Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fito da gawar Fir’auna da tsoffin sarakunan Masar

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. Biden ya ɗage takunkumin da Trump ya ƙaƙaba wa Fatou Bensouda

    Gwamnatin Joe Biden ta ɗage takunkumin da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba kan babbar mai gabatar da kara ta Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC.

    Amurka ta kakaba wa Fatou Bensouda takunkumin ne a shekarar da ta gabata bayan da ta sanar da bincike kan zarge-zargen laifukan yaki da ƙasar ta tafka a Afghanistan.

    Amurka ba ta taba zama mamba a kotun ICC ba kuma sakataren harkokin wajen kasar, Anthony Blinken ya ce har yanzu Amurka ba ta amince da binciken ba amma ta fi son tattaunawa da masu ruwa da tsaki.

    Kotun ICC ta ce ta ji dadin ɗage takunkumin wanda zai tabbatar da gaskiya a kokarin da ake na bin diddigin manyan laifukan.

  2. Mutum 10 sun kamu da korona a Kaduna

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 66 da suka kamu da cutar korona a ƙasar a ranar Juma'a sannan an sallami mutum 127 bayan sun warke daga cutar.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, Enugu ce ke kan gaba da yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 18.

    Mutum 10 suka kamu a Kaduna da ke matsayi na uku bayan Lagos inda mutum 17 suka kamu.

  3. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da za mu shafe yinin Asabar domin kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu