Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hukumar alhazan Najeriya za ta mayar wa maniyata kuɗaɗensu

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. Dubban mutane sun yi zanga-zanga yawaitar kisan gilla

    Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar a arewacin Burkina Faso domin nuna adawa da kisan da aka yi wa mutane sama da 130 a makon da ya gabata a ƙauyen Solhan.

    Masu zanga-zangar sun fito saman titi a garin Dori suna kiran gaggauta ɗaukar mataki yayin da ƙasar ke fuskantar ƙaruwar ayyukan ƴan tawaye.

    Kisan gillar da aka yi a Solhan shi ne mafi munin al’amarin da ya faru tun bayan da masu da’awar jihadi suka fara kai hari a Burkina Faso shekaru shida da suka gabata.

    Daruruwan mutane ne aka kashe yayin da kusan miliyan guda suka rasa muhallansu tun fara rikicin.

  3. An ci gaba da wasan Denmark da Finland

    An ci gaba da wasan Denmark da Finland bayan dakatar da wasan sakamakon ɗan wasan Denmark Christian Eriksen da ya fadi ana tsakiyar wasa.

    Hukumar ƙwallon Denmark ta ce ɗan wasan ya farfaɗo bayan ya some a fili

  4. Hukumar alhazan Najeriya za ta mayar wa maniyata kuɗaɗensu

    Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce za ta mayar wa maniyata aikin hajji kuɗaɗensu ba tare da ɓata lokaci ba bayan gwamnatin Saudiyya ta hana ƴan ƙasashen waje gudanar da aikin hajjin bana saboda annobar korona.

    Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce za ta mayar wa duk mai buƙatar kuɗinsa cikin gaggawa.

    Haka kuma ga waɗanda suke son barin kuɗinsu, hukumar ta buƙaci su jira ƙarin shawarwari da kuma matakin da ta yanke.

    Sanarwar kuma ta ce soken aikin hajjin wani al’amari ne da Allah Ya ƙaddara, kuma "hukumar alhazan Najeriya ta karɓi matakin da Saudiyya ta ɗauka."

  5. An kwashi Christian Eriksen ɗan wasan Denmark some a filin wasa

    Ɗan wasan Denmark Christian Eriksen ya faɗi ana tsakiyar wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai Euro 2020.

    Ɗan wasan ya faɗi ne shi kaɗai ba ƙwallo tare da shi a yayin da ƙasarsa Denmark ke tsakiyar fafatawa da Finland a ranar Asabar.

    Zuwa yanzu ba a san halin da yake ciki ba. Amma an kwashi ɗan wasan some a filin wasa.

    An dakatar da wasan sakamakon halin da Christian Eriksen yake ciki.

    Abokan wasansa dukkaninsu sun fice fili suna ƙwalla, wasunsu kuma suna ta addu’a.

  6. Copa America: Mutum 12 sun kamu da korona a tawagar Venezuela

    Gasar kwallon kafa ta Copa America ta sake fuskantar koma baya bayan gwaji ya tabbatar da mutum 12 daga tawagar Venezuela na ɗauke da cutar korona, kwana guda kafin su buga wasan farko da Brazil mai karɓar bakuncin gasar.

    Hukumomin lafiya na Brazil ba su fayyace waɗanda abin ya shafa ba tsakanin ƴan wasa ko jami’an tawagar.

    An sauya Copa America zuwa Brazil daga Argentina da Colombia ba shiri.

    A ranar Alhamis ne aka samu tabbatacin ƙarshe na yiyuwar gudanar da gasar, bayan Kotun Koli ta Brazil ta yi watsi da bukatar soke gasar saboda annobar korona.

  7. Jami’in tsaron Isra’ila ya harbe wata mata Bafalasdiya

    Ƴan sandan Isra’ila sun ce wani jami’in tsaro ya harbe wata mata Bafalasdiya a wani shingen binciken ababen hawa a Yamma da Kogin Jordan.

    Ƴan sanda sun ce matar tana ɗauke da wuka kuma ta ƙi tsaya wa lokacin da aka buƙaci ta yi hakan a mararrabar Qalandiya.

    Ƴan sanda sun ce jami’in tsaron na farin kaya ya harba harsasai da yawa.

    Sun fitar da hoton wata wuka da suka ce matar mai shekara 28 tana dauke da ita.

    Wannan na zuwa kwana ɗaya bayan da aka kashe wani matashi Bafalasdine ɗan shekara 15 yayin arangama da jami’an tsaron Isra’ila a zanga-zangar adawa da gina matsugunan Yahudawa a Yamma da Kogin Jordan.

  8. Krejcikova ta lashe Roland Garros

    Barbora Krejcikova ta Jamhuriyyar Czech ta lashe gasar French Open ɗaya daga cikin manyan gasar Tennis a duniya.

    Krejcikova ta lashe gasar ne bayan ta doke Anastasia Pavlyuchenkova a ranar Asabar.

    Ita ce mace ta farko daga Czech da ta lashe gasar tun Hana Mandlikovaa 1981 lokacin da ta wakilci Czechoslovakia.

  9. Dalilin da ya sa shugabannin kudu ba sa sukar 'yan IPOB - Rochas

    A Najeriya, a yau ne ake bikin cika shekara 22 da komawar kasar kan turbar demokuradiyya, inda mahukunta da `yan kasa ke kididdigar nasarori da kuma kalubalen da kasar ke fuskanta.

    Sai dai bikin wannan karon ya zo a lokacin da Najeriyar ke fuskantar barazana daga `yan kungiyar IPOB, wato `yan kabilar Igbo masu fafutukar ballewa don kafa kasarsu ta Biafra.

    Ana dai zarginsu da kisan mutane da dama, ciki har da jami`an tsaro, da kona ofisoshin `yan sanda da lalata dukiyar jama`a.

    Mahukunta dai na ikirarin daukar matakai da nufin dakile su.

    Amma tsohon gwamnan jihar Imo, kuma dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Rochas Okorocha ya tattauna da Ibrahim Isa a kan wannan batu, kuma ya ce amfani da karfi kadai ba zai magance matsalar ba.

  10. 'Na sadaukar da rayuwata ga Najeriya tun daga ranar da na zama soja'

    Shugaba Buhari na Najeriya ya ce a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don gyaran Najeriya tun daga sanda ya shiga aikin soja.

    Maganar tasa wani ɓangare ne na jawabin da ya gabatar da safiyar yau Asabar, 12 ga Yuni, a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya.

    Tsohon sojan wanda ya mulki Najeriya a shekarar 1983 ƙarƙashin mulkin soja, ya jaddada jajircewarsa wajen "ɗorewar Najeriya ƙasa ɗaya".

    "A matsayin mu na ƙasa, mun yi nisa daga inda muka faro sannan kuma muna ƙara kusantar inda muka sa gaba cikin sauri," in ji shi.

    "Kawo ƙarshen ƙalubalen da muke fuskanta a yanzu hanya da ya zama mu bi ta a matsayinmu na ƙasa saboda mu farfaɗo da ƙarfinmu. Tun daga ranar da na shiga aikin soja na kasance cikin shirin sadaukar da rayuwata ga Najeriya."

  11. APC na wulaƙanta 'yan Najeriya don sun nemi haƙƙinsu - PDP

    Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta yi Allah-wadai da abin da ta kira "murƙushewar da jami'an tsaro ke yi wa 'yan Najeriya masu zanga-zangar lumana" a Ranar Dimokuraɗiyya.

    Da safiyar yau ne masu zanga-zanga suka hau kan tituna musamman a jihohin kudu domin nuna damuwarsu game da halin da Najeriya ke ciki a yankunansu.

    Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kama mutane a Legas tare da harba musu hayaƙi mai sa hawaye kafin daga baya su sake su. A Abuja ma an harba hayaƙin domin tarwatsa su.

    "Jam'iyyarmu ta kwatanta murƙushewar da ake yi wa 'yan ƙasa a matsayin cin zarafin dimokuraɗiyya da jam'iyyar APC ke yi da kuma wulaƙanta 'yan Najeriya musamman a lokacin da suke neman haƙƙinsu," a cewar PDP cikin wata sanarwa.

    Jam'iyyar ta nemi a kawo ƙarshen "saɓa wa kundin tsarin mulki" sannan ta yi kira ga ƙasashen duniya da lura da abin da gwamnatin Buhari ke aikatawa "na take haƙƙin ɗan Adam".

  12. Ra'ayi Riga: Haramta amfani da Twitter a Najeriya

    Ranar Juma'a, 4 ga watan Yuni, gwamnatin Nigeria ta bayar da sanarwar dakatar da shafin sada zumunta na Twitter a kasar.

    Wannan lamari ya janyo cecekuce a ciki da wajen kasar. Yayin da wasu na cewa matakin ya saba doka, wasu kuma na cewa gwamnatin ta yi daidai.

    Batun da muka tattauna kenan a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon, wanda ke zuwa muku duk ranar Juma'a da dare.

  13. 'Yan sanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga a Legas

    'Yan sanda a Jihar Legas sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zanga domin tarwatsa su.

    Jami'an tsaron har wa yau sun kama wasu daga cikinsu kafin daga baya su sake su.

    Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya faɗa wa BBC Pidgin cewa 'yan sandan sun ƙuntata musu kafin sakin su.

    "Na fito ne don gyaran Najeriya. Mun gaji, mun gaji da zalinci da kashe-kashe, kyakkyawar Najeriya muke nema," a cewar wani mai zanga-zanga.

    Masu zanga-zangar sun taru a Ojota da ke ƙwaryar birnin na Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

  14. Gwamnan Zamfara ya dakatar da sarkin Zurmi kan zargin alaƙa da 'yan bindiga

    Gwamnan Jihar Zamfara a arewacin Najeriya ya dakatar da Sarkin Zurmi, Atiku Muhammad, bisa zargin sa da hannu a kashe-kashen da 'yan fashin daji ke yi a yankin masarautar tasa.

    Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta ce Gwamna Bello Matawalle ya kafa kwamatin bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

    Kazalika, an umarci Bunun Kanwa, Bello Suleiman, da ya karɓi jagorancin masarautar nan take .

    Wannan na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan gwamnatin Zamfara ta dakatar da Sarkin Dansadau, Alhaji Hussaini Umar, bisa zargin alaƙa da 'yan bindigar da ke addabar yankin.

  15. Labarai da dumi-dumi, A wani labarin na daban...Mutum 60,000 ne kacal za su yi aikin Hajjin 2021

    Hukumomi a Saudiyya sun ce jumillar mutum 60,000 ne kacal aka yarda su gudanar da aikin Hajji na bana, a cewar shafin Haramain Sharifain mai bayar da bayanai daga masallatan Harami biyu.

    Kazalika, mazauna Saudiyya ne kaɗai za su gudanar da aikin na shekarar Hijira ta 1442, waɗanda suka ƙunshi 'yan ƙasa da kuma baƙi.

    Shafin ya ce an ɗauki matakin ne sakamakon yaɗuwar sababbin nau'uin cutar ta korona a ƙasashen duniya.

    Haka nan, rukunin mahajjata guda uku ne kaɗai za a bai wa damar yin ibadar. Su ne:

    • Wanda aka yi wa rigakafin korona
    • Wanda aka yi wa rigakafi guda ɗaya kuma ya shafe kwana 14
    • Wanda aka aka yi wa rigakafi amma bai gama warkewa ba
  16. An fasa hancin wani ɗan zanga-zangar adawa da Buhari

    An fasa hancin wani mai adawa da Shugaba Buhari bayan da ya yayyaga takardun da magoya bayan shugaban suke ɗauke da su.

    Lamarin ya faru ne a Unity Fountain da ke Abuja a safiyar yau Asabar, inda mutane suka taru domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni.

    Sai dai taron ya koma na nuna goyon baya da kuma adawa da gwamnatin Muhammadu Buhari.

  17. Masu zanga-zanga sun fito a Jihar Rivers

    A Jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya ma masu zanga-zanga sun fito kan titi domin nuna ɓacin ransu game da halin da ƙasar ke ciki.

    Mutanen ɗauke da kwalayen nuna adawa da gwamnatin Buhari, sun fito ne a Fatakwal, babban birnin jihar.

    Suna zanga-zangar ce duk da umarnin da 'yan sandan jihar suka bayar na hana gudanar da ita.

  18. Mun fitar da 'yan Najeriya miliyan 10.5 daga talauci - Buhari

    A jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce gwamnatinsa ta fitar da mutum miliyan goma da rabi daga ƙangin talauci cikin shekara biyu da suka wuce.

    Ya ce: "Ƙudirinmu na cire 'yan Najeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci cikin shekara 10 shi ne muradinmu duk da ɓarkewar annobar korona.

    "Cikin shekara biyu da suka wuce, mun cire mutum miliyan 10.5 daga ƙangin talauci - manoma, ƙananan 'yan kasuwa, masu sana'ar hannu, mata 'yan kasuwa da ire-irensu.

    "Ina da ƙwarin gwiwar cewa waɗannan miliyan 100 da muka sa a gaba za mu cimma su kuma hakan na nuna ci gaban da muka samu a ma'aunin rage talauci. Nan gaba kaɗan za a bayyana ƙarara tsarin da muka bi wajen cimma hakan."

  19. 'Muna tare da Buhari, ku kuma fa?'

  20. 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja

    Rahotanni na cewa 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja, babban birnin Najeriya yayin da suke maci a Ranar Dimokuraɗiyya.

    Mutanen ɗauke da kwalaye, sun fito ne a yankin Gudu da ke ƙwaryar birnin.

    Bidiyo da hotuna da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna mutane na guduwa daga wurin, wasu ma na iƙirarin cewa an harba bindiga fiye da sau ɗaya.