Wasu 'yan bindiga sun sace wata uwa mai shayarwa a Jihar Jigawa, inda suka bar jaririnta ɗan wata ɗaya da haihuwa.
Lamarin ya faru ne a garin Gujungu na Ƙaramar Hukumar Taura bayan mutanen ɗauke da makamai sun shiga gidan Basiru Haruna tare da yin awon gaba da matarsa Habashiyya.
Mai magana da yawun 'yan sandan Jigawa, DSP Abdu Jinjiri, ya tabatar da faruwar lamarin, inda ya ce da misalin ƙarfe 2:00 na daren Asabar ya faru.
Ya ce sai bayan kusan awa takwas sannan aka kai musu rahoto, "abin da ya sa ba mu iya bin sahun maharan ba".
"Mun samu rahoto daga wani Alhaji Alasan Audu, mahaifin wadda aka yi garkuwa da ita, cewa an ɗauke 'yarsa Habashiyya da misalin ƙarfe 2:00 na dare kuma mijinta ya gudu cikin daji saboda tsoro har zuwa 8:00 na safe," in ji DSP Jinjiri.
"Bayar da rahoto a ƙurarren lokaci ba ya taimakawa. Ta yaya 'yan sanda za su ceci mutum bayan masu laifin sun tafi da awa takwas? Wajibi ne mutane su riƙa kai wa 'yan sanda rahoto a kan kari."
A jiya Juma'a ma sai da wasu miyagu suka kashe manyan jami'an 'yan sanda biyu a jihar ta Jigawa da kuma raunata wani bayan sun yi musu kwanton-ɓauna.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da kashe wani ɗan sandan yayin da suke yunƙurin sace wata ɗalibar Jami'ar Sule Lamido a Ƙaramar Hukumar Maigatari ranar Litinin.