Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fani-Kayode ya ce bai sauya sheƙa ba

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Awwal Ahmad Janyau

  1. Za a gudanar da zaɓe a Falasɗinu a karon farko cikin shekaru 15

    Ɓangarorin Falasɗinawa sun amince da tsare-tsare don gudanar da zaɓukan ƴan majalisar dokoki da na shugaban ƙasa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza, a cewar kafofin yada labarai na Falaɗinu.

    Bayan tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu da ke adawa da juna - Fatah da Hamas - wakilansu sun yi wata ganawa a Alƙahira wadda aka fara ranar 8 ga watan Fabrairu.

    An sa za a gudanar da zaɓen majalisa a watan Mayu sannan za a yi na shugaban ƙasa a Yuli.

    A cewar wani kwamiti kan zaɓukan, Falasɗinawa miliyan 2.36 a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza ne ke iya kaɗa kuri'a.

    An gudanar da zaɓen majalisar dokoki na karshe a Falasɗinu ne a 2006 kuma Hamas ne suka yi nasara. Kuma su ne ke mulkin Gaza tun 2007 lokacin da suka yi nasara a wata karawa da makamai da Fatah.

  2. Gwamnatin Chadi ta musanta kama tsohon shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

    Mai magana da yawun gwamnatin Chadi, Cherif Mahamat Zene ya musanta rahotanni da ke cewa an kama tsohon shugaban Jamhuriyar Tsakiyar Afrika Francois Bozize.

    Ya ce gwamnatin Chadi ta yi mamakin zargin da wasu kafofin yada labarai ke yi na cewa an tsare Shugaba Bozize a iyakar Chadi.

    "Ina so in ƙaryata wannan zargi," kamar yadda ya wallafa a Twitter.

    Jam'iyyar Bozize Kwa Na Kwa da ƙawancensa na tawaye, Coalition of Patriots for Chnage (CPC) duk sun ƙaryata rahotannin kama shi.

    An fara vyaɗa jita-jitar ne bayan da Bozize ya koma mahaifarsa daga garin Boda da ke kudu maso yammacin ƙasar, wanda a yanzu yake ƙarƙashin ikon rundunar sojin gwamnati da ke da goyon bayan Rasha da sojojin Rwanda.

    • Barry Burgess: Tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC ya rasu
    • Babagana Zulum: Gwamnatin Borno ta yi karin haske kan hatsarin da ya faru a Mafa
  3. Zulum zai dawo da ƴan gudun hijirar Najeriya 9,800 daga Kamaru

    Gwamnan jihar Borno, Fafesa Babagana Umara Zulum, tare da jami'an Ma'aikatar Harkokin Agaji da Ci gaban Al'uma ta Najeriya na ziyara a garin Marwa na Kamaru don mayar da wasu ƴan Najeriya 9,800 ƴan asalin Borno gida.

    Mutanen dai na cikin wasu ƴan gudun hijirar Najeriya 46,000 da suka yi hijira zuwa wani sansani a Minawao a Kamaru.

    Ƴan Najeriyar 9,800 na cikin rukunin farko na ƴan ƙasar da suka nuna son a kwashe su daga sansanonin ƴan gudun hijira zuwa wasu gidaje da gwamnatin Borno ta gina a garuruwan Bama da Banki.

    Zulum ya jagoranci tawagar daga Najeriya kan wata yarjejeniya da aka sa wa hannu tsakanin Najeriya da Kamaru da ofishin jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan ƴan gudun hijira, wanda za a yi a garin na Marwa a arewacin Kamaru.

    Gwamnan yankin arewa na Kamaru, Mijinyawa Bakare ne mai masaukin baƙi a tattaunawar.

    Cikin tawagar ta Najeriya akwai Sakatare na din-din-din na ma'aikatar ayyukan agajin ta Najeriya Malam Bashir Nura Alkali da Darektan ma'aikatar Ali Grema wasu jami'an gwamnatin jihar Borno.

  4. An rufe majalisar dokokin Ghana kan ɓarkewar cutar korona

    Majalisar Dokokin Ghana za ta ɗage zamanta tsawon makonni uku saboda yaduwar cutar korona a tsakanin ƴan majalisar da sauran ma'aikata, a cewar Kakakin Alban Bagbin ranar Talata.

    Adadin ƴan majalisar da suka kamu da cutar ya kai 17 yayin da ma'aiaktansu 151 ne kawo yanzu suka kamu.

    Kakakin Bagbin ya ce sai ran 2 ga watan Maris ne za su sake zama.

    Za a sake yi wa ƴan majalisar da ma'aikatansu nan da mako biyu a cewar kafar yaɗa labaran ƙasar.

    Ƙaruwar masu ɗauke da cutar a majalisar ta tursasa rage zama cikin makon jiya, inda aka mayar da taron majalisar zuwa kwanakin Talata da Alhamis kawai.

    Kawo yanzu, Ghana ta samu masu ɗauke da cutar 73,000 da wadanda suka mutu 482 tun farkon ɓullarta a watan Maris ɗin bara.

  5. JAMB za ta gurfanar da mutum 200 kan satar amsa a jarrabawa

    Hukumar JAMB da ke shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya ta ankarar da ƴan Najeriya kan wasu masu shirya maguɗi a jarrabawa a cibiyoyinta a lokacin jarrabawar 2020 a wasu sassan arewacin Najeriya.

    Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce sama da ɗalibai 400 da ke neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire ne aka kama da shaidar samun gurbi na bogi.

    A cewar hukumar, ƙungiyoyin masu shirya satar amsa a jarrabawar ta JAMB, wanda a baya an fi ganinsu a kudancin kasar a yanzu sun fara yaɗuwa a arewacin ƙasar.

    JAMB ta ce ta kama wani Buhari Abubakar wanda aka kama yana rubuta wa wani Muhammad Sanusi jarrabawa.

    Jami'an NSCDC ne suka kama mazan biyu a Kano.

    Oloyede ya ce JAMB za ta fitar da Naira miliyan 100 don yanke wa mutane 200 cikin 400 da aka kama da yin maguɗin jarrabawa.

  6. Dole ne gwamnoni su hada kai kan matsalar tsaro a Najeriya- Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

    Bayan jerin barazanar kora da aka yi wa Fulani makiyaya a kudancin Najeriya, Ƙungiyar gwamnonin Arewa ta bayyana damuwarta kan fargabar da barazanar ke haifarwa.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa kungiyar ta ce wannan matakin na ƙara ruruta matsalar rashin tsaro a ƙasar.

    Sai dai ƙungiyar ta ce a shirye ta ke ta yi aiki tuƙuru don ganin ta samo maslaha amma tana buƙatar goyon bayan takwarorinta na kudu.

    Daily Trust ta ce ƙungiyar ta bayyana haka ne a wani taron mambobinta da aka gudanar a daren Litinin inda aka tattauna batutuwan da ke shafar yankin arewa da ma ƙasar baki ɗaya.

    Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Filato Simon Lalaong ne ya jagoranci tattaunawar.

    Ƙungiyar ta ce akwai buƙatar ganawar gaggawa tsakanin duka gwamnonin ƙasar don samun mafita a matsalar tsaron da ta addabi ko wane yanki a Najeriya.

  7. Mutum 1,056 sun kamu da korona a ranar Talata a Najeriya

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,056 da suka kamu da annobar korona a ƙasar ranar Talata.

    Bisa sabbin alkaluman hukumar, jihar Legas ce kan gaba a yawan waɗanda suka kamu da cutar ranar Talata, da mutum 214.

    Osun dake jiha ta 14 wajen yawan masu cutar a Najeriya ce ke biye mata baya da mutane 120 da aka ba da rahoton sun kamu da cutar a wannan rana.

    Abuja babban birnin ƙasar na mataki na uku wajen yawan wadanda suka kamu a jiyan, da mutum 116, sai Plateau mai mutum 88, da Adamawa mai mutum 52, da kuma jihar Ebonyi da aka samu mutum 75 da suka kamu.

  8. Buɗewa

    Barkanku da safiya.

    Da fatan za ku kasance da mu a wannan shafin da ke kawo maku labarai kai tsaye, na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma sauran ƙasashen duniya.