Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya ta ƙara gano tarin gas

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau

  1. Ana taro kan yadda za a murkushe ISWAP

    A ranar Litinin ne Ministocin harkokin waje daga sama da kasashe 40 za su yi wata ganawa a Roma, babban birnin Italiya domin tattauna karuwar barazanar ayyukan kungiyar IS a Afirka.

    Yayin da IS ta fuskanci koma-baya a Syria da Iraki, tasirin kungiyar mai ikirarin Jihadi na ci gaba da karuwa a sassan nahiyar Afirka.

    Burtaniya za ta yi alkawarin samar da karin kudaden yaki da reshen kungiyar ta IS a Yammacin Afirka da ke da alhakin tada zaune tsaye a Chadi da Kamaru da kuma Najeriya.

  2. Abin da ya ja aka cire Portugal daga gasar Euro

    Bayan cire Portugal mai rike da kofin gasar kasashen Turai daga gasar, masana sun yi ta bayyana dalilan da suke ganin sune suka kai ga korar kasar daga Euro 2020.

    Wasu na ganin rashin mataimaka da za su buga kwallo kamar jagoran kungiyar Cristiano Ronaldo na daga cikin dalilansu.

    Wasu kuma na cewa duk inda ake neman ‘yan kwallo a duniya Portugal na da su, amma kawai Belgium sun fi karfin Portugal ne, ganin cewa Belgium din ita ce kasa ta daya cikin jerin kasashen duniya da suka fi karfi a duniya.

    A gefe daya kuma gani ake shekarun da suka fara tararwa Ronaldo na daga cikin abubuwan da suka janyo koma baya a Portugal.

    Mafi yawan masu sharhi sun fi alakanta raunin kyaftin din kungiyar Portugal da rashin nasararta.

    A wani sharhi da shafin Goal.com ya yi, ya ce Ronaldo ya buga bugun tazara a gasar Euro sau 27 bai ci ko daya ba, ya kuma buga sau 24 a gasar cin kofin duniya ya ci sau daya kacal, wanda ya ci Sifaniya a baya.