Akalla masu fama da cutar korona 22 ne suka mutu a wani asibiti
a Indiya sakamakon hujewar da iskar shaka ta Oxygen ta yi.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, a lokacin da tankar da ta
kawo iskar shakar take zubawa a asibitin Zakir Hussain da ke Nashik.
Babu tabbacin yadda lamarin ya faru da abin da ya janyo aka
dakatar da bai wa marasa lafiyar iskar shaƙa.
Sai dai jami’ai sun ce iskar ba ta isa cikin bututun da marasa
lafiyar ke shaƙa har na tsahon minti 30, lamarin da ya janyo mutuwarsu.
Kwamishinan birnin Kailash Jadhav ya ce "za mu yi
kwakkwaran bincike a kan lamarin da daukar mataki."
Asibitin dai sun kira masu tankar iskar shaƙar a lokacin da
wadda suke da ita ta fara ƙarewa.
Asibitoci a Indiya na fadi tashi saboda karancin iskar shaka, ga
kuma ƙaruwar masu kamuwa da cutar korona a kasar.
Wani matashi mai suna Vicky Jadhav, wanda kakarsa ke cikin
wadanda suka suka mutu, ya ce tana samun sauki a lokacin da ya bar asibitin domin
zuwa gida ya ɗauko mata abinci.
Yankin Maharashtra, inda asibitin yake daya ne daga cikin
wuraren da cutar korona ta fi yin muni a jihohin kasar da kuma suke fama da
karashin iskar shaƙa.
Kawo yanzu sama da mutum 200,000 ke kamuwa da cutar korona a kowacce
rana a Indiya.
Lamarin da ya
janyo karancin ban a iskar shaka kadai ba har da gadaje a sibitocin kasar da na
magunguna.