Mutum biyu sun mutu, an ceto mutum 14 a hannun 'yan fashi a Kaduna

Wannan shafin na kawo muku labaran abubuwa da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da ma wasu ƙasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Umar Mikail

  1. Ƙarshen rahotannin kenan

    A nan muke rufe wannan shafi, wanda ya kawo labaran abubuwan da suka faru a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Me zai hana mu haɗu da ku gobe da safe idan Allah ya kai mu domin kawo muku wasu rahotannin kai-tsaye!

    Umar Mikail ne yanzu ke cewa mu zama lafiya

  2. Mutum biyu sun mutu, an ceto mutum 14 a hannun 'yan fashi a Kaduna

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Samuel Aruwan

    'Yan bindiga sun kashe mutum biyu yayin wani hari da suka kai a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna.

    Haka nan 'yan fashin sun saci babur guda huɗu a ƙauyen, a cewar wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar a yau Juma'a.

    Sanarwar ta ce tun farko 'yan fashin sun kai hari gidan Abdulazeez Sani, wani kansila a yankin, inda suka ɗauke matarsa da 'ya'yansa biyu, Aliyu da Lawal, da kuma wata mace mai suna Halima M. Sani da ɗanta.

    Dakarun sa-kai na vigilante sun tare maharan yayin da suke ƙoƙarin guduwa da mutanen a ƙauyen Ungwan Mai Turmi da ke Ƙaramar Hukumar Igabi mai maƙwabtaka.

    Harbe-harben da suka biyo baya ne suka sa miyagun suka saki waɗanda suka kama kuma suka tsere. Sai dai sun kashe Musa Isah da Yusufa Suleiman tare da harbin mata biyu - Hafsatu Isah da Fatima Suleiman - a Unguwan Hazo.

    A wani filin dagar na daban, jami'an tsaro sun ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su a Birnin Gwari, inda tuni aka haɗa su da danginsu.

  3. Rasha ta kori jakadun Tarayyar Turai saboda zargin shiga zanga-zanga

    Rasha

    Asalin hoton, EPA

    Rasha za ta kori jami'an diflomasiyya uku na ƙasashen Jamus da Poland da kuma Sweden sakamakon abin da ta kira shiga zanga-zangar da ta saɓa ƙa'ida ta sakin jagoran ƴan adawa Alexei Navalny.

    Shugaban tsare-tsaren harkokin wajen Tarayyar Turai, Jozep Borell, ya nuna rashin jin daɗinsa matuƙa kan wannan korar yayin wata tattaunawarsa da ministan harkokin wajen Rasha.

    Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce matakin na Rasha sam bai kamata ba, inda ta ce hakan wuce gona da iri ne a doka.

    Shi ma ministan harkokin wajen Poland ba a bar shi a baya ba, inda ya aika da sammaci ga jakadan Rasha a ƙasar. Haka nan, ita ma Sweden ta yi watsi da lamarin.

  4. Ngozi Okonjo Iweala ce kaɗai ta rage a takarar WTO

    Ngozi Okonjo Iweala

    Kwan-gaba- kwan-baya da ake samu kan naɗa wadda za ta jagoranci kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) ya kawo ƙarshe, inda a yaznu ake sa ran Ngozi Okonjo Iweala daga Najeriya za ta zama mace ta farko da za ta riƙe muƙamin.

    Ms Okonjo Iweala ta ce akwai jan aiki a gaba, inda ta yi kira da a samu haɗin kan kowa.

    Waɗannan kalaman nata na zuwa ne bayan ministar kasuwancin Koriya Ta Kudu, Yoo Myung-hee, ta janye daga takarar bayan shawarar da Amurka da kuma wasu ƙasashen da ke goya mata baya suka ba ta.

    Ana zaɓen wanda zai jagoranci kungiyar ne ta hanyar cimma matsaya ko yarjejeniya, inda kuma aka kasa samun hakan tun a Oktoban 2020 bayan tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa zaɓen Ms Iweala ƙafar ungulu.

  5. Bankin Duniya zai tallafa wa Najeriya da biliyan ₦150 don haɓaka lantarki

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    Bankin Duniya ya amince ya bai wa Najeriya tallafin dala miliyan 500 domin bunƙasa rarraba wutar lantarki ga mazauna ƙasar.

    Kudin da suka zarta naira biliyan 150, za a bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar, inda su kuma za su samar da mitocin lantarkin da 'yan Najeriya suka daɗe suna nema.

    "Bugu da ƙari, za a bayar da tallafin kuɗi ga kamfanonin masu zaman kansu domin haɓaka sakamakon da ake samu wurin sadar da 'yan Najeriya da wuta da kuma faɗaɗa ta," a cewar wata sanarwa daga bankin a yau Juma'a.

    Bankin ya ce ƙiyasin 'yan Najeriya miliyan 85 ne ke cikin duhu, abin da ya yi daidai da kashi 43 cikin 100 na al'ummar ƙasar, kuma hakan na nufin Najeriya ce ta fi kowace ƙasa yawan marasa hasken lantarki a duniya.

    Ana yin asarar aƙalla naira tiriliyan 10 duk shekara a Najeriya sakamakon rashin tabbatacciyar wutar lantarki, wanda ya yi daidai da kashi biyu cikin 100 na baki ɗayan arzikin cikin gida na ƙasar.

    "Samar da tsayayyar wutar lantarki babbar hanya ce ta fitar da mutane daga talauci tare da buɗe hanyoyin arziki bayan wucewar annobar korona," in ji Shubham Chaudhuri, shugaban Bankin Duniya a Najeriya.

  6. Rashin fahimta ne ya hana ƙara yawan mazaɓu a Najeriya - INEC

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Ibrahim Isa

    A Najeriya, hukumar zabe ta INEC da jam`iyyun siyasa sun cimma maslaha game da yunkurin da hukumar ke yi na kara yawan rumfunan zabe a fadin kasar.

    Duka bangarorin sun fahinci cewa ana fama da cunkoso a runfunan zabe da dama sakamakon yawan al`umma.

    Wannan maslaha da hukumar ta cimma a Najeriya babban ci gaba ne, ganin cewa tun 1996 da aka kirkiri rumfunan zabe kusan 120,000 ba a kara ba, duk kuwa da karuwar al`ummar da aka samu a kasar.

    INEC ta yi yunkurin kara mazabun a lokuta daban-daban amma ba ta yi nasara ba saboda ana jahiltar manufarta sai a wannan karon.

  7. Sojojin Sweden sun isa Mali don yaƙar masu iƙirarin jihadi

    Sojojin Sweden

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojan Faransa ta ce dakarun ƙasar Sweden sun isa Mali don shiga cikin rundunar musamman ta ƙungiyar Tarayyar Turai mai yaƙi da masu tsattsauran kishin Musulunci.

    A shekarar da ta gabata, majalisar Sweden ta amince da tura sojoji guda 150.

    Sojojin waɗanda suka shiga rundunar Takuba, sun sauka ne a gari mai cike da rikici da ke kan iyakar Nijar da Burkina Faso.

    Tuni dakarun ƙasashen Estonia da Czech suka shiga rundunar.

    Faransa na ci gaba da neman goyon bayan ƙasashen Turai wurin tallafa wa yaƙin da take jogaranta a yankin Sahel mai fama da hare-haren 'yan bindiga.

  8. An zargi sojojin Kamaru da kashe fararen hula

    Kamaru

    Kungiyar Human Rights Watch ta zargi rundunar sojin Kamaru da kashe fararen hula tara ciki har da yarinya mai shekaru 6, a wani kauye a yankin Kudu maso Yammacin kasar masu amfani da turancin Ingilishi.

    Kungiyar ta bayyana haka a wata sanarwa inda suka ce "sojoji sun kashe a kalla fararen hula 9 ranar 10 ga Janairu".

    Ranar 12 ga Janairu, ma'aikatar tsaron Kamaru ta musanta kisan fararen hular, inda ta ce sojojin sun kashe "'yan ta'adda" ne ranar 10 ga Janairu.

    A baya fararen hula da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun

    a zargin rundunar sojin Kamaru da cin zarafin bil Adama a yankin masu amfani da Ingilishi da yankin Arewa, inda suke yaki da Boko Haram.

  9. Buhari zai ƙaddamar da aikin titin jirgin ƙasa na Kano-Maradi

    Buhari

    Asalin hoton, NG Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin gina layin jirgin ƙasa daga Jihar Kano zuwa Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar ranar Talata mai zuwa.

    Ministan Sufuri Chibuike Rotimi Amaechi ne ya bayyana hakan cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa a yau Juma'a.

    "Muna farin cikin sanar da ku cewa za a ƙaddamar da fara aikin titin jirgin ƙasa na Kano-Maradi da Kano-Dutse ranar Talata," in ji Amaechi.

    Ya ƙara da cewa "shugaban Ƙasa Buhari ne zai ƙaddamar. Za a fara aiki".

    A watan Satumban 2020 ne Majalisar Zartarwa ta Najeriya ta amince da kuɗi kusan dala biliyan biyu domin gina layin dogon, wanda zai ratsa jihohin Kano da Katsina da Jigawa sannan ya dangana da Maradi a Jamhuriyar Nijar.

    Ana sa ran za a kammala aikin mai tsawon kilomita 283 cikin shekara uku masu zuwa, a cewar Amaechi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Kotu ta ɗaure fasto saboda yi wa ƙananan yara fyade

    Ɗaurarre

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa wani mai da'awar addinin Kirista dan Amurka hukuncin dauri sama da shekara 16 a gidan kaso saboda cin zarafin yara ta hanyar lalata da su a Kenya a lokacin da yake aiki a wani gidan marayu.

    An kuma umarci Gregory Dow da ya biya $16,000 diyya.

    A bara ne ya amsa laifinsa na yi wa yara mata hudu fyade takanin shekarun 2013 da 2017.

    Gregory Dow da iyalinsa sun koma Kenya ne daga jihar Pennsylvania ta Amurka a 2008 kuma ya kafa gidan marayu na Dow Family Children's Home.

    Tsakanin 2013 da 2017, ya yi wa yara mata hudu fyade a gidan marayun, daya daga cikin yaran na da shekara 11 ne kacal.

    Wata kotu a Pennsylvania ta saurari cewa Mista Dow ya bar kasar bayan zargin yi wa yaran fyade da aka fara yi masa a 2017 a garin Bomet da ke Kenya inda gidan marayun yake.

    Amma an tuhume shi kuma ya amsa laifinsa.

  11. Biden ya yi alkawarin gyara hulɗarsa da ƙasashen Afrika

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin gayra hulɗar ƙasarsa da ƙungiyar ƙasashen Afrika jim kaɗan bayan gabatar da jawabinsa kan manufofinsa na huldar kasa da kasa.

    Donald Trump ya janyo ce-ce-ku-ce a 2018 bisa kiran kasashen Afrika a matsayin "kasashen banza".

    Daga baya Mista Trump ya musanta cewa shi mai wariyar launin fata ne.

    Ranar Juma'a ne Fadar White House ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter, inda Biden ya gabatar da wani jawabi inda ya ce:

    "Gwamnatina a shirye ta ke ta gyara alakarta da sauran ƙasashen duniya da kungiyoyi kamar kungiyar AU.

    Haka kuma, dole ne mu tunkari kalubalen da ke gabanmu. Wannan ya kunshi kiwon lafiya, dakile cutar korona.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Ƴan majalisar Ghana 15 sun kamu da korona

    Ƴan majalisar Ghana 15 da ma'aikatansu 56 sun kamu da cutar korona, kamar yadda kafofin yaɗa labaran kasar suka ruwaito.

    Sun kamu da cutar ne bayan gwaje-gwaje da aka yi a cewar kakakin majalisar Alban Bagbin.

    An bai wa ƴan majalisar da ma'aikatan nasu shawarar su killace kansu a cewar rahotannin.

    Akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu ƴan majalisa na gujewa gwajin koronar.

    Kawo yanzu Ghana na da mutane 69,255 da suka kamu da cutar da mutum 440 da suka mutu sakamakonta tun farkon ɓullar cutar a watan Maris din bara.

  13. Ƴan bindigar Zamfara na bukatar a ilimantar da su - Sheikh Gumi

    Ahmed Gumi

    Asalin hoton, FACEBOOK

    Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Mahmoud Gumi ya bayyana yadda haduwarsa da ƴan bindiga ta kasance a jihar Zamfara.

    Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta ruwaito cewa Malamin ya damu matuƙa da yadda rashin tsaro ya yi yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, shi ya sa ya yi tattaki ya tafi har sansanoninsu.

    Jaridar ta bayyana cewa Malamin ya shaida wa Gwama Bello Matawalle na jihar Zamfara ranar Alhamis cewa ƴan bindigar sun rikiɗa sun zama ƴan ta'adda saboda wulƙancin da al'umar jihar suke masu.

    Ya bukaci gwamnati a dukkan matakai ta yi sulhu da ƴan bindigar, inda ya je tattaunawa ce kawai hanyar da za ta kawo ƙarshen matsalar.

    "A mafi yawan sansanonin ƴan bindigar da Fulani da muka shiga, na fahimci babu wani abu da ke faruwa a jihar nan illa ta'ddanci."

    "Wasu na ganin kamata ya yi a yaƙi ƴan bindigar nan sannan a kashe su, amma mu abin da muka fahimta shi ne mafi yawansu ba su da ilimi. Suna bukatar a ilimantar da su sannan a wayar masu da kai," a cewarsa.

    Daily Trust ta ce Gumi ya ce mafi yawan ƴan bindigar sun zama marasa imani ne saboda yawan kai masu hari da mayaƙan sa kai ke kai masu a jihar.

  14. Kamfanin Johnson and Johnson na so a ba shi izinin fitar da riga-kafinsa na korona

    Kamfanin Johnson and Johnson ya buƙaci mahukunta a Amurka su ba da izini na amfani da allurar rigakafin korona da ya ƙirkira a lokacin gaggawa.

    Babban kamfanin hada magungunan ya ce zai iya samar da allurai miliyan ɗari a ƙarshen watan Yuni.

    Idan har aka amince, allurar ce ta uku da aka ba da damar yin amfani da ita a Amurka bayan ta kamfanin Pfizer-BioNTech da Moderna.

    Johnson and Johnson ya ce a cikin makonni masu zuwa, zai nemi izinin mahukuntan Turai don a fara amfani da rigakafinsa a nahiyar.

  15. Biden zai daina bai wa Saudiyya goyon baya a yakinta da Yemen

    Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Biden ya ce Amurka za ta kawo ƙarshen duk wani goyon baya da take bai wa Saudiya a yaƙin da take a Yemen ciki har da sayar da makamai.

    Mista Biden ya ce shekara shidan da aka shafe ana yaƙar ƴan tawayen Houthi ya jefa jama'a cikin bala'i a don haka dole ne a kawo ƙarshen sa.

    Amma Biden ɗin ya ce Amurka za ta ci gaba da ta taimakawa Saudiyya wajen kare kanta da ga hare-haren makamai masu linzami daga sojojin da Iran ke marawa baya a yankin.

    A martaninta, Saudiyya ta ce za ta goyi bayan ƙoƙarin samar da maslaha ta magance rikicin na Yemen.

  16. Budewa

    Barkanku da Juma'a.

    Muna fatan za ku kasance da wannan shafin da samun labarai kai tsaye daga Najeriya da makwabtanta da sauran kasashen duniya.