Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fani-Kayode ya ce bai sauya sheƙa ba

Wannan shafin na kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran ƙasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

    Da fatan za ku kasance da mu zuwa gobe idan Allah ya kai mu inda za mu shafe yinin Alhamis muna kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

  2. Shugabar ƴan kishin ƙasa a Faransa ta gurfana kotu kan wallafa hotunan IS

    Shugabar masu kishin ƙasa a Faransa Marine Le Pen ta gurfana a gaban kotu saboda wallafa wasu hotunan ta’asar ƙungiyar IS a shafin Twitter.

    Lokacin da ta shiga kotun Le Pen ta dangata shari’ar da siyasa.

    Ita da wata ƴar jam’iyyarta ana tuhumarsu da wallafa saƙonnin tashin hankali waɗanda ke iya haifar da ta'addanci ko cutar da ɗan adam.

    Ta wallafa hotuna uku a Disamban 2015 domin mayar da martani ga wani ɗan jarida wanda ya kwatanta jam'iyyarta da IS.

    Ta goge ɗaya daga cikin hotunan da ke nuna ɗan jaridar Amurka James Foley da aka fille kansa bayan iyalinsa sun koka.

    Amma ta ce laifuka ne masu ban tsoro da suka cutar da mutuncin ɗan adam, ba hotunan ba

  3. Sri Lanka za ta daina ƙona gawawwakin korona

    Firaministan Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, ya shaida wa majalisar dokokin ƙasar cewa gwamnati za ta fara bari a binne gawawwakin da korona ce ta yi sanadinsu a maimakon ƙona su.

    A kwanakin baya ne dai gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa binne mamacin da cutar ta kashe kan iya zama barazana ga jama'a, sakamakon gawar za ta iya gurɓata ruwan da ke cikin ƙasa.

    Masana kimiyya da dama da kuma Hukumar Lafiya Ta Duniya duk sun yi watsi da wannan tunanin.

    An kiƴasta cewa tun bayan saka wannan doka, an ƙona gawawwakin aƙalla mutum 200 ba tare da son ran iyalansu ba.

  4. Saudiyya ta saki mai fafutikar kare haƙƙin mata

    An sako sananniyar mai fafutikar kare haƙƙin matan ta Saudiyya daga gidan yari.

    Iyalan Loujain al-Hathloul sun bayyana cewa ta koma gida ne bayan ta shafe sama da kwanaki dubu a kulle, inda ake zargin cewa yayin zaman nata an ci zarafinta ta hanyar lalata da kuma gana mata azaba.

    An rufe al-Hathloul tun a 2018, kafin a cire haramacin tuƙin motar mata a ƙasar, wanda tana daga cikin waɗanda suka yi gwagwarmayar neman ƴancin tuƙin matan shekara da shekaru.

    Rahotanni sun bayyana cewa Yarima mai jiran gado na ƙasar Mohammed bin Salman ne ya bayar da umarnin a sake ta.

    Daga cikin zarge-zargen da aka yi mata a baya har da batun haɗa kai da ƙungiyoyin ƙasashen waje.

  5. Labaran BBC cikin minti ɗaya

  6. Fani-Kayode ya ce yana nan a PDP

    Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Femi Fani-Kayode ya musanta cewa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

    Gwamnan Kogi Yahya Bello ne ya shaida wa manema labarai cewa tsohon ministan ya koma jam'iyyar APC.

    Fani-Kayode wanda ya yi suna wajen caccakar APC da gwamnatin Buhari ya ce yana nan a jam'iyyarsa ta PDP.

    "Ko da yake mun tattauna a ɓangarorin jam'iyya kuma muna cikin lokaci na tuntuɓa ban bar PDP ba," kamar yadda Fani-Kayode ya wallafa a Twitter.

    A ranar Litinin Fani-Kayode ya wallafa hotonsa tare da gwamnan Yahya Bello da kuma gwamnan Yobe shugaban APC na riƙo a Twitter inda ya ce sun tattauna kan batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa.

  7. Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami’ar jihar zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur

    Gwamnatin Bauchi ta sauya sunan jami’ar jihar ta Gadau zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur.

    Kwamishinan ilimin jihar Dakta Aliyu Tilde a cikin wata sanarwa ya ce majalisar zartarwar jihar ce ta amince da sauya sunan.

    Ya yanzu za a gabatar wa majalisa domin ta amince.

  8. Iran ta yi bikin cika shekara 42 da juyin juya halin musulunci

    Iran ta yi bikin tunawa da ranar juyin juya halin Islama na ƙasar da aka yi a shekarar 1979.

    Sai dai na bana ya zo lokacin annobar korona, da kasar ta fi kowacce jin jiki a yankin gabas ta tsakiya.

    Kuma an gudanar da bikin ne ba kamar yadda aka saba ba inda aka kiyaye matakan korona don gudun ƙara bazuwarta.

    Ku saurari rahoton Aisha Shariff Baffah.

  9. Ƴan tawayen Houthi sun kai hari cikin Saudiyya

    Saudi Arabiya ta ce wani jirgin ɗaukar fasinja ya ci wuta bayan da ƴan Houthi suka kai hari wani filin jirgin samanta.

    Saudiya ba ta yi cikakken bayani kan lamarin ba musamman ta’adin da harin ya yi. Sannan ba a tantance yadda suka kai harin ba.

    Ƴan Houthi din sun ce sun kai hare-hare ne ta hanyar amfani da jirage marasa matuka a filin jirgin Abha da ake ajiye jiragen yaƙi.

    Kawancen da Saudiyya ke jagoranta na goyon bayan gwamnatin Yemen a yaƙin da ta ke yi da ƴan Houthi da ke samun goyon bayan Iran

    Ta ƙaddamar da hare-hare ta sama a yankin da ke karkashin ikon ƴan tawaye a arewacin Yemen wanda ke haifar da asarar rayukan fararen hula.

  10. Kotu ta yi ɗaurin shekara 30 kan mutumin da ya guntile hannayen matarsa

    Wata kotu a kasar Kenya ta yanke hukuncin daurin shekara 30 kan mutumin da aka samu da laifin yanke hannayen matarsa saboda ba ta haihu ba.

    Kamfanin dillancin labarai na PANA ya rawaito cewa alkalin kotun yankin Machakos da ke kasar Kenya ta yanke wa Stephen Ngila, mai shekara 39, hukuncin zaman gidan maza na shekara ne saboda samunsa da laifin yunkurin kisan kai.

    Kotun ta ce mutumin ya guntile wa matarsa Jackline Mwende hannaye da adda a shekarar 2016.

    Alkalin kotun mai shari'a Brenda Bartoo ta ce Stephen bai yi nadamar abin da ya aikata ba.

    Sai dai an ba shi damar daukaka kara nan da kwana 14.

  11. Matar da aka harba a zanga-zangar Myanmar na cikin mawuyacin hali

    Matar da aka harba a kai lokacin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin da soji suka yi a Myanmar na cikin mawuyacin hali a asibiti da ke Nay Pyi Taw babban birnin kasar.

    Mya Thwe Thwe Khaing, mai shekaru 19, ta samu rauni a ranar Talata lokacin da ‘yan sanda suka yi kokarin tarwatsa masu zanga-zanga ta hanyar amfani da harsasan roba da na gaske da kuma motar ruwan zafi.

    Ta samu raunin ne daga harbin da aka yi mata da harsashin gaske, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka bayyana.

    Akwai wasu rahotanni samun munanan raunuka bayan da ‘yan sandan suka kara kaimi wajen yin amfani da karfin tuwo kan masu gangamin amma har yanzu ba a samu asarar rayuka ba.

    Dubban mutane ne suka fita kan titina domin gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulkin, da ya kawo karshen mulkin gwamnatin dimokaradiyya ta Aung San Suu Kyi, duk kuwa da kafa dokar haramta taruwar jama’a da kuma ta hana fita da dare da aka yi.

    Zanga-zangar ta fara gudana ne da safiyar Laraba, har na tsawon kwanaki biyar a jere, inda kungiyoyin ma’aikata da dama suka hallara a birnin na Nay Pyi Taw domin gangamin.

  12. Minti Daya Da BBC Na Rana

    Latsa alamar lasifika da ke kasa domin sauraren Fauziyya Kabir Tukur wacce ta karanto muku labarai cikin minti daya da BBC na rana.

  13. Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram a garin Rann

    Kamfanin dillancin labarai na PR Nigeria ya ruwaito cewa dakarun Najeriyar sun daƙile wani hari a garin Rann inda suka kashe mahara 19 a cikin asu motocin yaƙi biyar.

    Rann wani babban gari ne a ƙaramar hukumar Balge da ke jihar Borno.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu jami'an hukumar fasa kwabri ta Najeriya suka ɓace bayan sojojin sun daƙile wani harin na daban a Geidam, kamar yadda PR Nigeria ya ruwaito.

    PRNigeria ya ruwaito cewa maharan sun far wa garin Rann ne da misalin ƙarfe 6 na yamma a cikin motocin yaki takwas da babura da dama inda suka yi yunƙurin kai wa wani sansanin sojoji hari.

    Kamfanin ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun fatattaki ƴan bindigar ne ta sama da ƙasa kuma nan da nan maharan suka tsere.

  14. Afrika ta Kudu na duba yiwuwar sayar da riga-kafin Oxford-Astrazeneca

    Afrika ta Kudu na duba yiwuwar yin musaya ko kuma sayar da allurar riga-kafin cutar korona ta Oxford-Astrazeneca, in ji ministan lafiyar ƙasar.

    An dakatar da shirin yi wa ma'aikatan lafiya allurar ne bayan da wani ƙaramin bincike ya nuna allurar ba ta aiki kan sabon nau'in cutar da ta ɓulla a cutar a tsakanin matasa.

    Yanzu ƙasar na shirin sayen wata alluar ta kamfanin Johnson & Johnson a madadin na Oxford-Astrazeneca.

    Afrika ta Kudu na da allurar miliyan ɗaya da rabi.

    Minista Zweli Mkhize ya ce "Akwai ƙasashen da suka riga suka fara neman mu sayar masu da allurar.".

    Kawo yanzu mutum milyan 1.5 ne suka kamu da cutar korona a Afrika ta Kudu, kuma mutum 47,000 ne suka mutu.

    Wannan ya haura na ko wace ƙasa a nahiyar.

  15. An buɗe hanyoyin intanet a Uganda bayan sama da mako uku

    Gwamnatin Uganda ta sanar da buɗe hanyoyin intanet da shafukan sada zumunta a ƙasar.

    "Muna ba da hakuri kan duk wani matsi da hakan ya janyo, amma mun yi ne don tsaron ƙasarmu," a cewar Peter Ogwang, ƙaramin ministan harkokin sadarwa.

    An taƙaita hanyoyin intanet ɗin ne a jajiberin zaɓe ran 14 ga Janairu.

    Shugaba Yoweri Museveni a lokacin ya zargi shafukan sada zumunta da ƙin gaskiya da ɗaukar ɓangare.

    Wanann zuwa ne a dai-dai lokacin da Facebook ya ce ya sauke shafuka sama da 200 da ke da alaƙa da kamfe ɗin jam'iyya mai mulki.

  16. An harbi wata mata cikin masu zanga-zangar Myanmar

    Wata mata da aka harba a kanta yayin zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a Myanmar na cikin mawuyacin hali a wani asibiti a babban birnin ƙasar Nay Pyi Taw.

    An harbe ta ne ranar Talata yayin da ƴan sanda ke ƙoƙarin watsa masu zanga-zangar ta hanyar amfani da ruwan zafi da harsasai.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce raunin da ta samu ya yi kama da wanda harsashin bindiga zai ji wa mutum.

    Kawo yanzu dai babu wanda ya rasa ransa.

    Dubban mutane ne suka hau titunan ƙasar don zanga-zanga kan juyin mulkin da ya hamɓarar da mulkin Aung San Suu Kyi na dimokuraɗiyya a makon da ya wuce.

  17. Kotu ta umarci CBN ya buɗe asusun bankin masu zanga-zangar #EndSARS

    Wata babbar kotu a Abuja ta umarci Babban Bankin Najeriya, CBN ya buɗe asusun banki na wasu masu zanga-zangar #EndSARS su 20.

    CBN ya dakatar da asusun mutanen ne a 2020 lokacin da ake tsaka da zanga-zangar na ta nuna adawa da cin zarafin da ƴan sanda ke yi wa matasa a kasar.

    Alƙali Ahmed Mohammed ne ya yanke hukuncin ranar Laraba bayan cimma matsaya tsakanin lauyoyin masu zanga-zangar da na CBN.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa CBN ya ce ya ɗauki matakin dakatar da asusun ne don binciken masu zanga-zangar bisa zargin laifukan da suka danganci ta'addanci da dai sauransu.

  18. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da kafa gwamnatin riƙo ta haɗin gwiwa a Libya

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi maraba da kafa gwamnatin riƙo ta haɗin gwiwa a Libya inda ta bayyana ta a matsayin wani mataki mai muhimmanci.

    An kafa wani kwamiti da zai sa ido kan miƙa mulkin a makon jiya, wanda ya ƙunshi firayim minista da mutum uku daga majalisar shugaban ƙasa.

    Ana fatan zai maye gurbin hukumomi masu adawa a Tripoli da Benghazi.

    Idan komai ya tafi yadda ya kamata, zai sa ƙasar ta gudanar da zabuka a shekara mai zuwa.

    A wata sanarwa da Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta yi kira da a bi cikakken tsari don samun maslaha a ƙasar.

    Libya dai ta auka cikin ruɗani da tashin hankali ne tun da dakaru masu samun goyon bayan ƙungiyar tsaro ta Nato suka yi wa shugabanta Muammar Gaddafi juyin mulki a 2011.

  19. Korona na ci gaba yaɗuwa sosai a Saudiyya

    Saudiyya ta ce cutar korona na ƙara yaɗuwa sosai a faɗin ƙasar.

    Hukumomin lafiya sun ce cutar ta ƙaru da kashi 330 cikin 100.

    Waɗanda cutar ke yi wa mummunan kamu har su buƙaci kulawa ta musamman sun ƙaru da kashi 41 cikin 100, a cewar ma'aikatar lafiya.

    Sabbin kamuwa a kwana ɗaya da ya gabata sun kai 353 kuma hakan ya sa adadin masu ɗauke da cutar gaba ɗaya ya kai 370,987 yayin da mutum 6,410 suka mutu.

    Kawo yanzu an rufe masallatai 12 na wucin gadi a wurare daban-daban na ƙasar bayan da aka gano masu ɗauke da cutar a tsakanin masu ibada.

  20. Tauraron ɗan Adam na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya isa duniyar Mars

    Haɗaɗdiyar Daular Larabawa na murnar aika tauraron dan Adam dinta duniyar Mars a karon farko.

    Ta aika da tauraron ne mai suna Hope a kusa da duniyar, kuma wannan ya sa ya zama na biyar kawai a cikin jerin taurarin da ke yawo a sararin samaniya bayan na Amurka da Rasha da Turai da Indiya.

    Jirgin wanda ya bar doron ƙasa wata bakwai da ya wuce ya ci burki a hanyarsa ta tafiya don auna ainihin ƙarfin juyawar duniyar Mars.

    Masana kimiyya a UAE a yanzu na iya fatan karantar yanayin duniyar.

    Taurarin ɗan Adam ɗin nasu na ɗauke da wasu na'u'rori uku da ke sa ido kan yadda ƙwayoyin halittar iskar hydrogen da ta oxygen ke shiga sararin samaniya.

    Hope zai riƙa ɗakko hotunan Marsa masu haske da inganci sosai.