Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An sake kashe yan kasuwar arewa a jihar Imo

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Buhari Muhammad Fagge

  1. Yau shekara ɗaya da rasuwar Abba Kyari

    An cika shekara ɗaya da rasuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaba Buhari, Malam Abba Kyari.

    Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2020 sakamakon rashin lafiya.

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa.

    Buhari ya ce Abba Kyari amininsa ne tsawon shekaru 42 suna tare kafin daga baya ya zama shugaban ma'aikata a fadarsa.

    Malam Abba Kyari ya rasu ne yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

  2. Ana shirin jana’izar Yarima Philip

    A yau Asabar ne za a yi jana’izar Yarima Philip kamar yadda masarautar Birtaniya ta sanar a hukumance bayan rasuwarsa.

    Prince Philip Duke na Edinburgh mijin Sarauniyar Ingila, ya mutu ne a ranar Juma’a 9 ga Afrilu, yana da shekara 99 a duniya.

    Wata biyu ya rage ya cika shekara 100 a duniya.

    Za a ɗauki gawarsa ne zuwa cocin St George cikin wata mota ƙirar Land Rover da ya taimaka aka ƙera.

    Sama da sojoji 730 ne za su kasance a bikin jana’izarar, amma an taƙaita yawan mutane zuwa 30 saboda annobar korona.

  3. Maraba

    Muna maku maraba da kasance da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kai-tsaye da ke faruwa a wannan rana ta Assabar a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kaance da mu