Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Faɗan ƴan daba ne ya sa muka hana tashe a Kano - Ƴan sanda

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Abin da shugabannin Afirka suka ce kan mutuwar Idriss Deby

    Shugabannin Afrika Chadi sun bayyana kaɗuwarsu da alhini bayan samun labarin mutuwar shugaban ƙasar Chadi, Idriss Deby, wanda aka harba a filin daga lokacin da ya jagoranci sojojin kasar yaƙi da yan tawaye.

    Shugaban rikon kwarya na MaliBah Ndaw, ya ce mutuwar Deby babban rashi ne a yaƙida kasashen sahel ke yi da mayaƙan jihadi.

    Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed, ya bayyana Deby a matsayin mai nuna sadaukarwa a yaƙi da ta'addanci, yayinda shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya yaba da irin rawar marigayi Deby ya taka a yaƙi da mayaƙan Boko Haram.

    Shugaban Kamaru Paul Biya ya kira mutuwar Deby a matsayin babban rashi ga Chadi da tsakiyar Afrika da kuma Afrika baki ɗaya.

    Biya ya yi Allah wadai da rikicin da har ya kai ga rasa ran Idris Deby.

    Shugaban Jamhuriyar Congo Felix Tshisekedi wanda shi ne shugaban Tarayyar Afrika ya ce “Chadi da Afrika ta yi babban rashi.”

    Mutuwar Deby ta zo ne bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugabanci kasar karo na shida.

    Sojoji sun ce ɗansa Mahamat Idriss Deby Kaka ne zai riƙe shugabanci zuwa lokacin wani sabon zaben a shekara mai zuwa.

  2. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye da ke faruwa a wannan rana ta Laraba a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu