Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An kafa kwamitin binciken lafiyar jiragen sojin Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Nasidi Adamu Yahaya and Awwal Ahmad Janyau

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. Rikicin makiyaya da manoma ya tarwatsa ƙauyuka 8 a Jigawa

    Rikici tsakanin makiya da manoma a wasu yankunan jigawa ya tilastawa ɗaruruwa ƙauracewa gidajensu.

    Wasu mazauna yankunan na jihar Jigawa da abin ya shafa sun ce mata da yara kusan dubu biyar ne suka kauracewa gidajensu saboda fargabar harin ramuwar gayya daga fulani makiyaya.

    Rikicin ya shafi ƙauyukan takwas a yankin ƙaramar hukumar Kirikasamma ta jihar.

    Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin inda kwamishinan ƴan sandan Usman Gomna ya ce sunbaza jami’ansu a garuruwan da ake rikicin.

    Mazauna yankin sun ce tsawon kwana uku suna zaman ɗar-ɗar sakamakon rikicin tsakanin makiyaya da manoma.

    Ɓangaren Fulani makiyaya sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar mutanensu biyu.

    Rikicinya samo asali ne bayan da wani Fulani makiyayi ya shiga gonar wani manomi a garin Gayin, inda manomin ya zargi dabbobin makiyayin da lalata amfanin gonarsa, wanda hakan ya yi sanadaiyar ɓarkewar rikicin.

    Wani mazaunin garin Gayin ya ce suna ciki zulumi domin sai cikin tsakiyar dare ake rikicin, dalilin da ya sa mazauna garin wasu tserewa zuwa Hadejia da garin Nguru na jihar Yobe da Birniwa wasu suna tsallakawa zuwa Kano domin fargabar abin da kaje ya zo.

  3. An kafa kwamitin binciken lafiyar jiragen sojin Najeriya

    Babban hafsan sojan sama na Najeriya (CAS), Air Marshal Oladayo Amao ya kafa wani kwamiti na musamman da ya ƙunshi har da manyan tsoffin sojojin da suka yi ritaya don gudanar da binciken lafiyar jiragen soji na ƙasar da kuma ɓangaren masu kula da su.

    Sanarwar da kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya fitar a ranar Talata ta ce aikin kwamitin ya shafi binciken rahoton lafiyar jiragen sojin da ayyukan injiniyanci tare da ba da shawarar matakan inganta ayyuka da amincinsu.

    “Kwamitin ƙarƙashin jagorancin Air Vice Marshal Abraham Adole, mataimakin kwamandan ayyukan rundunar Hadin Kai an ba shi wa’adin ya gabatar da rahotonsa kafin 18 ga watan Yunin 2021," in ji sanarwar.

  4. Cutar amai da gudawa ta kashe mutum 20 a Bauchi

    Hukumomi a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun ce wata cuta mai kama da kwalara da ta ɓarke a jihar ta yi ajalin kimanin mutum 20.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aliyu Muhammad Maigoro ya shaida wa BBC cewa fiye da mutum 320 suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

    Ya ce cutar ta bazu a yankunan kananan hukumomi tara, tun daga makwanni biyu da suka gabata.

    An dai danganta barkewar annobar da gurbatar ruwan da jama'a ke sha sakamakon zubar ruwan saman farko.

    Kwamishinan ya ce an kafa kwamiti na kar ta kwana don dakile cutar.

  5. Sojojin Mali sun tsige shugaban ƙasa da Firaminista

    Sojoji a Mali sun sanar da cewa an tsige shugaban kasar na rikon kwarya da Firaminista daga mukamansu.

    Ƙasar Faransa ta yi barazanar ƙaƙaba takunkumi kan wadanda suka aikata abin da ta kira juyin mulkin da ba za a amince da shi ba.

    Sojojin na tsare ne da Bah Ndaw da Moctar Ouane a wani sansanin soja inda aka kai su tun a yammacin Litinin.

    Kanal Assimi Goïta mataimakin shugaban gwamnatin rikon ƙwarya ya zargi sojojin da gazawa a kan ayyukansu tare da neman yin zagon kasa ga sauyin da ƙoƙarin tabbatarwa.

    Ya ce za a yi zaɓe a shekara mai zuwa.

    Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan yin garambawul a majalisar zartarwar Mali inda Firaminista ya tuɓe wasu manyan hafsoshin soja biyu.

  6. 'Yan fashin daji sun kashe mutum fiye da 10 a Jihar Zamfara

    An yi jana'iazar mutum 10 a safiyar yau Talata da suka rasu sakamakon wani 'yan fashin daji a wasu kauyukkan jihar cikin daren Litinin.

    Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce akalla mutum 10 ne suka mutu aka kuma yi awon gaba da wasu da dama.

    Wani mazaunin yankin Bungudu, in da lamarin ya faru, ya shaida wa BBC cewa maharan sun isa yankin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma suka kwashi dabbobi da mutane kuma suka tafi da su.

    Ya ce ya zuwa lokacin da yake magana ba su san adadin mutanen da suka mutu ba da kuma waɗnda 'yan fashin suka tafi da su.

    A wani lamarin na daban, jami'an tsaro sun ce sun kashe 'yan fashin dajin aƙalla 10.

  7. Idris Elba zai gudanar da bikin rawa na Ranar Afirka

    Tauraron fina-finan nan na Birtaniya dan asalin kasar Sierra Leonea Idris Elba zai gudanar da bikin rawa na tunawa da Ranar Afirka.

    Mahalarta bikin za su hada da manyan mawakan Afirka ciki har da mawakiyar Tanzania Zuchu da takwararta ta Afirka ta Kudu Elaine.

    Dandalin YouTube ya ce bikin rawar zai bayar da dama ga "sabbin mawakan Afirka".

    MTV Base zai dauki nauyin bikin kuma YouTube zai watsa shi kai tsaye da misalin karfe biyar na yamma a agogon GMT.

    Fitattun mawaka da suka hada da Yvonne Chaka Chaka, Angelique Kidjo da kuma Fally Ipupa za su halarci bikin.

    MTV Base Africa ya wallafa bidiyon mawakan inda ya bayyana nahiyar Afirka a cikin kalmomi uku domin yin bikin Ranar Afirka:

  8. Weah ya jinjina wa dansa kan lashe kofin lig na Faransa

    Shugaban Liberia kuma tsohon dan kwallon duniya George Weah ya taya dansa, Timothy Weah, murna bayan kungiyar kwallon kafar da yake murza wa leda a Faransa Lille ta lashe gasar lig.

    "A matsayina na wanda ya lashe kofin Ligue 1, na san ana bukatar aiki tukuru da kwazo da mayar da hankali kowanne mako domin ka zama gwarzo,” a cewar wani sako da Shugaba Weah ya wallafa a shafin intanet na shugaban kasa.

    “Duk da raunukan da Tim ya ji, ya buga wasa sau 28, kuma mun san wanna shi ne abin da yake so kodayaushe.

    “Muna farin ciki cewa a matsayinsa na dan wasan gaba a kungiyar, ya bayar da gudunmawa wajen ganin Lille ta sake zama gwarzuwar kungiyar wasan Zakarun Faransa,” in ji Mr Weah.

    Shugaba Weah ya murza leda a wasu daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai, wadanda suka hada da Paris Sainte Germaine, Monaco, AC Milan, Chelsea da Manchester City kafin ya yi ritaya a 2004 inda ya tsunduma cikin harkokin siyasa.

    A sekarar 1995 ya zama gwarzon dan wasan Fifa na duniya kuma ya zama shugaban kasar Liberia a 2017.

  9. 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda huɗu a Jihar Enugu

    Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sanda na Oghe da ke Jihar Enugu tare da kashe 'yan sanda huɗu ranar Talata.

    'Yan sandan sun rasa rayukansu ne sakamakon raunukan da suka ji yayin da suke fafatawa da maharan a Ƙaramar Hukumar Ezeagu, kamar yadda Kwamishinan 'yan Sanda Mohammed Ndatsu ya bayyana cikin wata sanarwa.

    "'Yan daban da suka zo da yawansu, sun bude wa 'yan sandan da ke bakin aiki wuta kafin su fuskanci tirjiya kuma da yawa daga cikinsu sun tsere da harbin bindiga," in ji shi.

    "Abin baƙin ciki, huɗu daga cikinsu da suka ji munanan rauni, an tabbatar da mutuwarsu a asibiti sannan kuma maharan sun ƙona wani ɓangare na ofishin."

    Kwamishinan wanda ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu yayin da suke bakin aiki.

    Ya ce an ƙaddamar da bincike don gano miyagun da suka kai harin.

    Hukumomi na zargin 'yan bindiga da ake zargin mambobin ƙungiyar ESN ne da ke son kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin Najeriya da kai hare-hare kan jami'an tsaro ƙarƙashin ƙungiyar IPOB.

  10. Labarai da dumi-dumi, Ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa da bam a Jihar Ebonyi

    Wani mutum ya tarwatse bayan ya tashi bam ɗin da ke jikinsa a Ƙaramar Hukumar Afikpo ta Arewa da ke Jihar Ebonyi a kudancin Najeriya yau Talata.

    Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗa wa BBC Igbo cewa mutumin ya nemi ya kai wa wata makarantar firamare hari ne kafin masu gadi su hana shi shiga makarantar.

    Majiyar ta ce akasarin kamfanonin da ke wurin sun rufe, yayin da sawu ya ɗauke a yankin.

    Ba a samu rahoton rasa rai ko jikkata ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton sannan rundunar 'yan sanda a jihar ba ta ce komai ba game da lamarin.

    Wannan ne karon farko da ake samun rahoton ɗan ƙaunar bakin wake a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

    Sai dai 'yan bindiga sun sha kai hare-hare a baya-bayan nan tare da kashe jami'an tsaro da kuma ƙona ofisoshin 'yan sanda.

    Hukumomi na zargin ƙungiyar IPOB mai fafutikar kafa ƙasar Biafra a yankin da kai hare-haren.

  11. Australia za ta rufe ofishin jakadancinta a Afghanistan

    Australiya ta sanar cewa za ta rufe ofishin jakadancinta da ke Afghanistan nan da ranar Juma'a yayin da kasashe ke ci gaba da janye sojojinsu daga kasar.

    Gwamnatin ta Australiya ta ce rashin tsaron da ake samu a kasar na nufin ba za ta iya ba da cikakken tsaron da ake bukata ba don ci gaba da kasancewar sojojin a Afghanistan.

    A cewar wakilin BBC, Australiyan ta kuma ce jami'anta na diflomasiyya za su rika zuwa Afghanistan din a kai a kai amma za su kasance a wani wurin ne ba a yankin ba.

    Ana ta nuna damuwa cewa janye sojojin tsaro na NATO da Shugaba Joe Biden ya yi na iya jefa Afghanistan cikin rikici.

  12. Buhari na halartar taron yankin Tafkin Chadi kan tsaro

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na halartar taron shugabannin ƙasashen yankin Tafkin Chadi.

    Ana gudanar da taron ne a Abuja a ranar Talata.

    Cikin mahalarta taron har da shugaban Nijar Mohamed Bazoum.

    Shafin gwamnatin ƙasar ya wallafa hotunan yadda taron ke gudana.

  13. Ƴan fansho na koka wa kan sabbin sharuɗɗan gwamnatin Kaduna na tantance su

    Ƴan fansho a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya na kokawa kan wani aikin tantance su da gwamnati ke yi, wanda suka ce yana jefa su cikin ƙunci sakamakon sharuɗɗan da aka gicciya.

    Daga cikin sharuɗɗan har da gabatar da takardar kammala karatun firamare sannan galibi shekaru sun cim musu.

    Da ma dai gwamnati ta yi wani tsari na tantance ƴan fanshon ta yadda sai ko wanne ya je banki da kansa domin ya karbi kudinsa bayan wata uku-uku don tabbatar da cewa yana raye, sai ga shi an bijiro da wannan tantancewar da ake yi a hukumar kula da masu karbar fanshon.

    Alhaji Jafaru Dada Yusuf, shi ne mataimakin sakatare na kungiyar ƴan fansho ta jihar Kaduna, ga kuma

    karin bayanin da ya yi wa Ibrahim Isa:

  14. MDD ta buƙaci a saki shugabannin Mali nan take

    Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta buƙaci a saki shugaban Mali Bah Ndaw da firaminista bayan rundunar sojan ƙasar ta kama tare da tsare su a wani sansanin soja da ke kusa da Bamako.

    Babban Sakataren MDD, António Guterres, ya yi kira da a kwantar da hankali cikin wani saƙon Twitter.

    Ƙungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka da Amurka duk sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.

    Ita ma Najeriya ta buƙaci a gaggauta sakin su ba tare da wani sharaɗi ba.

    A jiya Litinin ne sojoji suka tsare shugaban Mali na riƙon ƙwarya da firaministansa jim kaɗan bayan sanar da yunƙurin kwaskwarima a majalisar ministocin ƙasar, wanda zai sa a sauya manyan sojoji biyu da suka yi juyin mulki a bara.

    Za a kori tsohon ministan tsaro Kanar Sadio Camara da kuma ministan harkokin soja Kanar Modibo Koné daga majalisar.

  15. Najeriya ta sake karya darajar naira a hukumance

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karya darajar naira a hukumance sakamakon fara aiki da ya yi da sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX).

    CBN ya rage darajar kuɗin da kashi 8 cikin 100, inda yanzu take N410.25 kan kowace dala ɗaya.

    Mako biyu da suka wuce kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa bankin zai karya darajar naira ta hanyar sauka daga kan N379 kan kowace dala ɗaya domin tsayar da farashin nairar guda ɗaya a kasuwa.

    Wannan sauyin na nufin daga yanzu kasuwa ce za ta dinga fayyace darajar naira ko kuma farashinta yayin canji.

    Najeriya ta daɗe tana amfani da tsaruka mabambanta wajen canjin kuɗaɗen ƙasar waje, abin da ya sa CBN ya mayar da hankali kan tsari guda ɗaya kenan a yanzu.

    Babu tabbas game da yadda darajarta za ta kasance a kasuwar bayan fage, yayin da a 'yan kwanakin nan nairar ke kaiwa har kusan N490 kan dala ɗaya.

    Yadda ake canzar da dala da yuro da fan a farashin gwamnati:

    • Dala - $1/N410.25
    • Fan - £1/N579.64
    • Yuro - €1/N501.07
  16. An kashe shugaban 'yan sanda a Mexico

    An kashe shugaban 'yan sanda na jihar Sinaloa da ke arewa maso yammacin Mexico.

    Jami'ai a kasar sun ce masu aikata laifi sun harba harsashi 200 kan motar Joel Ernesto Soto yayin da yake tuki.

    A farkon watan nan ma sai da Mista Soto ya tsallake rijiya da baya lokacin da aka kai wa jerin motocin da yake ciki hari kusa da birnin Mazatlan.

    Yankin ya kasance gida ga ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin masu aikata laifi da ke safarar hodar ibilis da tabar wiwi zuwa Amurka.

  17. Najeriya ta buƙaci a saki shugabannin Mali bayan juyin mulki

    Gwamnatin Najeriya ta yi tir da kama shugabannin Mali da sojojin ƙasar suka yi, tana mai bayyana shi da "abin da ba za a amince da shi ba".

    Cikin wata sanarwa daga Ma'aikatar Harkokin Waje, gwamnatin Najeriya ta ce kama Shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctar Ouane zai kawo tsaiko wajen mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya.

    "Gwannatin Najeriya na kira da a saki shugaban ƙasa da firaminista nan take ba tare da wani sharaɗi ba," a cewar sanarwar.

    "Waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin su sani cewa ƙasashe ƙawayen Mali na Allah-wadai da tilasta wa shugabannin ko kuma matsa musu su sauka daga mulki."

    A jiya Litinin ne sojoji suka tsare shugaban Mali na riƙon ƙwarya da firaministansa jim kaɗan bayan sanar da yunƙurin kwaskwarima a majalisar ministocin ƙasar, wanda zai sa a sauya manyan sojoji biyu da suka yi juyin mulki a bara.

    Za a kori tsohon ministan tsaro Kanar Sadio Camara da kuma ministan harkokin soja Kanar Modibo Koné daga majalisar.

  18. Labarai cikin minti ɗaya

  19. Yunƙurin sauya ministocin da ya jawo juyin mulki a Mali

    Sojoji sun tsare shugaban Mali na riƙon ƙwarya da firaministansa jim kaɗan bayan sanar da yunƙurin kwaskwarima a majalisar ministocin ƙasar, wanda zai sa a sauya manyan sojoji biyu da suka yi juyin mulki a bara.

    An fita da Shugaba Bah Ndaw da Firaminista Moctar Ouane zuwa barikin soja na Kati da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.

    A cikin sauyin da za a yi, za a cire tsohon ministan tsaro Kanar Sadio Camara da kuma ministan harkokin soja Kanar Modibo Koné.

    Ba a bayyana wani dalili ba game da korar tasu.

    Janar Souleymane Dacouré da Manjo Janar Mamadou Lamine Diallo ne za su maye gurbinsu.

    Majalisar na da ministoci 25, huɗu daga cikinsu mata ne da kuma huɗu sojoji.

  20. An saka sabuwar dokar zaman gida a Haiti saboda korona

    Mahukunta a Haiti sun sa dokar hana fita cikin dare yayin da adadin mutanen da suka kamu kuma suke mutuwa sanadin cutar korona ke ci gaba da karuwa.

    Shugaba Jovenel Moise ya bayar da umarnin duka 'yan kasar su zauna a gida tsakanin karfe 10;00 na dare zuwa 5:00 safiya.

    Sannan an ƙara tilasta amfani da takunkumi a cikin jama'a.

    Mista Moise ya ce ya yi matuƙar damuwa da yadda cutar ke ƙara bazuwa a kasar a 'yan makwannin baya-bayan nan.

    Jami'an lafiya sun ce akwai yiwuwar ainihin adadin mutanen da suka mutu sun fi yawan mutanen da hukuma ta sanar.