Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Najeriya ta ƙara gano tarin gas

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah ya kai mu

  2. Najeriya ta ƙara gano tarin gas

    Karamin ministan man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya ce kasar ta gano tarin gas da yawansa ya kai zurfin kafa triliyan 206 jibge a karkashin kasa, yayin da ake kokarin hako danyen man fetur.

    Jaridun Najeriyar sun rawaito ministan na cewa kasar na iya gano karin gas din da yawansa ya kai zurfin kafa triliyan 600 idan ta mayar da hankali sosai a nan gaba da zummar cimma burinta na fadada harkar gas a kasar.

    Ministan ya kuma bayyana shirin fadada samar da iskar gas a matsayin "babbar madafar ci gaban tattalin arziki".

    Najeriya ce kasar da ta fi kowace kasa samar da mai da iskar gas a Afirka.

  3. Ƴan sandan Osun sun ce sun kama wadanda ake zargi sun kai wa musulmi hari a masallaci

    Ƴan sanda a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya sun ce sun kama wasu mutane bayan samun rahotannin kai wa wani masallaci hari da wasu masu shigar dodanni suka yi a birnin Osogbo na jihar Osun.

    Bayanai sun ce dodannin sun kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu a wannan harin da suka kai wa masallata a ranar Lahadi.

    Amma shugaban ƙungiyar masu shigar dodannin na Igungun ya musanta zargin inda ya yi ikirarin cewa su aka fara takala.

    Ko da yake, hukumomin tsaron jihar na cewa tuni suka ɗauki matakai kuma yanzu haka ƙura ta lafa.

  4. Da gaske Ganduje na shirin tsige Muhuyi magaji?

    Gwamnatin Kano ta musanta zargin akwai wani yunkurin sauke shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Muhuyi magaji Rimin Gado daga kan mukaminsa.

    Gwamnatin ta Kano ta ce a iya saninta babu wata matsala makamanciyyar da ake yadawa tsakanin gwamnati da shugaban hukumar.

    Ku saurari rahoton Khalifa Shehu Dokaji

  5. Najeriya ta ɗauki mataki kan fasinjan Afirka ta kudu saboda korona

    Najeriya ta ƙara Afrika ta Kudu cikin jerin ƙasashen da aka hana fasinjojinsu shiga ƙasar saboda annobar korona.

    Shugaban hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa Chikwe Ihekweazu ya bayyana ɗaukar matakin saboda yadda nau’in cutar da ake kira Delta ke bazuwa a Afirka ta Kudu.

    Yanzu ƙasar ta bi sahun India da Brazil da Turkiya da Najeriya ta hana shiga cikin ƙasarta.

    Shugaban Hukumar ta NCDC ya ce har yanzu ba a samu ɓullar nau’in cutar Delta ta korona ba a Najeriya.

  6. Samfurin korona ‘ƴar Najeriya’ ta ɓulla a Tunisia

    Rahotanni daga Tunisia sun ce an samu ɓullar nau’in korona da ake kira ƴar Najeriya a Tunisia.

    Kafofin yaɗa labaran Tunisia sun ce an tabbatar da ɓullar cutar ƴar Najeriya ne a ranar Litinin yayin da nau’in cutar da ake kira ƴar Delta ke ci gaba da bazuwa a ƙasar.

    An ambato jami’in lafiya na Tunisia na cewa wani mutum da ya fito daga Libya ne ya shigo da cutar wanda aka kwantar a asibiti.

    A wata sanarwa ma’aikatar Lafiya ta Tunisia ta ce an samu mutum bakwai da ke ɗauke da cutar korona nau’in Delta a yankin Kairouane da kuma mutum 11 a lardunan Tunis, Siliana da Monastir.

  7. Ƙungiyar agaji ta Faransa da Zulum ya dakatar ta faɗi dalilin yin atisayen harbi

    Kungiyar agaji ta Faransa da gwamnatin Borno ta dakatar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya ta ce babu wani ma'aikacinta da ke dauke da bindiga.

    A ranar Asabar ne Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya sanar da dakatar da ayyukan ƙungiyar bayan mazauna kusa da wata otal a garin Maiduguri sun bayar da rahoton jin ƙarar harbin bindiga.

    Hukumomin Borno sun zargi ƙungiyar da koya wa mutane harbin bindiga.

    Amma Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ce a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Lahadi, Acted ta ce tana ƙoƙarin tabbatar da tsaron ma’aikatanta ne a yankin da ke fama da matsalar Boko Haram tsawon shekara 12 “ta hanyar horo da atisaye.”

    Ƙungiyar ta bayyana atisayena matsayin “tsari na ƙungiyoyi da ke aiki a Najeriya da sauran ƙasashe, kuma ma’aikata ba su yawo da bindiga da kuma wurin da ake atisayen,” in ji sanarwar.

  8. Ƙasashen duniya na taro kan barazanar IS a Afrika

    Ministocinharkokin wajan kasashen duniya na gudanar da taro abirnin Roma inda suke tattaunawa akan ƙaruwar barazanar da ake fuskanta daga kungiyar ISa Afrika.

    Kasashe sama da 40 ne ke halartar taron wanda Amurka ke jagoranta.

    Yaɗuwar Kungiyar ISa cikin manyan sassan nahiyar ya tayar da hankalin kasashen duniya.

    Ƙungiyoyi masu alaka da IS na ci gaba da tasiri asassan nahiyar Afrika, musamman a yammaci da Jamhuriyar Dimokuradiya Kongo da kuma Mozambique.

    Amurka ta saka jagororinkungiyar ISa Jamhuriyar Dimokraddiyar Kongo da Mozambique a cikin jerin sunnayen mutanen da ta ke nema ruwa a jallo.

    Birtaniya ta sha alwashinbayar da ƙarin tallafidomin yaƙi da reshen kungiyar ta IS da ke tasiri a Chadi da kamaru da Najeriyaa yankin yammacin Afrika

  9. Hukumar INEC ta bude shafin rijistar katin zabe

    Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce ta bude shafinta na internet ga ‘yan kasar wadanda suka cancanci yin rijista ko gyara katin zabe don su yi da kansu.

    INEC ta ce wadanda suka cancanci yin rijistar za su fara shigar da bayanansu ne ta intanet kafin daga bisani su je kafa-da-kafa su kammala a cibiyoyin rijistar da za a samar nan gaba.

  10. Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe gwamman 'yan Boko Haram da ISWAP

    Dakarun Najeriya sun kashe gwamman 'yan kungiyar ISWAP da Boko Haram, an kuma kashe masu mutum biyu.

    Cikin wata bata-kashi da aka yi a yankin Bula Yobe a karamar hukumar Bama da ke arewacin jihar Borno wasu daga cikin mayakan sun sha da kafafunsu da raunuka jikinsu.

    Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa, wani jami'in tsaro da ta tattauna da shi na runduna ta 21 da ke Bama an ce an share sama da awa biyu ana kai ruwa rana kafin daga bisani a kai ga samun nasarar kashe 'yan bindigar.

    "An yi zargin cewa mayakan ISWAP da Boko Haram daga dajin Sambisa za su zo a kan wasu manyan motocin yaki guda shida daga kusurwa daban-daban da zummar yaki, amma sai suka hadu da karshensu a wajen dakarunmu."

    "Abin bakin ciki muma mun yi rashin bayan da aka samu nasarar maganin wadannan mutanen da aka kora."

  11. Labaran duniya cikin minti daya

    • Babban jami'in kamfanin Twitter a India ya sauka daga aiki a yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin kamfanin na sada zumunta da gwamnatin kasar.

    A kwanakin baya ne aka nada Dharmendra Chatur a matsayin babban jami'in riko na kamfanin.

    • Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce kasar ta samu kudin shiga daga zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar da suka kai naira miliyan 918,662,682.

    Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar na watanni hudun farko na wannan shekarar da ta kwatanta da abubuwan da aka samu a watanni hudun farko da kuma watanni hudun karshe na 2020.

    • Sojoji 52 ne aka hallaka a wani hari da al_shabaab ta kai Wisil a ranar Lahadi, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta.

    Gwamnatin Somalia ta ce dakarunta sun kashe 14 daga cikin maharan.

    • Fitaccan mawakin nan na Najeriya Burna Boy ya lashe gasar kida ta BET ta wannan shekara.

    Wizkid da Diamond Platnumz na kasar Tanzania na cikin wadanda aka fafata da su wajen neman lashe gasar.

  12. Dajin da mata ne kaɗai suke shiga a Indonesia

    A Papua da ke kasar Indonesia, akwai wani daji da mata ne kawai ake bari su shiga.

    Daji ne na musamman mata masu shekaru daban-daban suke zuwa domin tsintar wuri sannan su yi hira a tsakaninsu.

    Idan aka kama maza a cikin dajin, ana cin tararsu. Tawagar ma'aikatan BBC Indonesia ta mata zalla ta samu izinin shiga dajin.

    Wadanda suka daukin bidiyon: Ayomi Amindoni, Yulika Anastasia, Alfonso Dimara

    Latsa hoton da ke kasa domin kallon bidiyon:

  13. Rikicin India da Twitter ya ci rawanin babban jami'in kamfanin

    Babban jami'in kamfanin Twitter a India ya sauka daga aiki a yayin da ake ci gaba da takaddama tsakanin kamfanin na sada zumunta da gwamnatin kasar.

    A kwanakin baya ne aka nada Dharmendra Chatur a matsayin babban jami'in riko na kamfanin.

    Mukaminsa na cikin manyan mukamai uku da ake sa rai duk wani babban kamfanin sada zumunta zai cike a karkashin sababbin dokokin kasar kan harkokin sadarwa na zamani.

    Twitter ba ta ce uffana ba kan saukarsa sai dai ba ta sanya sunan Mr Chatur a shafinta na intanet ba.

    Sababbin dokokin, wadanda a hukumance ake kira dokokin Information Technology (Intermediary Guidelines and Digital Media Ethics Code), an sanya su ne a watan Fabrairu.

  14. Masar ce 'yar tsakiya a yarjejeniyar Isra'ila da Hamas

    Masar ta shiga tsakani a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra'ila da Kungiyar Falasdinawa ta Hamas domin ba da damar kai mai zuwa zirin Gaza daga yau Litinin.

    Wata sanarwa daga jami'in Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya Tor Wennesland ya ce matakin zai taimaka wajen samar da mai a cibiyar hasken wutar lantarki ta Gaza.

    Isra'ila da Hamas wadanda ke jagorantar zirin Gazan tun 2007 sun fada yaki cikin watan Mayu da ya gabata.

    Suna kuma kokarin cimma yarjejeniyoyi kan batutuwan da suka shafi fursunoni.

  15. 'Wakokin Aminu Ala sun zama gagara-badau a fanni nazarin harshen Hausa'

    Masana adabi na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan zuben wakokin shahararren mawakin hausar nan Aminudeen Abubakar Ladan Wato Ala saboda irin rawar da suke takawa wajen bunkasa adabi da harshen hausa.

    Masanan dai sun bayyana haka ne a yayin taron Ga Fili Ga mai Doki da sashen harsuna na jami’ar Bayero kan gabatar a duk shekara.

    Jami’ar Bayero da ke Kano kan gayyato mawaka daga sassa daban-daban na arewacin Najeriya dan yin wakoki tare da amsa tambayoyi daga mahalarta taro don sanin ma’anar wasu adabai da mawakan kan yi amfani da su.

    Aminudeen Abubakar Ladan Ala daya ne daga cikin irin wadan nan mawaka na zamani a arewacin Najeriya da jami'ar Bayeron ta gayyato wajen taro don bajekolin fasaharsa yadda yake amfani da adabi a wakkokinsa.

  16. Najeriya ta samu kudin shiga N918m daga zirga-zirgar jiragen kasa - NBS

    Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce kasar ta samu kudin shiga daga zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar da suka kai naira miliyan 918,662,682.

    Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar na watanni hudun farko na wannan shekarar da ta kwatanta da abubuwan da aka samu a watanni hudun farko da kuma watanni hudun karshe na 2020.

    Rahoton ya ce naira miliyan 892,467,526, daga fasinjojin da suka hau jirgin a watanni hudu na farkon 2021, wanda kari ne mai yawa kan N398,999,290 da aka samu a watanni hudun karshe na 2020.

    An kuma samu irin wannan kudin shiga na kayan da jiragen suka dauka a watanni ukun farko da suka kai naira 26,195,160, wanda shi kuma raguwa ce aka samu idan aka kwatanta da abin da aka samu a 2020 naiara 82,572,300.

    An samu yawan fasinjoji da suka shiga jirgin kasa a watanni hudun sun kai 424,460. adadin yaragu idn aka kwatanta da mutum 647,055.

  17. Ramuwar gayya ce harin da muka kai Iraki - Amurka

    Amurka ta ce ta kai wasu hare-hare ta sama a Iraki da Syria a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren jirgi maras matuki da aka kai kan jami'anta da cibiyoyinta a Iraki.

    Wakilin BBC ya ce wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, John Corby, cikin wata sanarwa ya ce Shugaba Joe Biden ne ya ba da umarnin kai hare-haren a kan iyakar Iraki da Syria.

    Ya kara da cewa Amurka ta yi haka ne domin kare kanta. Masu samar da tsaro kan iyakar Iraki sun ce an kashe kimanin mayaka hudu.

    Harin da Amurkan ta kai ta kai shi ne kan "inda ake ajiye makaman mayakan da ke Iraki" in ji ma'aikatar tsaro ta Amurka.

    Pentagon har yanzu ba ta fitar da bayanan komi ba, sai dai kungiyoyin masu sanya sun ce an kashe mayaka biyar a Syria.

    Kungiyar kare hakkin dan adam da ke bibiyar yaki a Syria ta ce an jiwa mayaka da yawa ciwo a yayin harin saman da Amurka ta kai.

  18. Burna Boy ya lashe kyautar BET karo na uku a jere

    Fitaccan mawakin nan na Najeriya Burna Boy ya lashe gasar kida ta BET ta wannan shekara.

    Cikakken sunan mawakin dai Damini Ebunoluwa Ogulu, kuma ya lashe gasar ne karo na uku a jere.

    Wizkid da Diamond Platnumz na kasar Tanzania na cikin wadanda aka fafata da su wajen neman lashe gasar.

    Burna Boy kuma ya kara da Youssoupha da Aya Nakamura wadanda dukansu daga Faransa suke, sai kuma Emici daga kasar Brazil, da kuma 'yan kasar Burtaniya Headie One da Young T& Bugsey.

    Dan shekara 29 ya yi wa mahaifiyarsa godiya, "matar da ta fi kowacce mace kyau a duniya", a lokacin da yake karbar kyautar a Los Angeles.

    Diamond Platnumz ya godewa mutanen Tanzania saboda hadin kansu - yayin da ake tsaka da korafi akan shi na cewa sai an cire shi daga cikin wadanda suka cancanci shiga gasar.

  19. Al-Shabaab ta yi ikirarin kisan sojojin Somaliya

    Sojoji 52 ne aka hallaka a wani hari da al_shabaab ta kai Wisil a ranar Lahadi, kamar yadda kungiyar ta wallafa a shafinta.

    Gwamnatin Somalia ta ce dakarunta sun kashe 14 daga cikin maharan.

    Wasili na cikin wani bangare na yankin Mudug, mai nisan kilomita 60 daga arewa maso yammacin birnin Hobyo mai cike da tarihi.

    An fara rikicin ne bayan da al-Shabaab ta girke wani bam a gefen titi, kafin yunkurin da ta yi na kwace wani sansani a wurin.

    An kuma kashe fararen hula uku a yyain wannan rikici.

    Awanni kafin fara wannan rikici, masu gudanarwa a yankin Puntland sun zartarwa da wasu mayakan al-Shabaab 21 hukuncin kisa, biyo bayan hukuncin wata kotun soji.

  20. 'Yan bindiga sun kashe mutum 15 tare da kona motoci masu yawa a Burundi

    Akalla mutum 15 ne aka kashe a tsakiyar Burundi, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

    An kai harin ne a ranar Asabar a lardin Muramvya, inda aka kashe mutum 12 a kwatankwacin harin a watan Mayu.

    A cewar wani ganau, 'yan bindigar sun tare titi ne da wasu manyan duwatsu dun da sauran duhun asuba, kafin daga bisani su fara budewa ababan hawa wuta.

    An koma wasu motocin safa-safa guda biyu. An kuma garzaya da wasu masinjoji masu yawa zuwa aibiti.

    Ministan cikin gidan Burundi ya bayyana harin a matsayin na ta'addanci.