Za a fara yi wa mutane allurar riga-kafin cutar korona a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta karbi allurar rigakafin Korona 209, 520.
A lokacin da yake karbar allurar rigakafin a filin jiragen sama na Malam Aminu Kano, a madadin Gwamna Ganduje, kwamishinan lafiya, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce allurar rigakafin kashin farko zai fi mayar da hankali ne kan ma’aikatan lafiya da ke jahar.
Jami’ar hulda da jama’a ta ma'aikatar lafiya a Kano, Hadiza Namadi ta tabbatar wa da BBC karbar riga-kafin.
Sannan nan ba da jimawa ba za a yi wa gwamanan jihar Abdullahi Umar Ganduje allurar rigakafin.
Sai dai kwamishinan ya ce kwamitin yaki da cutar ta korona a jihar nan gaba zai sanar da lokacin da za a fara riga-kafin ga kowa da kowa a jihar.