, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya rasu a wani hatsarin jirgin sama a JIhar Kaduna.

    Janar Yahaya na tare da iyalansa a lokacin da aka saka masa aninin.

    Bayan kammala bikin ne kuma Shugaba Buhari ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa, wanda ya ƙunshi ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati da ake gudanarwa duk Laraba.

  19. 'Yan fashi sun kashe soja biyu a Jihar Jigawa

    Wasu sojojin Najeriya biyu sun rasa ransu yayin da wasu 'yan fashi suka tare hanya a Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Lawan Shisu Adam, ya ce an kashe sojan ne mai muƙamin manjo tare da wani kurtun soja a ƙauyen Dumdubus da ke Ƙaramar Hukumar Dutse, babban birnin jihar.

    Cikin wata sanarwa da Daily Trust ta ruwaito, ASP Lawan ya ce sojojin suna kan hanyarsu ta zuwa Jihar Kaduna ne daga Maiduguri.

    "An samu labari da misalin ƙarfe 9:00 na daren 4 ga watan Yuli cewa 'yan fashi sun tare hanyar Kano zuwa Maiduguri a daidai ƙauyen Dumdubus," a cewar sanarwar.

    Sai dai ta ce 'yan fashin sun tsere kafin jami'an tsaron da suka tafi kai ɗauki su ƙarasa, inda suka kutsa cikin daji.

  20. Hamshaƙin tauraron fina-finan Indiya Dilip Kumar ya rasu

    Ɗaya daga cikin fitattun taurarin fina-finan Indiya, Dilip Kumar, ya mutu yana da shekara 98.

    Tauraron wanda sunansa na ainihi shi ne Mohammed Yusuf Khan, ya fara samun aiki a masana'antar a matsayin marubuci amma daga baya ya fara fitowa a fina-finai a 1944.

    Ya fara fitowa ne a cikin wani fim mai suna Jwaar Bhata.

    Kumar wanda ya yi nasarar samun kyautuka fiye da kowane ɗan wasan fim a Indiya ya jima yana shan yabo saboda gagarumar rawar da ya taka a fina-finan takaici da na barkwanci.