Rundunar
‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta tabbatar da sace mutane 12 da wasu
gungun yan bindiga suka yi a garin Kachia da ke jihar Kaduna.
Mai magana da yawun rundunar a jihar ASP
Muhammed Jalige ya tabbatar da sace mutanen yayin zantawa da jaridar Vanguard.
Ya ce ''A ranar 23 ga watan Yuni, jiya
kenan, rundunarsu ta samu wani rahoto mara dadi daga Kachia, cewa da daddare wasu
‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, dauke da muggan makamai sun mamaye
mahadar Awon / Mothercat a karamar hukumar inda suka fara harbin kan mai uwa da
wabi.
Ya ce, da samun wannan bayanin, hadin
guiwar 'yan sanda da sojoji da kuma 'yan banga suka durfafi wajen da nufin
tunkarar yan bindigar, amma sai suka tarar sun yi wa mutane hudu rauni, yayin
da kuma suka kashe wani mai suna Hamisu Mikailu, mai shekaru 40 a duniya.
Ya ce sun kuma yi awon gaba da mutane 12,
yayin da su kuma wadanda aka raunata ke ci gaba da karbar magani a asibiti.