Yadda ƴan fashi suka kashe wani limami a Jihar Kaduna saboda yana sukarsu
Wannan shafi ne da ke kawo muku abarai da rahotanni na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sasssan duniya a ranar da muka shiga sabuwar shekarar 2021.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Imam Saleh
Rufewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Imam Saleh
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu ta wannan shafi a nan muka zo ƙarshen kawo muku labaran duniya kai tsaye a wannan rana ta Lahadi.
Sai kuma gobe Litin domin ci gaba.
Domin karanta labaran da muka wallafa na yau sai ku koma ƙasa.
Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya.
Labarai da dumi-dumi, Wasu mahara sun kashe mutum 14 a Kaduna
Asalin hoton, AFP
Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne a daren Asabar sun kashe kimanin mutane 14 a garin Kaya, wani kauye da ke karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yamma. lokacin da 'yan fashin, wadanda aka ce suna shirin daukar fansa ne, suka afka wa karamin kauyen suka kashe mutanen kuma suka bankawa motoci wuta.
Wani mazaunin yankin, wanda kawai ya bayyana kansa a matsayin Suleiman, ya ce mutane tara sun samu raunuka.
A cewarsa, a safiyar ranar Juma'a, wasu 'yan banga a yankin sun kashe wasu' yan ta'adda da suka kai hari a wani kauye da ke makwabtaka da su.
”‘ Yan fashin sun far wa kauyen mu ne don daukar fansar kisan da mambobin mu da ‘yan banga mu ka yi bayan sun sace tare da kashe mutum daya a ranar 1 da 2 ga watan Janairu. Don haka suka dawo cikin dare ranar Asabar a kan babura suka kashe mutane 14, ”inji shi, kamar yadda Premium Times ta rawaito.
''Yawan waɗanda aka kashe yayin wani hari a Jamhuriyyar Nijar ya kai 100''
Asalin hoton, AFP
Jami'ai a Jamhuriyar Nijar sun ce kimanin mutum 100 ne suka mutu a wani hari da aka kai wasu kauyuka biyu a kasar, wanda ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai.
Wani masaraucin gargajiya ya ce kimanin mutum 70 aka kashe a kauyen Cho-ma Bangu, aka kuma kashe 30 a Zaro-madare.
Yace gwamman masu ikirarin jihadin ne suka kutsa yankin a kan babura.
Kauyukan dai na yankin jihar Tillaberi ne, kusa da iyakar kasar da Mali, ida kuma ya yi fice da ayyukan masu ikirarin jihadi.
An dai aika wasu dakarun gwamnati na musamman zuwa yankin.
Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a Jamhuriyyar Nijar
Asalin hoton, Google
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani gari da ke kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan ta-da-kayar baya suka yi, ya na mai bayyana lamarin da cewa wani kira ne na ganin an hada karfi da karfe don magance ta'addanci.
Shugaba Buhari ya ce, "Na yi matukar kaduwa da kisan mutane da dama marasa laifi'' da wadannan mugayen tsageru suka yi.
A cewar Shugaban, "Muna fuskantar babban ƙalubale na tsaro saboda yaƙin da ake yi da ƴan ta'adda a yankin Sahel kuma daukar matakan hadin kai ne kawai zai taimaka mana wajen fatattakar wadannan muggan makiya jama'a''.
Ya bayyana cewa "ta'addanci yanzu ya zama kamar wata muguwar cuta wacce ke iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba."
Shugaba Buhari ya ce "rashin zaman lafiya a wani yanki na Afirka na da tasiri ga tsaron wasu wasu ƙasashen."
Ambaliya ta fatattaki mutane daga gidajensu a Malaysia
Wata mummunar ambaliyar ruwa a jihar Johor ta Malaysia ta tilasta wa mutane fiye da dubu shida barin gidajensu.
Ana fargabar wani mutum ya mutu bayan da ta yi awon gaba da motarsa.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya haddasa ambaliyar a yankin Mahara, abin da ya haifar da zaftarewar kasa.
Wasu iyalai sun ba da rahoton sun makale a tsakanin wasu magudanar ruwa biyu a kan wata hanya kusa da wurin shakatawar Fraser.
Haka nan ruwa ya cinye hanyoyi da yawa a yankin.
Armashin zanga-zangar Belarus na raguwa
Asalin hoton, Getty Images
An ci gaba da zanga-zanga a kasar Belarus kan shugaban kasar, Alexander Lukashenko, kusan watanni biyar bayan gudanar da zaben shugaban kasa da aka yi tir da shi.
Mutane sun taru a gundumomin da dama na babban birnin Minsk, da sauran garuruwa, suna daga tutocin adawa na ja da fari, yayin da suke tafiya a yanayi sanyi da ake ciki a kasar.
Amma a karon farko cikin watanni yan adawa basu yi wani kira na a fito zanga zangar ba.
Yawan masu fita zanga-zangar ya ragu sosai a makwannin nan, a daidai lokacin da hukumomi ke ci gaba da murƙushe jama'a.
Masar ta fara bincikar wani asibiti da masu korona da dama suka mutu a cikinsa
Asalin hoton, AFP
Masu gabatar da kara a Masar sun fara bincike bayan da masu cutar korona da dama suka mutu a wani asibiti saboda karancin naurar taimakawa numfashi.
Yawancin al'ummar kasar sun nuna fushinsu ta Internet kan abin da ya faru a asibitin al-Husseiniya da ke lardin Sharqia.
Hakan na faruwa ne yayin da kasar Masar ta amince da wata allurar rigakafin korona da kamfanin Sinopharm ya samar.
Fiye da mutane dubu ɗari da arba'in ne suka kamu da cutar a hukumance a kasar.
Sojojin ƴan tawayen Afrika ta tsakiya sun kai sabon farmaki
Asalin hoton, Getty Images
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta
Tsakiya ya ce sojojin ƴan tawaye sun kai hari a kudu maso gabashin garin
Bangassou.
An ba da rahoton arangama tsakanin dakarun hadin
gwiwar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan
sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Fararen hula na tserewa ta kan iyaka zuwa Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Kawancen ‘yan tawayen sun kai hari kan garuruwa da dama a
makonnin da suka gabata, suna zargin gwamnati da yin magudi a zabe.
Mutane da
yawa ba su sami damar yin zaɓen a watan da ya gabata ba saboda rashin tsaro.
Sojojin Najeriya sun ƙaddamar da sabon shirin tsaro a kan hanyar Kaduna-Abuja
Asalin hoton, Nigeria Airforce
Rundunar sojojin sama ta Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon shiri da ta yi wa laƙabi da "Operation Taimako Ya Zo" domin kakkaɓe miyagun da ke kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hafsan Sojojin Sama na Najeriya Air Marshal Sadique Baba Abubakar ya ce nan gaba kaɗan za su faɗaɗa shirin zuwa Jihohin Zamfara da Katsina.
"Wannan aiki ne da za mu ci gaba da yinsa ƙari a kan wasu guda shida da muke tsarawa," in ji shi.
Manufar shirin ita ce zaƙulowa tare da maganin 'yan fashi masu garkuwa da mutane da ke kamawa tare da kashe mutane a kullum a kan hanyar mai nisan kilomita kusan 200.
A ranar Litinin ne gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana kisan ƙasurgumin jagoran miyagun mai suna Nasiru Kachalla, wanda ya mutu yayin wani artabu da wasu 'yan bindigar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sojojin Najeriya sun yi wa sansanonin Boko Haram ruwan wuta
Asalin hoton, Nigerian Military
Hedikwatar tsaro ta sojojin Najeriya ta ce jiragenta sun tarwatsa sansanonin ƙungiyar Boko Haram a Jihar Borno tare da kashe wasu daga cikin mayaƙan.
Shugaban sashen yaɗa labarai na hedikwatar Manjo Janar John Enenche ya ce dakarun rundunar musamman ta Operation Lafiya Dole ta yi wa sansanonin biyu ruwan wuta a Kote Kura da Bulama Isamari jiya Asabar.
Jiragen yaƙi da na helikwafta sun kai hare-haren ne bayan samun rahotannin sirri da suka nuna cewa 'yan Boko Haram sun kafa sabbin sansanoni a wuraren, a cewar sanawar da Janar ɗin ya fitar a yau.
Wani bidiyo da rundunar ta wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda wasu wurare ke ci da wuta bayan jiragen sun harba ababen fashewa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
'Ya kamata mu koyi darasi daga bala'in da aka shiga a shekarar 2020'
Annobar cutar korona ta yi matuƙar tagayyara rayuwar tsofaffi. Mahnaz Rehman, wata mai shekara 71 daga Karachi a Pakistan, ta ce ta yi ban-kwana da shekarar cikin matuƙar taƙaici.
Ta rasa mijinta bayan ya sha fama da doguwar rashin lafiya, ta yadda ta kasa gayyatar ƴan uwa da abokan arziƙi zuwa wajen jana’izarsa saboda dokar kulle da aka sanya a lokacin.
A yanzu da aka ɗage wasu dokokin kullen, ta bayyana yadda shekarar ta zo mata, da darussan da take ganin ya kamata al’ummar duniya su koya daga yanayin da aka samu kai a ciki.
Wannan fim ɗin da Karim ul-Islam ya shirya an yi shi ta hanyar bin dokar yin nesa-nesa da juna, kuma yana cikin jerin wasu bidiyo da BBC ta samar masu taken ‘Abin da na koya daga shekarar 2020’.
Gobe Litinin za a fara riga-kafin korona ta biyu a Birtaniya
Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da rarraba allurar riga-kafin korona da Jami'ar Oxford da Astrazeneca suka sarrafa a sassa daban-daban na Birtaniya a shirye-shiryen fara aikin riga-kafin a gobe Litinin.
Ana ta tanadar ɗaruruwan sabbin cibiyoyi domin abin da ka iya zama gagarumin mataki na faɗaɗa aikin riga-kafin a kasar.
Mataimakin shugaban kwamitin riga-kafin korona na Birtaniya, Furofesa Anthony Hernden, ya ce: "Wani abu da ya sanya dole mu tunkari wannan ƙwayar cuta shi ne cewa an san tana yaɗuwa cikin hanzari matuƙa, kuma ta samu nasarar yaduwa.r''
Birtaniya za ta kasance ƙasa ta farko da za ta yi amfani da wannan allurar rigakafin - wadda ba kamar sauran alluran da ake amfani da su ba - wadda ba dole ne a adana ta a cikin tsananin sanyi ba.
Yayin da Birtaniya ke gaban sauran duniya a ayyukan riga-kafi, a ɓangare guda kuma ita ce kasar da sabon nau'in ciwon na korona mai saurin yaɗuwa ya fi addaba.
'Yan fashi sun kashe limami a Jihar Kaduna saboda yana sukarsu
Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi ne sun kashe Danleeman Isah, limamin garin Kawaran Rafi da ke Ƙaramar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna.
Sun kashe limamin ne yayin da suka far wa ƙauyen. Sai dai sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar a jiya Asabar ba ta bayyana lokacin da lamarin ya faru ba.
Aruwan ya ce kisan nasa na da alaƙa da sukar da malamin yake yi kan ayyukan miyagun na garkuwa da mutane da satar shanu.
"'Yan fashin sun wuce kai-tsaye zuwa gidan Danleeman, kuma kamar da ma abin da ya kai su kenan, suka harbe shi tare da barin wurin ba tare da sun ɗauki komai ba ko kuma garkuwa da wani," in ji sanarwar.
Kazalika, kwamishinan ya lissafa mutum biyu da aka yi wa irin wannan kisa sakamakon sukar ayyukan 'yan fashin da suke yi.
Mutanen su ne Ardo Musa Layi, wanda aka kashe a Ƙaramar Hukumar Kajuru a Oktoban 2020, da kuma Ardo Ahmadu Suleiman wanda suka halaka a Kasuwan Magani, shi ma a Kajuru.
Bugu da ƙari, Aruwan ya tabbatar da mutuwar Sarkin Yakin Godogodo mai suna Yohanna Abu, bayan wasu miyagu sun kai wa garin Nisama hari da ke Ƙaramar Hukumar Jema'a a daren Juma'a.
Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Charles Audu ya rasa ransa a harin sannan suka yi garkuwa da wani mai suna Mr Abu.
Gwamna Zulum ya ziyarci mafarautan da Boko Haram ta jikkata a asibiti
Asalin hoton, @GovBorno
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulium ya ziyarci mafarauta guda shida da ke samun kulawa a asibiti biyo bayan raunin da suka ji sakamakon taka abin fashewar da mayaƙan Boko Haram suka dasa a kan hanya.
Mutum bakwai daga cikinsu ne suka mutu nan take kuma wasu 16 suka ji raunuka yayin da mayaƙan na sa-kai ke fatro a kusa da dajin Sambisa, a cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.
Kwamishinan Wasanni Sainna Buba ya ce an sallami 11 daga cikin 16 bayan an ba su magunguna a Asibitin Ƙwararru na Jami'ar Maidudri.
Gwamna Zulum ya koma jihar ne ranar Asabar daga Abuja bayan ya gana da Shugaba Buhari da Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama da shugaban hukumar bayar da agaji ta NEMA kan tallafa wa 'yan gudun hijira da yaƙin Boko Haram ya raba da mahallansu.
Zimbabwe ta sake saka dokar kulle ta ƙasa baki ɗaya
Asalin hoton, EPA
Gwamnatin Zimbabwe ta sake ƙaƙaba dokar kulle ta ƙasa baki ɗaya nan take biyo bayan ƙaruwar yaɗuwar cutar korona.
Masu ayyukan da suka zama dole ne kaɗai kamar asibitoci da wuraren shan magani da manyan kantuna za su ci gaba da kasancewa a buɗe har tsawon kwana 30, a cewar rahoton AFP.
Dokar hana fita za ta riƙa aiki daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe.
Da ma tuni ƙasar wadda ke kudancin Afirka ke fama da rikicin tattalin arziki da tashin farashin kayayyaki da kuma rashin aikin yi.
A watan Maris da ya gabata ne aka fara saka dokar kullen da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona amma sai aka sassauta saboda a dawo harkokin kasuwancin da zai taimaka wa tattalijn arziki.
Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma Ministan Lafiya Constantino Chiwenga ya faɗa wa 'yan jarida cewa an samu ƙaruwar masu kamuwa da cutar yayin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara da suka kusa ninka waɗanda aka samu a tsawon shekarar.
Jumillar mutum 14,084 ne suka kamu da cutar a Zimbabwe, yayin da 369 suka mutu.
An kashe sojojin Faransa a Mali
An kashe sojojin Faransa biyu a gabashin Mali yayin wani aikin tattara bayanan sirri.
Ofishin Shugaba Macron ya ce motarsu ce ta taka nakiya a yankin Menaka.
Lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan da irin wannan nakiyar ta kashe wasu sojojin Faransa uku a gabashin ƙasar.
Wannan adadin ya sa jumillar sojojin Faransa da aka kashe a Mali sun zama 50.
Tun 2013 dakarun Faransa ke yaƙi da 'yan binidiga masu iƙirarin kishin Islama a Mali don taimakawa wajen samar da kwanciyar hankali a ƙasar.
Korona a Najeriya: Mutum takwas sun mutu, 576 sun kamu ranar Asabar
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin takwas da suka mutu sakamakon cutar korona sannan 576 sun kamu da cutar a ranar Asabar.
Sabbin alƙaluman da hukumar ta wallafa a shafinta na twitter sun nuna cewa jihar Legas ce ke kan gaba da mutum 277.
Babban birnin kasar, Abuja ne ke biye da Legas da mutum 90, inda jihar Oyo take da 51 sannan Nasarawa ke da 49.
Sauran jihohin su ne: Sokoto (23), Anambra (14), Bauchi (11), Imo (11), Kano (11), Edo (10), Plateau (10), Ogun (9), Osun (5), Jigawa (3), Rivers (2).
Da wannan adadi, jumillar mutum 89,163 ne suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,302 suka mutu sannan aka sallami 74,789 bayan sun warke.
Barka da hantsin Lahadi
Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo yadda duniya ke ciki musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.
Ni ne Umar Mikail zan kasance da ku har zuwa yamma.