Babu 'yan zanga-zanga a Ojota ta Jihar Legas
A Jihar Leags, ana iya ganin 'yan sanda ƙalilan a Ojota, wurin da masu zanga-zanga suka ce za su taru a yau.
Wani jami'in ɗan sanda a wurin ya faɗa wa wakilin BBC cewa tun a daren jiya Shugaba Buhari ya saka hannu kan wata doka da ta haramta gudanar da zanga-zangar. Sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin iƙirarin nasa ba.