Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mata sun fi fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu - WHO

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Awwal Ahmad Janyau

  1. Masu zanga-zanga sun tsere wa samamen ƴan sanda a Myanmar

    Dubban masu adawa da sojojin Myanmar sun ce sun yi nasarar tserewa samamen cikin dare da jami'an tsaro suka yi a wata gunduma mafi girma a Yangon, babban birnin ƙasar.

    Masu fafutuka sun tsinci kansu a maƙale a gidajen da ke Sanchaung bayan ƴan sanda sun sanar a ranar Litinin cewa za su bi gida-gida su yi bincike don gano waɗanda ba ƴan gundumar ba.

    Sun yi gargaɗin hukunta duk wanda suka kama yana bai wa masu zanga-zanga mafaka.

    Rahotanni na cewa an tsare kimanin mutum 50.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta jagoranci kiraye-kirayen a dakatar da matakin.

    Wasu daga cikin waɗanda suka tsere sun yi alƙawarin ci gaba da zanga-zangar da suke yi.

  2. Mutum 371 sun kamu da cutar korona a Najeriya ranar Litinin

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 371 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Litinin, sannan 13 sun mutu.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, a wannan rana, jihar Legas ce ke kan gaba a jerin jihohin da aka samu ɓullar cutar da mutum 102 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Alƙaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 65 a Enugu, da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    Mutum 56 sun kuma sun kamu da korona a Edo sai Birnin Tarayya Abuja da aka samu mutane 23 da aka tabbatar sun kamu da Ogun da aka samu mutum 20.