Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kwana uku a jere ƴan fashi na kai hari ƙauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da suaran ƙasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Har yanzu Syria na cikin mummunan yanayi

    Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce shekara 10 bayan yaƙi a Syria, har yanzu ƙasar na fuskantar mummunan yanayi na neman agaji.

    Kimanin mutum miliyan 12.4 kusan kashi 60 na mutanen ƙasar na fama da rashin abinci da yuwa.

    Hakan na nufin an samu ninki biyu na adadin da aka samu a shekarar 2018.

    A cewar hukumar, annobar korona ta ƙara ta'azzara matsalar inda farashin kayan masarufi suka ƙaru da kashi 200 a shekarar da ta gabata.

    Hukumar ta buƙaci ƙarin kuɗaɗen tallafi inda ta ce rashin samun tallafin na iya sa ta rage kuɗaɗen da take samarwa.

  2. Mutum 287 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Alhamis

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 287 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Alhamis.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 107 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 26 a Kwara, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    A Akwa Ibom mutum 23 sun kamu sai Bauchi da aka samu mutane 22 da aka tabbatar sun kamu da Ogun da aka samu mutum 21.

  3. Buɗewa

    Barkanku da safiya.

    Jumu'atu babbar rana, kuma muna fata za ku kasance da mu a wannan shafin inda muke kawo maku labarai daga Najeriya da abubuwan da ke faruwa a makwabtanta da sauran sassan duniyam