Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An 'ƙirƙiri' wata dabba a ɗakin gwaji a Amurka

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. An kashe matashiya 'yar shekara 20 a zanga-zangar Myanmar

    An kashe mutum na farko a zanga-zangar Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Myanmar, inda aka harbi wata matashiya a ka.

    Tun a makon da ya gabata ne aka jikkata Mya Thwe Thwe Khaing mai shekara 20 a lokacin da 'yan sanda suka yi yunƙurin tarwatsa masu zanga-zangar da ruwa da harsashin roba da kuma mai kisa.

    Sai dai harbin da aka yi mata a kanta ne ya yi ajalinta, a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙi.

    An kwana biyu ana zanga-zanga a Myanmar biyo bayan juyin mulkin da ya tumɓuke Aung San Suu Kyi daga mulki.

    Asibitin da ke birnin Nya Pyi Taw ya tabbatar da mutuwarta da misalin ƙarfe 11:00 na dare agogon ƙasar.

  2. Cutar Korona a Najeriya: Mutum 16 sun mutu, 877 sun kamu

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce ƙarin mutum 16 sun mutu sakamakon annobar cutar korona.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, an samu ƙarin mutum 877 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Alhamis.

    Jihar Legas da ta fi yawan masu fama da cutar a Najeriya ce ke kan gaba da mutum 273 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Kazalika, mutum 87 ne a jihar Kaduna gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

    Jihar Rivers da ke yankin kudu maso gabas ce a mataki na uku, da adadin mutum 58 suka kamu da korona ranar Alhamis, sai kuma Akwa Ibom da ke wannan shiyya ita ma da aka samu mutum 47.

    A jihar Ebonyi an samu mutum 47, yayin da ƙarin mutum 46 suka kamu a Edo, dake kudu maso yammacin Najeriya, duka dai a ranar ta Alhamis.

    Ga yawan wadanda aka samu a wasu jihohi:

    • Ogun-46
    • Abia-34
    • Imo-34
    • Kano-34
    • Oyo-26
    • Osun-22
    • Gombe-20
    • Ekiti-19
    • Cross River-15
    • FCT-15
    • Plateau-11
    • Enugu-9
    • Kebbi-8
    • Borno-7
    • Niger-6
    • Bayelsa-5
    • Nasarawa-4
    • Kwara-2
    • Katsina-1
    • Sokoto-1
  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da safiyar Juma'atu babbar rana, tare da fatan mun tashi lafiya.

    Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu - har ma sassan duniya.