Ƙarin mutum 135 sun kamu da cutar a Najeriya ranar Alhamis
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 135 da suka kamu da cutar korona a ƙasar ranar Alhamis.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohi 16 da mutum 41 da aka tabbatar sun kamu da cutar.
Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 20 a jihar Imo da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.
A Ogun, an samu mutane 14 da suma suka kamu da korona sai Abuja, babban birnin ƙasar da aka samu mutum 10, Kebbi mai mutum 11 da Rivers da aka samu mutum 10.
Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:
- Akwa Ibom-8
- Plateau-4
- Ebonyi-3
- Kaduna-3
- Kano-3
- Osun-3
- Oyo-2
- Ekiti-1
- Gombe-1
- Nasarawa-1
Kazalika cikin kwana ɗayan, an sallami masu cutar 426 daga cibiyoyin da suke kwance a faɗin Najeriya - mutum 162 daga jihar Ebonyi.
Ya zuwa yanzu, alƙaluman masu cutar ta korona a ƙasar sun kai 161,409, sannan an sallami 146,890 jumulla, baya ga mutum 2,027 da suka mutu kawo yanzu.