Kotun Malaysia ta amince kiristoci su yi amfani da sunan ‘Allah’ a rubutunsu
Kotun Koli a Malaysia ta kawo karshen taƙaddama ta tsawon shekaru 13 inda ta zartar da hukuncin da ya ba Kiristoci damar yin amfani da kalmar "Allah" a rubuce-rubucensu.
Shari’ar ta shafi wata mata ce daga 'yan asalin ƙasar Malaysia bayan ƴan sanda sun ƙwace kaset kaset na CD na addini a 2008 da ke cewa haramun ne a gare tamallaki abubuwan da ke ɗauke da sunan Allah a Larabci.
Gwamnatin ƙasar kullum tana jaddada cewa kalmar ‘Allah’ Musulmai ne kawai ya kamata su yi amfani da ita, tana mai cewa saɓa ma hakan ga wani addini zai iya sauya tunani da kuma jirkita tunaninsu zuwa wasu addinai idan aka yi amfani da sunan wanda zai saba wa addinin.
A shekarar 2013, wata kotun ɗaukaka ƙara a kasar Malaysia ta yanke hukuncin haramta wa wata jaridar mabiya Katolika a ƙasar amfani da kalmar Larabci "Allah" a cikin fassararta ta Malay a rubutunta game da addinin Kirista ba, wani lamari da ya haifar da hare-hare a wuraren ibada uku shekarun baya.