Shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai EU 27 sun yi maraba da cimma yarjejeniyar cinikayyar da aka yi tsakaninsu da Birtaniya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce irin haɗin kai da kuma dagewar da Turai ta nuna yayin tattaunawar da aka yi kan yarjejeniyar, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Ya saka a shafinsa na Tuwita cewar yanzu Tarayyar Turai za ta iya tsara yadda gobenta za ta kasance tana mai cikakken ƴanci da kuma ƙarfi.
Takwararsa ta Jamus Angeka Merkel ta bayyana yarjejeniyar a zaman wani kyakkyawan sakamako.
Yayin da shi kuwa Ministan Harkokin Wajen Denmark ya ce babu wani abu da Birtaniya da kuma EU za su iya bai wa junansu a matsayin goron Kirsimeti da ya kai cimma wannan yarjejeniyar.
Masu fashin baƙi suna cewa da a ce Birtaniya ta fice ba tare da cimma wannan yarjejeniya ba da tabbas za ta afka cikin ruɗani ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewa.
Sai dai ga alama tana ƙasa tana dabo don sai dukkan ɓangarorin biyun sun jefa ƙuri'ar amincewa da yarjejeniyar a Majalisar Dokoki kafin ta fara aiki a watan Janairu.
A Birtaniya ana sa ran ƴan majalisar su kaɗa ƙuri'ar amincewar cikin sauƙi a makon gobe.
Babbar jam'iyyar adawa ta Labour ta ce za ta goyi bayan yarjejeniyar duk da cewa tana da ƙorafe-ƙorafe game da ita.
A ɓangaren Tarayyar Turai kuwa Minsitan Harkokin Wajen Jamus ya ce ƙasarsa za ta taimaka wajen amincewa da yarjejeniyar cikin sauri.
A halin yanzu Jamus ce ke riƙe da shugabancin EU.
Ya zama dole majalisar dokokin EU ta amince, amma ana iya fara aiki da dokar na wucin gadi gabanin ƴan majalisa su jefa ƙuri'a a kanta.