An kawo ƙarshen matsalar ruwan famfo a Abuja
Hukumomi a birnin Abuja, babban birnin Najeriya sun ce sun kawo ƙarshen matsalar ruwan famfo da ta addabi wasu sassa na birnin bayan tsawon kwana 12.
Unguwannin da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Ushafa da Kubwa da Dutsen Alhaji da Katampe da wasu sassa na Jabi da Gwarinpa da wasu sassan Garki.
Lamarin ba ƙaramin sanya mutanen yankunan cikin tasku ya yi ba, musamman waɗanda ba su da rijiyoyin burtsatse.
Wasu mazauna yankunan sun tabbatar wa da BBC cewa yanzu sun samu ruwan bayan kusan mako biyu.
- Kuna iya karanta taskun da mazauna birnin suka shiga a nan