Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Allah ƙara wa Ganduje lafiya da tsawon kwana ‒ Buhari

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Masu biibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Asabar idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin.

    • Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta'aziyya bisa rasuwar mahaifinsa
    • Korona ta yi ajalin jagoran ƴan adawan Mali, Soumaila Cisse
    • An gudanar da jana'izar mahaifin Kwankwaso a Kano
    • Ƙura 'ta lafa' a garin Garkiɗa da 'ƴan Boko Haram' suka kai hari ranar Alhamis
    • Sabon nau'in cutar korona ya ɓulla Lebanon
    • Jirgin ɗaukar kaya ya ci karo da bam a cikin Bahar Maliya

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai

  2. An yi wa Yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman allurar riga-kafin korona

    An yi wa yarima mai jiran gado kuma ministan tsaro na Saudiyya, Muhammad Bin Salman allurar riga-kafin korona a ranar Juma'a.

    Jaridar Saudi Gazette ta ƙasar ta ruwaito ministan lafiya na ƙasar Dakta Tawfiq Al-Rabiah inda yake gode wa yariman kan ƙoƙarin da yake yi wurin ganin cewa ƴan ƙasar sun samu riga-kafin.

    A ranar 17 ga watan Disamba ne aka ƙaddamar da riga-kafin a Saudiyya inda aka fara ta kan ministan lafiya na ƙasar

  3. Ɓarayi 5 sun haɗu da ajalinsu a hannun wasu matasa a Kaduna, an ƙona biyu ƙurmus

    Wasu fusatattun matasa a Kaduna sun kashe ɓarayi biyar a Ƙananan Hukumomin Sanga da Lere, kamar yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar.

    Tun da farko dai, biyu daga cikin ɓarayin sun kai wa wani ɗan kasuwa hari inda suka ƙwace masa kuɗaɗe a Fadan Karshi da ke Sanga.

    Sai dai ko da jami'an tsaro suka isa inda lamarin ya faru sai suka tarar da wasu fusatattun matasa sun ƙona ɓarayin ƙurmus.

    Kwamishinan ya ƙara da cewa a Ƙaramar Hukumar ta Sanga dai, wasu 'yan bindiga sun ɓude wa motoci wuta kan hanyar Aboro zuwa Kafanchan.

    A yayin da suke harbin, sai harsashi ya sami wani mai suna Richard Sabo wanda ya kaɗe ɗaya daga cikin ɓarayin da mota bayan motar ta ƙwace masa.

    A Ƙaramar Hukumar Lere kuma wasu matasa ne da suka shahara wurin satar dabbobi su ma suka haɗu da ajalinsu a wurin fusatattun matasa.

    Kwamishinan ya bayyana cewa an bi ɓarayin su uku inda aka ci ƙarfinsu a ƙauyen Domawa, inda a nan ne matasan suka kashe su.

    A cewar kwamishinan, Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya ja hankalin matasan jihar da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

  4. Adadin waɗanda aka kashe a harin Ethiopia ya kai 207

    Adadin mutanen da aka kashe a harin da aka kai a jihar Benishangul-Gumuz ta Ethiopia ya kai 207, kamar yadda wani jami'in gwamnati ya shaida wa BBC.

    Kassahun Addisu, wanda shi ne mai magana da yawun gundumar Bullen, wanda nan ne lamarin ya faru, ya shaida cewa an yi jana'izar mutum 171 kuma tuni aka binne su.

    A baya dai, mai magana da yawun jihar ya shaida wa BBC cewa zai yi wuya a iya gane adadin mutanen da suka mutu sakamakon waɗanda aka kashe na da ɗumbin yawa.

    Wani rahoto da ke da alaƙa da hukumar kare haƙƙin bil'adama ta ƙasar ta fitar ya nuna cewa waɗanda aka kashe akasari ƴan ƙabilar Oromo ne da Agaw da Amhara - kuma an kai musu hari ne saboda ƙabilanci .

    Kassahun ya shaida cewa mutane da dama da ke yankin na barin gidajen su sakamakon tsoron wani sabon harin.

  5. Jirgin ɗaukar kaya ya ci karo da bam a cikin Bahar Maliya

    Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa wani jirgin ruwa na ɗaukar kaya da ke tafiya a cikin Bahar Maliya ya ci karo da wani bam da ƴan tawayen Houthi suka dasa a cikin ruwan.

    Gidan talabijin na Saudiyya ya ruwaito cewa ɓarnar da bam ɗin ya yi wa jirgin ruwan ba ta da yawa kuma babu wanda ya mutu.

    A kwanakin baya ne dai wasu jiragen ruwa da ke ajiye a tashar ruwa ta Saudiyya tashin bam ya rutsa da su sakamakon wasu ababen fashewa da aka ajiye a wasu jiragen ruwan.

    Ƴan tawayen Houthi dai na yaƙar haɗakar dakarun da Saudiyya ke jagoranta da ke goyon bayan gwamnatin Yemen a yaƙin basasa na ƙasar.

  6. Coronavirus: 'Yan wasan Man City Jesus da Walker sun kamu

    'Yan kwallon Manchester City, Gabriel Jesus da kuma Kyle Walker sun kamu da cutar coronavirus.

    'Yan wasan biyu tare da wasu ma'aikatan kulob ɗin su biyu za su killace kansu kamar yadda dokokin gasar Firemiya da na gwamnati suka gindaya.

    Hakan na nufin 'yan wasan biyu ba za su buga wa City wasaninta na gaba wato da Newcastle United a ranar 26 ga watan Disamba, da kuma karawa da Everton sai kuma fafatawa da Chelsea a ranar 3 ga watan Janairu.

    Ana sa ran Sergio Aguero wanda ya warke daga rauni zai maye gurbin Jesus a cikin tawagar.

  7. Allah ƙara wa Ganduje lafiya da tsawon kwana ‒ Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje murnar cika shekara 71 da haihuwa.

    A wani saƙo da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan watsa labarai, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya roƙi Allah (SWT) ya ƙara wa gwamnan lafiya da tsawon kwana domin ya ci gaba da yi wa mutanen Kano da Najeriya aiki.

  8. Sabon nau'in cutar korona ya ɓulla Lebanon

    Lebanon ta sanar da ɓullar sabon nau'in cutar korona wanda aka samu irinsa a Birtaniya.

    Ministan lafiya na ƙasar, Hamad Hassan ya bayyana cewa an samu cutar ne daga wasu matafiya waɗanda suka isa ƙasar daga Birtaniya kwanaki huɗu da suka gabata.

    Masana sun bayyana sabon nau'in cutar da cewa ya fi saurin bazuwa da kusan kashi 70 cikin 100 fiye da na baya.

    A yanzu dai ƙasar ta Lebanon ta sanar da cewa sama da mutum 1,300 cutar ta kashe.

  9. Ƙura 'ta lafa' a garin Garkiɗa da 'ƴan Boko Haram' suka kai hari ranar Alhamis

    Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa a Najeriya ta ce ƙura ta lafa a garin Garkiɗa, bayan wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne suka far wa garin mai makwaftaka da jihar Borno.

    Lamarin dai ya afku ne jiya da marece inda ‘yan bindigar suka kutsa garin na Garkiɗa cikin motoci ƙirar Hilux guda bakwai ɗauke da makamai inda suka riƙa harbe-harbe.

    Bayanai na cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, sai dai kawo yanzu jami’an ƴan sanda ba su tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.

    Wasu da BBC ta zanta da su ta waya sun shaida cewa, daman tun farkon makon nan suka samu labarin cewa za a kawo musu hari garin, lamarin da yasa wasu suka fara ficewa.

    Wani wanda ya rasa ‘yan uwansa biyu, ya shaida cewa iyalansa a kan dutse suka kwana saboda fargaba, sannan ya ce maharan sun tafi da mutum biyu.

    Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Yayan Guroje, ya tabbatar wa BBC da afkuwar lamarin, inda ya ce jami’ansu na can na gudanar da bincike don tantance abubuwan da suka faru.

  10. Bidiyon yadda ake bikin Kirisimeti a Kano

  11. An gudanar da jana'izar mahaifin Kwankwaso a Kano

    An gudanar da jana'izar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, wanda mahaifi ne ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma fitaccen ɗan siyasa Rabi'u Musa Kwankwaso.

    An gudanar da jana'izar ne tare da binne sa a harabar masallacin gidan Rabiu Kwankwaso da ke Miller Road a Bompai da ke Kano.

  12. Mutum 15 sun mutu kan iyakar Afrika Ta Kudu da Zimbabwe

    Aƙalla mutum 15 suka mutu a ƴan kwanakin nan a iyakar Afrika Ta Kudu da Zimbabwe ta ɓangaren garin Beitbridge, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Mutanen dai sun mutu a dogon layin da ake yi wanda bai saurin tafiya sakamakon tantancewar da ake yi saboda cutar korona.

    Ma'ikatar lafiya da kuma na harkokin cikin gida na Afrika Ta Kudu ba ta su ce komai ba kan wannan lamarin, sai dai kafafen yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa cikin abubuwan da suka jawo mace-macen har da gajiya da rashin lafiya da kuma rashin kayan aiki na kula da marasa lafiya kan iyakokin ƙasashen biyu.

  13. Indiya ta sanar da tallafin dala biliyan 2.4 ga manoman ƙasar

    Firaiministan Indiya, Narendra Modi, ya sanar da da tallafin kusa dala biliyan 2.4 ga manoman ƙasar a daidai lokacin da ƙungiyoyin manoman ke zanga-zanga inda suke buƙatar gwamnatin ƙasar ta janye kudirinta na sabbin tsare-tsare ga aikin gona na ƙasar.

    Mista Modi ya bayyana cewa ƴan adawar ƙasar ne ke hure wa manoman kunne kan sabuwar dokar ƙasar da aka amince da ita a watan Satumba.

    Dubban manoma ne dai ke zanga-zanga a wajen birnin Delhi inda suke nuna rashin goyon bayansu ga sabuwar dokar da aka yi.

    Ƙungiyoyin manoman sun ce wannan sabuwar dokar za ta sa gwamnatin ƙasar ta daina sayan alkama da shinkafa daga manoman akan farashi mai inganci.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta musanta hakan inda ta ce wannan sabon tsarin zai jawo masu zuba jari.

  14. Korona ta yi ajalin jagoran ƴan adawan Mali, Soumaila Cisse

    Jagoran ƴan adawa a ƙasar Mali, Soumaila Cisse ya mutu a yau Juma'a yana da shekara 71 sakamakon cutar korona.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya ruwaito ai magana da yawun tsohon ministan kuɗi na ƙasar inda yake tabbatar da mutuwarsa.

    Mista Cisse ya rasu ne a ƙasar Faransa, inda ya je asibiti domin maganin cutar korona.

    'Yan bindiga sun yi garkuwa da Cisse tun a watan Maris a lokacin da ya je yakin neman zaɓen 'yan majalisa a yankin Timbuktu, amma an sake shi a watan Maris tare da ma'aikaciyar agajin nan ta Faransa, Sophie Petronin da wasu ƴan Italiya biyu.

    Mista Cisse ne ya zo na biyu a zaɓen ƙasar na 2013 da 2018 wanɗanda duka tsohon shugaban ƙasar, Ibrahim Boubacar Keita ya lashe.

    Kafin rasuwar Cisse, jama'ar ƙasar sun saka rai cewa zai kasance daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙasar da za su fafata a 2022.

  15. Ganduje ya yi wa Kwankwaso ta'aziyya bisa rasuwar mahaifinsa

    Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rashin mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

    Mahaifin Sanata Kwankwaso, wanda shi ne dagacin Madobi, ya rasu ne a daren Alhamis wayewar yana da shekara 93 a duniya.

    A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar, ya ce Gwamna Ganduje ya kaɗu da samun saƙon mutuwar, sannan za a dinga tuna marigayin da irin hikimarsa da dattako a matsayin na jagoran al'umma.

    "A madadina da gwamnatin jihar Kano, ina yi wa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Masarautar Ƙaraye ta'aziyyar wannan babban rashi.

    "Haƙiƙa marigayin ya bar mana darussan koyo da suka haɗa da gaskiya da adalci da tsoron Allah a wannan jiha tamu," in ji sanarwar.

    Duk da cewa Gwamnan Ganduje da Sanata Kwankwaso ba sa ga maciji da juna saboda bambancin siyasa, wanda ya samo asali a lokacin rasuwar mahaifiyar Ganduje da Kwankwaso ya je ta'aziyya, akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Gandujen da mahaifin Kwankwason.

  16. Ana ci gaba da yi wa ƴan Saudiyya allurar riga-kafin cutar korona

    Ana ci gaba da gangamin wayar da kai da yi wa mutane allurar riga-kafin annobar cutar korona a birnin Jeddah na Saudiyya, bayan da ƙasar ta karɓi sawun farko na alluran na kamfanin Pfizer-BioNTech a ranar Laraba a birnin Dammam.

    An tsara cewa za a fara yin alluran ne a ranar Lahadi a faɗin ƙasar.

    An fara gangamin wayar da kan a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah, sannan wani dattijo mai shekara 60 ɗan ƙasar ta Saudiyya ne mutum na farko da aka yi wa allurar.Jami'an lafiya na ma'aikatar lafiya ne suke yi wa mutanen da suka riga suka yi rijista allurar.

    A makon da ya gabata ne ƙasar ta fara gagarumin wayar da kai kan muhimmancin yin riga-kafin kariya daga cutar korona, inda Ministan Lafiya Dr. Tawfiq Al-Rabiah ya zama mutum na farko da aka yi wa.

  17. Hotunan Mo Salah yana taya masoyansa murnar bikin Kirsimeti

    FItaccen ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya wallafa waɗannan hotunan a shafinsa na Instagram yana taya masoyansa barka da bikin Kirsimeti.

  18. Mutum 1,041 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya ranar Alhamis

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,041 da suka kamu da cutar korona a ranar Alhamis.

    Sai hukumar ba ta bayar da bayanin samun mutuwa ba sakamakon annobar a ranar Alhamis ɗin.

    Jihar Legas ce mai kaso mafi yawa na 316, yayin da FCT ke biye da ita da mutun 210.

    Koronar ta kuma kama mutum 83 a Kaduna, sai jihar Filato mai mutum 70 inda Gombe mai mutum 56 ke biye mata duk a bayanan hukumar na ranar Alhamis.

    A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bullarta zuwa yanzu sun kai 81,963, yayin da 69,651 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,242.

  19. Wasu hotunan bikin Kirsimeti a wasu sassan duniya

  20. Abu biyar da suka kamata ku sani game da bikin Kirsimeti

    Ranar Kirsimeti, rana ce da ake murna saboda zagayowar ranar haihuwar Yesu, kamar yadda yake a imanin duk wani mai bin addinin Kiristanci.

    Duk da cewa an samu saɓani a kan cewa ranar 25 ga watan Disamba aka haife shi, wasu na cewa ba a wannan rana ba ce, amma mafiya rinjaye sun tafi cewa a wannan rana ce aka haifi Yesu al-Masihu.

    Ku karanta cikakken labarin a nan.