Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Wata ƙungiya ta kai ƙarar NAFDAC kotu kan sakaci da aiki

Wannan shafin na kawo maku labarai daga Najeriya da maƙwabtanta da ma sauran ƙasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Fauziyya Kabir Tukur

  1. Ɗan Najeriya da ke jagorantar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Liberia ya yi murabus saboda rikicin zama ɗan ƙasa

    Shugaban hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Liberia, Ndubusi Nwabudike ya yi murabus, a cewar gwamnatin kasar.

    Dama dai ana ta ce-ce-ku-ce kan yadda ya samu shaidar zama ɗan kasar. Mista Nwabudike dan asalin Najeriya ne.

    Sai dai ya dage kan cewa shi dan Liberia ne kuma ya musanta yin wani laifi, amma ya gaza tabbatar wa wani kwamiti a bara sahihancin shaidar zama ɗan Liberia da har ya samu ikon rike mukamai masu girma a kasar.

    Shugaba George Weah ya amince da ajiye aikin nasa ya kuma yi masa godiya bisa hidimar da ya yi wa kasar.

  2. Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'i za ta tafi yajin aiki

    Jaridar Daily Trust ra ruwaito cewa Kwamitin haɗin gwiwa na kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i (SSANU) da NASU a Najeriya za su tafi yajin aikin sai baba-ta-gani ranar 5 ga watan nan na Fabrairu kamar yadda suka shirya.

    Shugaban SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim da Babban Sakataren NASU, Peters Adeyemi suka bayyana wa manema labarai a Abuja bayan wata tattaunaawa sirri da wakilan gwamnatin tarayya wadda Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya jagoranta.

    Adeyemi ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin ƙungoyiyin ba su da ikon sa mambobinsu su dage yajin aikin.

    "Don haka mun ce gwamnati ta ba mu lokaci mu sake ganawa da mambobinmu don mu san matakin da za mu dauka," a cewarsa.

    Batutuwan da aka tattauna sun haɗa da batun tsarin biyan albashi na IPPIS da tsaikon da aka samu wurin tattaunawar nan ta tsakanin Gwamnatin Tarayya da NASU da SSANU ta 2009 da rashin biyan alawus-alawus na wadanda su ke shirin yin ritaya.

    A nasa ɓangaren, Chris Ngige ya ce an samu ci gaba a tattaunawar ta hanyar kafa kwamitin da zai duba matsalolin IPPIS.

    Kwamitin ya ƙunshi ƙungiyoyin ƙwadagon da jami'an gwamnati daga ma'aikatar ilimi da ofishin Akanta janar na kasar da sauransu.

    Ya ce za su aiki tare don ganin an warware dukka matsalolin.

  3. Har yanzu ba a bai wa mata ƴan ƙabilar Ibo gadon iyayensu

    Har yanzu ba a bai wa mata gadon iyayensu a yankin kudu maso gabashin Najeriya, duk da umarnin da Kotun Ƙoli ta bayar na hana nuna wannan wariyar.

    Bayan mahaifin Onyinye Igwe ya rasu shekara biyu da suka gabata, sai rayuwa ta yi mata tsanani duk da cewa ya mutu ya bar tarin dukiya kamar gidaje da filaye da kuɗaɗe a banki.

    Mahaifinta ya bi sahun galibin maza masu ra'ayin riƙau a ƙabilar da ba ta yarda da barin wasiyyar gado ba, don haka da ya mutu sai ƴaƴansa suka ɗauki ragamar raba gadon.

    Duk da cewa Onyinye mai shekara 29 ce babbar ƴarsa, ita da sauran ƙannenta mata biyar ba su tashi da ko sisi ba - ƴan uwanta maza uku ne suka mallake komai kamar yadda al'adar ƙabilar Ibo ta tanada.

    Ta shaida wa BBC cewa : "Ƴan uwana maza sun handame duk abin da mahaifinmu ya mallaka.

    "Sun ce mana mu mata aure za mu yi a gidan wani don haka ba za mu gaji komi na mahaifinmu ba. Saboda haka al'adar take, mu kuma ba mu yi faɗa da su kan hakan ba."

    Karanta ƙarin bayani a nan.

  4. Ana yi wa mata ƴan ƙabilar Uighur fyaɗe don azabtar da su

    BBC ta samu muhimman shaidu dake bayyana yadda ake yi wa mata fyade da azabtar da su a sansanonin da aka boye musulmiai yan kabilar Uighur a China.

    Wakilin BBC yace ya ji bayanan shaida masu tada hankali, da suka hada da azabtarwa da ƙarafan lantarki, da kuma wani lokaci da aka tilastawa kimanin 100 daga cikinsu kallon yadda jami'an tsaro ke yi wa ɗaya daga cikinsu fyaɗe ta ƙarfi da yaji.

    A cikin wata sanarwa, gwamnatin China ta ce ta dukufa wajen kare ƴancin mata.

    Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam dai sun ce kusan musulman Uighur dubu ɗari biyar ne ake tsare da su.

    Hukumomin ƙasar sun ce ana koya musu sana'o'i ne don kaucewa samun masu tsatstsauran ra'ayi a cikinsu.

  5. Biden ya fara sauya tsauraran dokokin gwamnatin Trump da ke adawa da baƙin haure

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya ɗauki matakan farko don sauya wasu daga cikin tsauraran dokokin gwamnatin Trump da ke adawa da bakin haure.

    Ya sanar da ƙirƙirar wani kwamiti don sake haɗa yaran da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta raba su da iyayensu a kan iyakar Amurka da Mexico.

    Da yake sanya hannu kan umarnin a Fadar White House, Mista Biden ya ce za su warware abin da ya kira ''Rashin imani gwamnatin da ta shude''.

    A ranar Talata ne majalisar dattijan Amurka ta tabbatar da wani lauya ɗan asalin Cuba, Alejandro Mayorkas, a matsayin Sakataren hukumar tsaron Cikin gida ta Homeland.

    Ya zama bakon haure na farko da ya jagoranci hukumar da ke kula da batutuwan shige da fice da kan iyaka.

  6. Adadin masu fama da talauci a Najeriya zai ƙaru da mutum miliyan 15- World Bank

    Babbar jami’ar Babban Bankin Duniya a ɓangaren Tattalin Arziƙi, Gloria Joseph- Raji ta bayyana cewa annobar cutar korona ta yi wa tattalin arziƙin Najeriya babban naƙasu inda harƙasar ta fuskanci koma bayan tattalin arziƙin a shekarar 2020, koma baya mafi tsanani tun shekarun 1980, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    “Don haka, ganin babu ci gaba a tattalin arzikin ga rashin aikin yi sannan ga hauhawar farashi, mun yi kiyasin cewa adadin mutanen da ke fama da talauci zai karu da kusan mutum miliyan 15 zuwa 20 zuwa shekarar 2022.

    “A baya mutum miliyan 83 ke fama da talauci a Najeriya a kiyasinmu na 2019,” a cewarta.

    A cewarta, Najeriya na bukatar gyara manufofinta don taimakawa sana’o’i sannan a inganta walwalar ƴan ƙasar.

    Shi ma Dakta Doyin salami. Shigaban majalisar da ke bai wa shugaban Najeriya shawara kan tattalin arziki ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta kaddamar da sauye-sauye masu muhimmanci don fitar da ƴan ƙasar daga halin da suke ciki na talauci.

    Misis Raji ta ce ƙididdigar Babban Bankin Duniya ta nuna cewa Najeriya na wani mataki mai wahalar tsallakewa a yanzu saboda fitar da mutum miliyan 100 daga cikin talauci zuwa shekarar 2030 abu ne mai wahala ganin cewa ko kafin annobar korona, kasar na cikin wani hali.