Bankin Duniya ya amince ya bai wa Najeriya tallafin dala miliyan 500 domin bunƙasa rarraba wutar lantarki ga mazauna ƙasar.
Kudin da suka zarta naira biliyan 150, za a bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar, inda su kuma za su samar da mitocin lantarkin da 'yan Najeriya suka daɗe suna nema.
"Bugu da ƙari, za a bayar da tallafin kuɗi ga kamfanonin masu zaman kansu domin haɓaka sakamakon da ake samu wurin sadar da 'yan Najeriya da wuta da kuma faɗaɗa ta," a cewar wata sanarwa daga bankin a yau Juma'a.
Bankin ya ce ƙiyasin 'yan Najeriya miliyan 85 ne ke cikin duhu, abin da ya yi daidai da kashi 43 cikin 100 na al'ummar ƙasar, kuma hakan na nufin Najeriya ce ta fi kowace ƙasa yawan marasa hasken lantarki a duniya.
Ana yin asarar aƙalla naira tiriliyan 10 duk shekara a Najeriya sakamakon rashin tabbatacciyar wutar lantarki, wanda ya yi daidai da kashi biyu cikin 100 na baki ɗayan arzikin cikin gida na ƙasar.
"Samar da tsayayyar wutar lantarki babbar hanya ce ta fitar da mutane daga talauci tare da buɗe hanyoyin arziki bayan wucewar annobar korona," in ji Shubham Chaudhuri, shugaban Bankin Duniya a Najeriya.