Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun kashe Danleeman Isah, limamin garin Kawaran Rafi da ke Ƙaramar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.
Sun kashe limamin ne yayin da suka far wa ƙauyen. Sai dai sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar a jiya Asabar ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
Aruwan ya ce kisan nasa na da alaƙa da sukar da malamin yake yi kan ayyukan miyagun na garkuwa da mutane da satar shanu.
"'Yan fashin sun wuce kai-tsaye zuwa gidan Danleeman, kuma kamar da ma abin da ya kai su kenan, suka harbe shi tare da barin wurin ba tare da sun ɗauki komai ba ko kuma garkuwa da wani," in ji sanarwar.
Kazalika, kwamishinan ya lissafa mutum biyu da aka yi wa irin wannan kisa sakamakon sukar ayyukan 'yan fashin da suke yi.
Mutanen su ne Ardo Musa Layi, wanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Kajuru a Oktoban 2020, da kuma Ardo Ahmadu Suleiman wanda suka halaka a Kasuwan Magani, shi ma a Kajuru.
Bugu da ƙari, Aruwan ya tabbatar da mutuwar Sarkin Yakin Godogodo mai suna Yohanna Abu, bayan wasu miyagu sun kai wa garin Nisama hari da ke Ƙaramar Hukumar Jema'a a daren Juma'a.
Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Charles Audu ya rasa ransa a harin sannan suka yi garkuwa da wani mai suna Mr Abu.