Ƙarin mutum 44 sun kamu da korona a Najeriya
Mutum 44 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Laraba, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.
Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa daga jihohi huɗu ne har da Abuja aka samu sabbin kamuwar sannan kuma babu wanda ya rasa ransa.
Jihoihin su ne Legas mai mutum 32, da Rivers mai takwas, sai kuma Abuja da Filato masu biyu-biyu kowaccensu.
NCDC ta ce ya zuwa yanzu mutum 167,375 ne aka tabbatar sun kamu da cutar sannan ta kashe 2,118. Kazalika, an sallami mutum 163,917 bayan sun warke.
Annobar korona ta ɓulla Najeriya ne a watan Fabarirun 2020, wata uku kenan bayan da aka gano ta a ƙasar China.