Rufewa
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muka kawo ƙarshen kawo muku rahotanni kai tsaye ta wannan shafin sai kuma gobe Asabar da yardar Ubangiji. A kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.
Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin
Masu bibbiyar mu a wannan shafin da haka muka kawo ƙarshen kawo muku rahotanni kai tsaye ta wannan shafin sai kuma gobe Asabar da yardar Ubangiji. A kwana lafiya.
Rahotan daga Kano na cewa wani mutum ya rataye kansa a garin tsamiya da ke Gezawa, tare da barin wasiƙar da ke tabbatar da cewa shi ya kashe kansa.
Wasikar dai na cewa "mutuwar tasa daga Allah ne dan haka ba wani ne ya aikata masa hakan ba".
Mutumin mai suna Babagana Usman mai shekaru 42 ɗan asalin jahar Bornon ne da ke aure a tsamiya Babba, kuma ya rataye kansa a cikin ɗakinsa.
Rundunarr yan sandan Kano ta bakin kakakinta, DSP Abdullahi Kiyawa, ta tabbatar da faruwar al'amarin, sannan tana kan bincike.
DSP Kiyawa ya ce rundunar su ta damu ganin cewa ana samun ƙaruwar mutanen da ke kashe kansu a Kano, don haka za su haɗa kai da malamai da sauran al'umma a bincikensu.
Ko a cikin kwanakin bayan sai da aka samu irin wannan labari na wani mutum a unguwar Sauna kawaji da wani matashi a unguwar masukwani da ke kano da suka kashe kansu ta irin wannan hanya
Rundunar ƴan sandan Kano, ta tabbatar da samun wani abu da ake zargi bam ne a unguwar Aujirawa Alkalai da ke yankin karamar hukumar Gezawa.
A cewar kakakinta, DSP Haruna Kiyawa sun sami labarin ganin bam din ne daga wani mutum da ya je wata gona dan bahaya sai ya ci karo da bam ɗin, don haka sai ya gaggauta sanar da hukumomin tsaro.
DSP Kiyawa ya ce nan take da karbar wannan labarin suka tashi jami’an da ke kwance bam, kuma aka yi nasarar ɗauke shi.
Ya ce, "Da misalin karfe biyar na asuba wani mutum ya kira ya sanar mana da cewar ya je wata gona dan ya biya bukata, sai ya ga wani abu mai kama da bam wanda hakan yasa ya ji tsoro ya sanar da ƴan Sanda abun da ya gani.
Sai muka hanzarta tura jami’an mu masu cire bam, kuma suka sami nasarar dauko shi tare da bincike ko akwai wani amma ba’a samu ba, sai dai muna ci gaba da faɗaɗa bincike," in ji Kiyawa.
DSP Kiyawa ya kuma ja hankalin al’ummar Kano da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokin da kasancewa masu lura sosai da abubuwan da ke faruwa a kusa da su da kuma tuntuɓar hukumomi idan sun yi karo da abin da su ke da shaku a kai.
Shafukan Facebook da Instagram da WhatsApp sun daina aiki a sassa da dama na duniya a yammacin Juma'a abin da ya tunzura da dama daga cikin masu amfani da shafukan.
Shafukan na sada zumunta mallakar mai kamfanin Facebook, da Messenger tun daga karfe 5:30 agogon GMT suka tsaya.
Masu amfani da shafin idan suka yi ƙoƙarin buɗe wa suna cin karo da irin wannan sako da ke cewa ‘5xx Server Error’, wato alamar matsala ba tare da wani cikakken bayani ba.
Hakazalika da dama daga cikin masu amfanin da shafin Facebook sun ce sun gaggara iya shiga shafin, koda yake kashi 63 cikin 100 na masu amfani da shi ne suka ce an datse su baki ɗaya.
Mutane dai sun yi ta bayyana takaicinsu da ƙorafi a shafukan sada zumunta kan gaggara iya tuntuɓar abokansu da iyalai ko abokan aiki na wani lokaci.
An binne firaministan Ivory Coast, Hamed Bakayoko wanda cutar kansa ta yi ajalinsa a makon da ya gabata a Jamus, a kusa da kabarin mahaifinsa.
An yi jana'izarsa ne a wani gidan gona mallakar iyalansa mai tazarar kilomita 6 daga yammacin garin Séguéla.
A Yulin shekarar da ta gabata aka naɗa Bakayoko a matsayin firaminsta inda ya maye gurbin Amadou Gon Coulibaly wanda ya mutu sakamakon bugun zuciya.
An naɗa Patrick Achi a matsayin firaministan riƙon ƙwarya.
Ƴan bindiga sun kai sabbin hare-hare a ƙananan hukumomi uku na Kaduna tare da kashe mutum 13 da jikkata da dama da kuma ƙona gidaje.
Wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Arwan na cewa an kai hare-haren ne a yankunan Zango-Kataf da Kauru da Chikun a yau Juma'a.
A cewar sanarwar, rundunar ta musamman ta 'Operation Safe haven' ce ta sanarwa da hukumomi halin da ake ciki.
Aruwan ya ce ƴan bindigan sun soma farwa kauyen Gora Gan a Zango-Kataf, sannan suka shiga Kizachi da ke karamar hukumar Kaura nan suka kashe mutum 10, da jikkata mutum hudu.
"An ƙona gidaje 56 da babura 16, da wawushe kayan amfanin gona da kona da dama," a cewarsa.
Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai ya yi alla-wadai da hare-haren da addu'a da kuma mika sakon ta'aziya ga iyalan mutanen da aka kashe.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya, NCAA, ta ce ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Azman saboda kaucewa afkuwar haɗari da salwantar rayuka, wanda tabbas alamomi sun nuna hakan, muddin jiragen suka ci gaba da fatali da ƙa'idojin kiyayye haɗura.
Kakakin hukumar, Sam Adurogboye, ne ya faɗa hakan a cikin sanarwar da ya fitar da ke bayani kan dalilan dakatar da hada-hadar jiragen kamfanin Azman.
Ya ce babu batun ƙoƙarin yaudara ko barazana ga hukumar NCAA yayinda take aikin da ya rataya a wuyanta.
A ranar Talata NCAA ta dakatar da jirgin Azman domin tantace lafiyar jiragen bayan sun fuskanci matsala har sau uku.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, kamfanin Azman ya yi iƙirarin cewa yana bin ƙa'idojin kare faruwar haɗura.
Hukumar kare hakkin bil adama ta kasar Mozambique ta ce akalla zabaya (albino) 114 ne suka bace a kasar a cikin shekaru bakwai.
A yanzu haka ana shari'a kan bacewar mutum kusan 55 wadanda suka duka zabaya ne.
Shekara da shekaru ana kashe zabaya a yankunan gabashi da kudancin Afrika, kuma ana amfani da sassan cikinsu wajen yin tsafi bisa dogaro a kan cewa mutum zai yi kudi ko kuma zai taki sa'a.
Wakiliyar BBC ta ce ma'akatar shariar kasar ta ce tana iyaka kokarinta wajen kare zabaya a kasar tare da yaki da masu nuna musu bambamci.
Zabaya a Mozambique na fuskantar matsaloli a wannan lokacin na annobar korona saboda asibitoci da dama na kin dubasu.
Jami'an tsaro a Myanmar sun harbe karin mutum tara har lahira a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin da aka yi a watan da ya wuce.
Shaidu sun ce an kashe mutum takwas a garin Aungban sannan aka kashe daya a Loikaw.
Cikin wata sanarwa, BBC ta ce ta damu matuka kan makomar wakilinta Aung Thura, wanda wasu da ba a san ko su wane ne ba suka tafi da shi a babban birnin kasar Naypyitaw.
BBC ta yi kira ga mahukunta a kasar su gano inda yake sannan su tabbatar yana cikin koshin lafiya.
An ɗauke ma'aikacin na BBC ne tare da wani dan jaridan.
A halin yanzu kuma mutane na ci gaba da tserewa daga Yangon babban birnin kasar saboda tashin hankalin da ke kara muni.
Rundunar sojan Najeriya ta tabbatar da mutuwar soja ɗaya a wani artabu da dakarunta suka kashe 'yan fashi da yawa a garin Kabasa da ke Jihar Zamfara.
Dakarun a cewar wata sanarwa da kakakin sojan Najeriya Mohammed Yerima ya fitar yau Juma'a, sun yi nasarar daƙile wani harin 'yan fashin.
Ya ce sojojin na Runduna ta 3 Operation Hadarin Daji sun shiga garin ne da ke Ƙaramar Hukumar Magami sakamakon wani rahoton sirri da suka samu ranar Talata cewa 'yan bindiga na tsaka da kai hari a yankin.
Ya ƙara da cewa zuwansu ya sa 'yan bindigar suka gaza aikata abin da suka je yi kuma "aka yi nasarar kashe gommai daga cikinsu sannan wasu suka tsere da raunuka".
"Abin baƙin ciki, soja ɗaya ya rasu sannan wasu uku da suka ji rauni yayin fafatawar na karɓar magani a asibiti," a cewarsa.
A gefe guda kuma, sojojin sun yi nasarar kuɓutar da wasu mata guda biyu mazauna ƙauyen Kuyallo na Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna bayan sun shafe kwana 22 a hannun 'yan fashin, in ji sanarwar.
Man United za ta fafata da Granada a wasan dab da na kusa da na ƙarshe (kwata fayinal) a gasar zakarun Turai ta Europa League.
Ita kuwa Arsenal za ta ɓarje gumi ne da Slavia Prague.
Ajax da Roma za ta buga nata wasan, yayin da Dinamo Zagreb za ta kara da Villarreal.
Idan aka zo wasan dab da na ƙarshe wato semi fayinal, wanda ya ci wasa tsakanin Granada v Manchester United zai haɗu da Ajax ko Roma.
Real Madrid za ta fafata da Liverpool a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai ta Champions League.
Manchester City za ta buga nata wasan da Borussia Dortmund, yayin da Chelsea za ta barje gumi da FC Porto.
Mai rike da kofin Bayern Munich za ta buga wasanta da Paris St-Germain kungiyar suka buga wasan karshe na gasar a bara.
Wani babban jami'i a ofishin jakadancin Canada na China ya ce an hana shi damar shiga kotu domin zaman sauraron shari'ar wani dan kasar ta Canada da ake zargi da leken asiri.
Canada ta ce China ta bayar da dalilin tsaron kasa a matsayin abin da ya sa aka hana shi shiga inda Micheal Spavor yake, wanda ake sa ran zai bayyana gaban kotu a yau Juma'a.
A cewar wakilin BBC ya ce Mista Spavor daya ne daga cikin 'yan Canada biyu da aka kama cikin shekarar 2018.
Wata tawagar jami'an difilomasiyya sun taru a gaban kotun, inda suke sukar rashin ba su damar shiga kotun.
China ta dade tana musanta cewa tsare mutanen ramuwar gayya ce ga kamen da aka yi wa wata babbar jami'a a katafaren kamfanin kera wayar hannu na Huawei mai suna Meng Wanzhou.
Ana zarginta ne da tafka almundahana a Amurka.
Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta ƙara adadin masu son yin Umara ta hanyar ƙara ajin shekarun maniyyatan ga mazauna ƙasar.
Shafin Haramain ya ruwaito cewa cikin wasu bayanai da ke amsa tambayoyin da maniyyata ke yawan yi, ma'aikatar ta ce a yanzu 'yan shekara 18 zuwa 70 za su iya yin rajista don gudanar da aikin saɓanin 60 da aka yarda a baya.
A baya dai an taƙaita wa dajjitai gudanar da aikin ne saboda kare su daga kamuwa da cutar korona.
Ma'aikatar ta ce tana bayar da damar yin aikin ga waɗanda suka yi rajista duk kwana 15.
Kazalika, an ƙara yawan adadin ne bisa ƙa'idojin ma'aikatar lafiya.
Ƙaramin Ministan Ilimi a Najeriya Emeka Nwajiuba ya ce adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar ya kai miliyan 10.
Kafafen yaɗa labarai sun ruwaito ministan na bayyana haka a birnin Dutse na Jihar Jigawa yayin ƙaddamar da wani shirin haɓaka ilimi da Bankin Duniya ya ɗauki nauyi a jihar ranar Alhamis.
"Da adadin yara 10,193,918, Najeriya ce ke da adadi mafi yawa na yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasashen saharar Afirka," in ji Nwajiuba.
Daily Trust ta ruwaito Ministan Ilimi Adamu Adamu a watan Janairu na wannan shekarar cewa adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya ya ragu zuwa miliyan 6.946 a 2020 maimakon 10.1 a 2019.
Sai dai hakan na nufin an samu ƙarin 3,054,000 kenan a kan adadin na 2020.
Ƙaramin ministan ya ce Jigawa na cikin jihohin da suka fi yawan yaran marasa zuwa makaranta.
Dakarun 'yan sanda a Jihar Kaduna sun kashe 'yan fashi biyu ranar Laraba yayin wani artabu a Ƙaramar Hukumar Lere ta jihar.
'Yan fashin kamar yadda wata sanarwa daga kakakin rundunar 'yan sandan ta nuna, na shirin kai "wani mummunan hari" ne a garin Saminaka a lokacin da haɗin gwiwar dakarun suka far musu bayan samiun wasu bayanan sirri.
Mohammed Jalige ya ce 'yan bindigar sun fara harbi a kan mai tsautsayi bayan sun hangi jami'an tsaron, abin da ya haddasa zazzafar musayar wuta.
Hakan ya sa 'yan sandan suka kashe biyu daga cikinsu sannan wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Kakakin 'yan sandan ya ce sun ƙwace makaman 'yan fashin da suka haɗa da bindigar AK-47 guda biyar da kwanson harsashi guda 17.
Gidauniyar Global Fund mai tallafawa wajen yaƙi da cutuka a ƙasashen duniya ta bai wa Najeriya tallafin kuɗi dala miliyan 890 - kwatankwacin naira biliyan 338 - domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar ƙasar.
A baya dai dangantaka ta yi tsami tsakanin Najeriya da gidauniyar, wadda har ta yanke bai wa kasar tallafi.
A jiya Alhamis ne hukumomin Najeriya suka bayar da sanarwar sabon tallafin.
A tattaunawarsa da Isahq Khalid, kakakin fadar shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen kula da cutuka irinsu tarin fuka da ƙanjamau da korona.
Wata tawagar haɗin gwiwa ta dakarun sojan sama da na ƙasa na Najeriya sun karɓe iko da ayyukan tsaron filayen jirgin sama a wasu jihohin arewacin Najeriya sakamakon barazanar tsaro da 'yan fashin daji ke haifarwa a yankin.
Rahoton jaridar Leadership ya ruwaito cewa matakin ya biyo bayan umarnin da gwwamnatin tarayya ta bayar ne bayan 'yan bindiga sun kutsa unguwar ma'aikatan hukumar kula da filayen jirgi ta ƙasa a Kaduna kuma suka yi garkuwa da mutum 10 - waɗanda sojoji suka ceto.
A baya dai, jami'an hukumar Federal Airport Authority of Nigeria (FAAN) ne da kuma na NSCDC ke kula da tsaron filayen jirgin kafin sojojin su maye gurbinsu.
A Jihar katsina inda hare-haren 'yan fashin ya yi ƙamari sosai, an ga ƙarin jami'an soja saɓanin baya a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua, a cewar rahoton.
A jihar Kaduna kaɗai, 'yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.
Mahukunta a Mexico sun ce wani hari da aka kai kan ayarin motocin 'yan sanda a tsakiyar ƙasar ya halaka mutum 13.
Waɗanda lamarin ya rusta da su 'yan sanda ne da ke sintiri a garin Coatepec Harinas.
'Yan sandan birnin sun duƙufa wajen yaƙar ƙungiyoyin ɓatagari masu aikata miyagun laifuka a kasar.
An kashe fiyed 'yan sanda fiye da 500 a shekarar da ta gabata a Mexico.
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a matsayin mace ta farko Shugaabar Ƙasar Tanzania biyo bayan mutuwar John Magufuli ranar Laraba.
Alƙalin Alƙalai Ibrahim Juma ne ya rantsar da ita a Fadar Gwamnati da ke babban birnin ƙasar Dar es Salaam.
Ita ce shugabar Tanzania ta shida bayan ta shafe shekara fiye da biyar a matsayin mataimakiyar Magufuli, wanda ya rasu sakamakon ciwon zuciya.
Kundin tsarin mulkin Tanzania ya tanadi cewa mai shekara 61 ɗin za ta ƙarasa wa'adi na biyu na shekara biyar da suka fara.
Ita ce shugabar ƙasa mace tilo a Nahiyar Afirka da ke kan mulki yanzu haka.