Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kafa kwamitin binciken lafiyar jiragen sojin Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Nasidi Adamu Yahaya and Awwal Ahmad Janyau

  1. Ƙarin mutum 42 sun kamu da cutar korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 42 sun kamu da cutar korona a Najeriya cikin awa 24 da suka wuce, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a ƙasar.

    Da wannan sabbin alƙaluman, jumillar waɗanda suka kamu da cutar tun watan Fabarairun 2020 sun zama 166,061.

    Sai dai babu wanda ya rasa ransa a ranar ta Talata.

    Sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun fito ne daga jihohi takwas da suka haɗa da Legas (14) da Gombe (11) da Ebonyi (5) da Kano (5) da Abuja (4) da Edo (1) da Kaduna (1) da Rivers (1).

    Ya zuwa yanzu, cutar ta yi ajalin mutum 2,067, sai kuma 156,492 da aka sallama bayan sun warke.

  2. Maraba

    Barkanmu da hantsin Talata tare da fatan kun tashi lafiya. Umar Mikail ke fatan za ku kasance da mu a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Za mu mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da maƙotansu da sauran sassan duniya.