Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tsohuwar Ministar Mata Aisha Alhassan ta rasu

Wannan shafi ne da ke muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ƙarin mutum 28 sun kamu da korona a Najeriya

    Ƙarin mutum 28 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Alhamis, a cewar hukumar yaƙi da yaɗuwar cutuka ta ƙasar, NCDC.

    Bisa alƙaluman da ta wallafa, sabbin kamuwar sun fito ne daga jihohi shida na ƙasar har da Abuja.

    Jihohin su ne: Legas (10), Rivers (7), Akwa Ibom (7), Delta (2), Abuja (2), Kaduna (1).

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 165,301 ne suka kamu da cutar a Najeriya, 2,065 sun mutu da kuma 155,424 da aka sallama bayan sun warke.

  2. Marabanku

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi na Juma'atu babbar rana.