Burtaniya ta nesanta kanta daga zargin Gowon da wawushe Baitul-malin Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Imam Saleh
An kaddamar da fara rigakafin korona a Turai
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Tarayyar Turai ta fara riga- kafin korona a dukkan nahiyar, a wani mataki da ta kira "Hadin kai don yaki da annoba".
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce allurar rigakafin ta isa dukkan kasashen nahiyar 27 zuwa yanzu.
Tuni dai wasu daga cikin kasashen suka fara yiwa mutane rigakafin, inda suka ce babu bukatar sake jira sai wata rana.
Fiye da mutane Miliyan 14 ne aka tabbatar sun kamu da cutar korona a nahiyar, kana fiye da dubu 300 sun mutu.
Rufewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Imam Saleh
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Brodcast Journaalist
Masu bibiyarmu ta wannan shafi nan muka zo ga karshen kawo muku labaran duniya kai tsaye a yau.
Sai ku kasance da mu idan Allah ya kaimu gobe don ci gaba.
Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya.
An sace wani malamin addinin kirista da matarsa a Kaduna
Asalin hoton, SAMUEL ARUWAN
Yan bindiga a Kaduna, sun sace wani malamin addinin kirista Apostle Emmanuel Egoh Bako tare da matarsa Cindy Bako.
Rahotannin hukumomin tsaro a Najeriya sun ce maharan sun bude wuta kan wani majalisi yayin da ake gudanar da harkokin ibada, a kusa da hanyar Afana zuwa Fadan a karamar hukumar Jema'a, inda daga bisani suka yi nasarar yin awon gaba da malamin da matarsa, da kuma wani mutum guda.
Sanarwar kwamishinan tsaro na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ta ce sojoji sun yi yunkurin bin sahun maharan, sai dai basu yi nasarar samunsu ba.
Ga hotunan daya daga cikin motocin da harsashi ya huda yayin harin.
Asalin hoton, SAMUEL ARUWAN
Sabon nau'in cutar korona na ci gaba da yaduwa a turai
Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da samun yaduwar sabon nauin cutar korona da yafi bazuwa tsakanin jama'a a turai gabanin fara amfani da rigakafi a wasu daga cikin kasashen nahiyar.
Sabon nauin wanda aka yi imanin ya samo asali ne daga Burtaniya, a yanzu ya shiga wasu kasashe da suka hadar da Spaniya, da Sweden, da kuma Suwizalan
Bullar cutar da aka samu a kwanakin baya, ya tilastawa kasashe da dama a sassan duniya hana shiga daga Burtaniya.
Kasar Hungary ce ta zamo kasa ta farko a turai da ta yiwa al'ummarta rigakafin korona.
Gobara ta kashe masu cutar korona a wani asibiti dake Masar
Asalin hoton, Google
Wata gobara da ta tashi a wani asibiti a arewacin Alkahira a ranar Asabar ta kashe marasa lafiya bakwai dake fama da cutar korona, a cewar majiyoyin jami'an tsaro.
Wutar da ta tashi a sashen kulawa na musamman na asibitin da ke gundumar Obour, a wajen birnin Alkahira, ta kuma raunata wasu mutane biyar, in ji majiyar.
Ba a bayyana takamaiman abin da ya haddasa gobarar ba, majiyoyin sun kara da cewa tuni masu gabatar da kara suka fara gudanar da bincike kan lamarin.
An tura jami'an kashe gobara zuwa wurin tare da dakatar da wutar daga yaduwa, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
Burtaniya ta nesanta kanta daga zargin Gowon da wawushe Baitul-malin Najeriya
Asalin hoton, Google
Kasar Burtaniya ta nesanta kanta daga zargin wawushe baitul-malin Najeriya da wani ɗan majalisar ta, Tom Tugendhat ya yiwa tsohon Shugaban Najeriyar Yakubu Gowon.
Matakin ya biyo bayan koken da wata ƙungiya, Igbo for a Progressive Nigeria (IPAN) ta gabatar ga majalisar dokokin Burtaniyan, suna neman cikakken bayani game da zargin.
A yayin wata muhawara a ɗakin taro na Westminster a ranar 23 ga watan Nuwamba ne dai Tugendhat ya zargi Gowon da wawure rabin kuɗaɗen da aka tara a Babban Bankin Najeriya yayin da yake kan mulki.
Jaridar The Nations ta rawaito wata jami'a a ofishin kula da ƙasashe renon Burtaniya Angela, ta bayyana cewa Tom Tugendhat ya yi wannan kalami ne a kashin kansa, ba da yawun Burtaniya ba.
Aƙalla mutum 20 sun mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa a Bahar Rum
Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla baƙin haure 20 ne suka mutu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tekun Bahar Rum, yankin gaɓar ruwan Tunisia, in ji jami’ai.
Jiragen ruwan masu tsaron gabar ruwan Tunusiya sun tsamo gawarwakin mutanen a gaɓar garin Sfax da ke tsakiyar kasar a ranar Alhamis.
Ana ci gaba da neman karin aƙalla mutane 20 waɗanda har yanzu ba a gansu ba.
An kuɓutar da mutane biyar da suka tsira, a jirgin ruwan wanda aka ƙiyasta na ɗauke da kimanin mutane 45, kuma ya taso ne daga yankin Kudu da hamadar Afirka, yana kokarin isa Italiya.
Jirgin ya yi lodi da yawa kuma a cikin mummunan yanayi, sannan ya gamu da iska mai karfi wanda watakila ita ta taimaka wajen nitsewarsa, in ji kakakin rundunar tsaron kasar Ali Ayari, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AP.
'Yan bindiga sun sace mai jego a Jihar Jigawa
Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan bindiga sun sace wata uwa mai shayarwa a Jihar Jigawa, inda suka bar jaririnta ɗan wata ɗaya da haihuwa.
Lamarin ya faru ne a garin Gujungu na Ƙaramar Hukumar Taura bayan mutanen ɗauke da makamai sun shiga gidan Basiru Haruna tare da yin awon gaba da matarsa Habashiyya.
Mai magana da yawun 'yan sandan Jigawa, DSP Abdu Jinjiri, ya tabatar da faruwar lamarin, inda ya ce da misalin ƙarfe 2:00 na daren Asabar ya faru.
Ya ce sai bayan kusan awa takwas sannan aka kai musu rahoto, "abin da ya sa ba mu iya bin sahun maharan ba".
"Mun samu rahoto daga wani Alhaji Alasan Audu, mahaifin wadda aka yi garkuwa da ita, cewa an ɗauke 'yarsa Habashiyya da misalin ƙarfe 2:00 na dare kuma mijinta ya gudu cikin daji saboda tsoro har zuwa 8:00 na safe," in ji DSP Jinjiri.
"Bayar da rahoto a ƙurarren lokaci ba ya taimakawa. Ta yaya 'yan sanda za su ceci mutum bayan masu laifin sun tafi da awa takwas? Wajibi ne mutane su riƙa kai wa 'yan sanda rahoto a kan kari."
A jiya Juma'a ma sai da wasu miyagu suka kashe manyan jami'an 'yan sanda biyu a jihar ta Jigawa da kuma raunata wani bayan sun yi musu kwanton-ɓauna.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da kashe wani ɗan sandan yayin da suke yunƙurin sace wata ɗalibar Jami'ar Sule Lamido a Ƙaramar Hukumar Maigatari ranar Litinin.
Isra'ila ta yi ruwan wuta a Gaza
Asalin hoton, AFP
Israila ta kai hare-hare a wurare daban-daban a birnin Gaza bayan an harba rokoki zuwa cikin ƙasarta daga can.
Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta kai harin kan wata masana'antar ƙera rokoki da sansanin soji da kuma wasu gine-ginen ƙarƙashin ƙasa.
A jiya Juma'a ne na'urar cafke makami mai linzame ta Isra'ila mai suna Iron Dome ta kama roka biyu da aka harba daga zirin na gaza.
Sojojin ƙasar sun ce ƙungiyar Hamas ce suka ɗora wa alhakin duk wani harin da aka kai mata daga Gaza.
Sabon nau'in cutar korona na Birtaniya ya ɓulla Faransa
Faransa ta samu mutum na farko da ya harbu da sabon nau'in cutar korona mai mafi saurin bazuwa da ya ɓulla a kwanannan a Burtaniya.
Ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce wanda aka samu da ita ɗan Faransa ne wanda ya koma daga birnin Landan a makon da ya wuce.
Hukumomi sun ce ya killace kansa a gidansa da ke garin Tours.
Wakiliyar BBC ta ce: "An fara gano sabon nau'in cutar ne a kudu masu gabashin Ingila kuma ɓullarsa ya sa ƙasashe fiye da 40 sun haramta wa mutanen da suka fito daga Burtaniya shiga ƙasashensu."
Kafin Faransa, an samu ɓullar sabon nau'in cutar a Denmark da Australia da kuma Netherlands.
Saudiyya ta rufe ƙasarta ruf na tsawon mako guda tare da tilasta wa waɗanda suka je ko suka wuce ta ƙasashen da sabon nau'in ya ɓulla yin gwaji duk bayan kwana biyar.
Dole ne sabbin ma'aurata su nemi izini daga gwamnati kafin taron biki a Legas
Asalin hoton, @jidesanwoolu
Gwamnatin Jihar Legas ta wajabta wa sabbin ma'aurata da su nemi izini daga gwamnatin jihar kafin su shirya shagalin bikin da zai tara mutum 300.
Sabon matakin na ƙunshe ne a cikin wani bayani da gwamnatin ta fitar jiya Juma'a mai taken "Stay At Home" wato ku zauna a gida.
"Bikin aure da kuma taron jama'a, kar su wuce mutum 300 bayan an samu izini daga hukumar kiyaye lafiya ta Jihar Legas," a cewar wani ɓangare na bayanin.
Shugaban hukumar ta Lagos State Safety Commission, Lanre Mojola, ya faɗa wa jaridar Punch cewa neman izinin kyauta ne, inda sabbin ma'auratan za su je shafin hukumar na intanet domin yin rajista.
Ya ƙara da cewa dakarun kiyaye lafiya za su je wuraren taron domin tabbatar da cewa an bi ƙa'idojin kare kai daga kamuwa da cutar korona.
Boko Haram ta kashe mutum 11 a Jihar Borno
Asalin hoton, Boko Haram
Akalla mutum 11 ne suka mutu cikin wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai kan wani kauyen da galibin mazaunansa Kiristoci ne a Jihar Bornon Najeriya.
Kazalika, mayaƙan sun yi awon gaba da wani limamin Kirista da wasu mazauna kauyen Pemi a harin wanda suka kai ranar Alhamis, inda suka ƙona gine-gine da wata coci.
Ganau sun ce maharan sun shiga garin na jihar Borno ne cikin motoci da babura suna harbin kan mai tsautsayi yayin da mutane ke shirye-shiryen shagulgulan Kirsimati.
Wasu mazauna garin sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukannsu.
"'Yan ta'addan sun kashe mutum bakwai, suka ƙona gida 10 sannan suka wawashe kayan abincin da ake shirin raba wa mutane domin bikin Kirsimeti," kamar yadda wani ganau ya shaida wa AFP.
"Daga baya aka gano wasu gawarwakin guda huɗu a dajin da ke kusa da garin," a cewar wani dattijo a yankin.
Cutar korona ta kashe likita 20 a mako ɗaya a Najeriya - NMA
Asalin hoton, Getty Images
Likitoci aƙalla 20 ne suka mutu sakamakon annobar cutar korona a faɗin Najeriya cikin mako ɗaya da ya gabata, a cewar ƙungiyar likitoci ta ƙasa Nigerian Medical Association (NMA) reshen birnin Abuja.
Shugaban reshen ƙungiyar, Dr. Enema Amodu, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma'a a Abuja.
"A cikin mako ɗaya da ya gabata, mun yi rashin farfesoshi da ƙwararru da likitoci manya da ƙanana da kuma sauran manyan masana kiwon lafiya," in ji shi.
"Adadin abokan aikinmu da suka rasu ƙaruwa yake kullum. Yanzu haka da nake magana da ku, wani aboki ya kira ni daga cibiyar killace mutane kuma da alama yana jin jiki.
"Idan na faɗa muku adadin a yanzu zai iya sauyawa nan da dare. Amma ina faɗa muku cewa mun yi rashin likitoci aƙalla 20 a cikin mako ɗaya da ya wuce."
Ya ƙara da cewa hakan na tabbatar da cewa "wannan ƙwayar cuta na nan tare da mu".
Ya ce duk da irin barazanar da likitoci ke fuskanta har yanzu alawus ɗin da ake ba su na haɗari naira 50,000 ne a wata.
Tarwatsewar mota ta raba ɗan sanda da ƙasa, ta raunata mutum uku
Wata motar yawon shaƙatawa ta tarwatse a birnin Nashville na Jihar Tennessee da ke Amurka a safiyar ranar Kirsimeti.
Fashewar ta jawo raunata mutum uku tare da lalata harkokin sadarwa a jihar baki ɗaya sakamakon ƙarfinta.
Kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa da alama an samu wasu sassan jikin mutum daga baya.
'Yan sanda sun ce suna tunanin an dasa abin fashewar ne da gangan.
'Yan sandan da aka kira bayan an ji harbe-harbe da misalin ƙarfe 6:00 na safe (1:00 na dare agogon Najeriya) sun ga wata mota na gargaɗin mutane da su bar wurin.
'Yan mintuna bayan haka ne kuma motar ta tarwatse. Ƙarfin fashewar ya raba wani ɗan sanda da ƙasa, a cewar hukumomi.
'Yan sanda sun saki hoton motar wadda suka kira motar shaƙtawa a loƙacin da take isa wurin da abin ya faru.
Korona a Najeriya: Mutum huɗu sun mutu, 712 sun kamu ranar Kirsimeti
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 712 da suka kamu da cutar korona a ranar Juma'a.
Sabbin alƙaluman da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet sun nuna cewa ƙarin wasu mutum huɗu sun mutu.
An samu sabbin mutanen da suka kamun daga jiha 20 na ƙasar da suka haɗa da Legas (388) da Abuja (77) da Kwara (39) da Katsina (35) da Bauchi (33).
Sauran jihohin su ne: Filato (22), Ogun (18), Akwa Ibom (16), Delta (13), Kaduna (12), Osun (12), Yobe (11), Sokoto (10), Kebbi (8), Enugu (6), Edo (5), Ondo (3), Niger (2), Kano (1), and Oyo (1).
Da wannan adadi, jumillar mutum 82747 suka harbu da cutar a Najeriya, yayin da 1,246 suka mutu sannan aka sallami 70,239 bayan sun warke.
Barkanmu da hantsin Asabar
Barkanmu da hantsin Asabar tare da fatan ana shan hutun Kirsimeti lafiya ƙalau.
Umar Mikail ne zai kawo muku rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar.