Masu iƙirarin jihadi sun sace gwamman yara a Mozambique
Ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun sace gwamman yara, mafi yawansu mata a shekarar da ta gabata in ji ƙungiyar Save the Children ta Burtaniya.
Ƙungiyar ta ce a ƙalla yara 51 ne aka sace a lokacin rikici da ya raba dubban mutane da muhallansu.
Haka kuma ta ce akwai yiwuwar adadin yaran ya fi haka.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan irin waɗannan sace-sacen na yara inda ta ce abun na ƙara ta'azzara kuma yana da ban tsoro.
Shugaban ƙungiyar ya ce sace-sacen na cikin manyan laifukan da suka shafi cin zarafin yara a lokacin rikici kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ce.
Ƙungiyar ta yi kira da a gaggauta sako yaran sannan a kama kuma a hukunta masu aikata laifin.
Masu iƙirarin jihadi sun kwashe sama da shekara uku suna ayyukansu a arewacin Mozambique, suna sare kan mutane da kai hare-hare a ƙauyuka da birane da ƙona gidaje.
Sama da mutum 700,000, sama da rabinsu yara ne, sun rabu da muhallansu a shekarun baya-bayan nan dalilin masu ta da ƙayar baya.