Buhari ya sake tsawaita wa'adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da korona

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Laraba idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa, ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Jiragen ruwan Amurka sun isa gaɓar tekun Somalia

    Wasu jiragen ruwa na sojin Amurka sun isa gaɓar tekun Somalia domin kwashe dakarun Amurkar kusan 700, waɗanda aka kai can domin yaƙi da 'yan kungiyar al-Shabaab.

    A farkon wannan watan na Disamba, Shugaban Amurkar mai barin-gado, Donald Trump, ya bayar da umarni, dukkanin sojojin Amurkar su bar Somalia, matakin da ya saɓa da ra'ayin tsohon sakataren tsaronsa, da ya cire a watan da ya wuce, Mark Esper.

    Hukumar sojin Amurkar ta ce za a kai dakarun ne wasu sassan Afrika Ta Gabas, amma ba ta faɗi ko waɗanne ƙasashe ba ne.

    Ganin yadda ƙungiyar ta al-Shabaab ke yawan kai hare-hare, da yawa daga cikin 'yan Somalia na nuna shakku da tababa a kan manufar aikin sojin na Amurka a ƙasarsu.

  3. LABARAN WASANNI - NA YAMMA 22/12/2020

    Bayanan sautiLatsa lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
  4. Jami'an farin kaya sun kama wani fitaccen lauya a Uganda

    Wasu jami'an farin kaya a Kampala babban birnin Uganda, sun kama wani fitaccen lauya mai kare haƙƙin ɗan adam, da ya yi suna wajen sukar lamirin gwamnati.

    'Yan sandan sun ce Nicholas Opiyo - wanda ke jagorantar ƙungiyar Chapter Four a Uganda - an kama shi ne kan zargin almubazaranci.

    Ƙungiyarsa ta bayyana kama jagoranta da aka yi a matsayin abin da aka yi ba bisa ƙa'ida ba, ta kuma nemi a sake shi cikin gaggawa.

    A 'yan kwanakin nan ne dai Mista Opiyo ya caccaki gwamnatin ƙasar kan yunƙurin da ta yi na neman kamfanin Google ya sauke manyan tashoshin 'yan adawar a shafin YouTube.

    Kama Mista Opiyo na zuwa ne wata guda kafin zaɓe a ƙasar.

  5. Ofishin bayar da biza na China da ke Landan ya dakatar da ayyukansa saboda korona

    .

    Asalin hoton, Reuters

    China ta dakatar da ayyukan samar da takardar visa a birnin London.

    A wata sanarwa da ofishin jakadancinta ya fitar, ba ta bayyana ko tsawon wane lokaci ne dakatarwar za ta kawo karshe ba.

    “Saboda shawarwari game da daukar matakan kariya kan annobar cutar korona, ofishin samar da takardun visa na kasar China a birnin London zai dakatar da ayyukansa daga ranar 22 ga watan Disambar shekara ta 2020 har sai yadda hali ya yi,’’ in ji sanarwar.

    Sanarwar na zuwa ne bayan bayyana sabuwar barkewar annobar ta korona a Birtaniya.

    Kawo yanzu dai kasashe fiye da 50 ne suka dakatar da harkokin sufuri daga Birtaniyar.

    A watan da ya gabata, ofishin huldar jakadancin kasar China ya sanar da dakatar da shiga kasar ta China na wucin gadi ga wadanda ba ‘yan kasar ba da ke zaune a Birtaniya da ke dauke da takardar biza ko takardar izinin zama kasar ta China.

  6. Jirgin Isra'ila ya sauka Morocco a karon farko a tarihi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images/EPA

    Tawagar haɗin gwiwa tsakanin Isra'ila da Amurka ta isa Morocco cikin jirgin sama na farko da a tarihi ya tashi daga Isra'ila ya sauka Morocco.

    Wannan lamari mai cike da tarihi ya tabbata ne bayan shiga tsakani da Amurka ta yi ta ƙulla yarjejeniyar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

    Tawagar da ta isa Moroccon za ta saka hannu kan wasu yarjejeniyoyi da suka haɗa da na jigila da wasu yarjejeniyoyi da za su taimaka wa ƙasashen biyu wajen ƙara danƙon zumunci.

    A watannin da suka gabata, an samu sasanci matuƙa tsakanin wasu ƙasshen Larabawa da kuma Isra'ila.

    Sai dai Falasɗinawa ba su maraba da wannan sulhu sakamakon sun so a ce ba a yi wannan sulhun ba sai an sasanta tsakaninsu da Isra'ila.

  7. WHO za ta yi taro na musamman kan sabon nau'in korona

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, za ta gudanar da wani taro na ƙasashen da ke cikinta, domin tattauna dabarun dakile sabon nau'in kwayar cutar Korona da ya bayyana a Birtaniya.

    Ba a dai sanya ranar da za a gudanar da wannan taro ba tukunna.

    Daraktan hukumar a nahiyar Turai Hans Kluge, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Twitter inda yake cewa matakan kariyar da ake ƙara ɗauka na da matukar muhimmanci, har zuwa lokacin da WHO ɗin za ta samu bayanan da suka kamata.

    Ya ce yana da muhimmanci kuma a taƙaita tafiye- tafiye domin daƙile cutar, amma ya ce kamata ya yi manyan kantinan da ke samar da kayayyaki su kasance a buɗe.

  8. Labarai da dumi-dumi, Buhari ya sake tsawaita wa'adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da korona

    .

    Asalin hoton, Nigerian Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake tsawaita wa'adin kwamitin da ya kafa na yaƙi da annobar korona zuwa ƙarshen Maris ɗin 2021

    A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba zai yiwu ci gaban da aka samu na watanni tara da suka gabata ya tafi haka nan ba.

    Shugaban ya ce "na tsaya na yi nazari kan lamarin kuma na aminta da cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa wajen daƙile yaɗuwar wannan cutar ta korona.

    Shugaban ya kuma yi kira ga masu sarautun gargajiya da kuma malamai da su ba kwamitinsa haɗin kai wurin wayar da kan al'umma kan cutar.

    A jiya ne dai kwamitin shugaban ƙasar da ke yaƙi da korona ya sake bayar da umarni ga ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa da su zauna a gida har nan da makonni biyar.

    Haka kuma kwamitin ya sanar da rufe duka makarantu da kuma wuraren motsa jiki.

    Kwamitin kuma ya saka takunkumi kan taruka irin na addini inda kwamitin ya ce ko wane wuri kada ya ɗauki sama da kashi 50 cikin 100 na mutanen da yake ɗauka a baya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. MDD na nuna damuwa kan fararen hulan da ke yankin Tigray

    .

    Asalin hoton, AFP

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana ƙara shiga cikin damuwa game da halin ƙuncin da fararen hula na yankin Tigray a ƙasar Ethiopia suke ciki, don haka take ƙara yin kira ga gwamnati da ta ba da damar a shiga domin gudanar da cikakken bincike kan zargin aikata laifukkan yaki.

    Shugabar hukumar kare haƙƙin bil'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Michelle Bachelet, ta ce wasu tawagogin ayyukan jin-Ƙai biyu sun samu sukunin shiga yankin jiya Litinin.

    Sai dai ta ce sakamakon yadda aka taƙaita ayyukansu, sun gaza gudanar da bincike kan zargin hare-haren da aka kai da bindigogin igwa kan wuraren zaman jama'a, da kisa ba tare da gurfanar da su gaban shari'a ba, da kuma kwasar ganima.

  10. Akwai yiwuwar ASUU ta janye yajin aiki a yau Talata

    Ma'aiktar kwadagon Najeriya

    Asalin hoton, @LabourMinNG

    Daliban jami'o'i a Najeriya ka iya sanin makomarsu a yau Talata yayin da kungiyar ASUU ta malaman jami'a ke tattaunawa da tawagar ma'aikatar kwadago dom kawo karshen yajin aiki.

    Ministan Kwadago Chris Ngige ya ce tattaunawar tasu ta kai kashi 98 cikin 100 domin kawo karshen yajin aikin da malaman suka shafe fiye da wata takwas suna yi.

    Mai magana da yawun ministan kwadagon, Charles Akpa, ya ce bangarorin biyu za su shaga tattaunawar a yammacin yau, wanda shi ne irinsa karo na takwas.

    A zaman da suka yi a baya, gwamnati ta amince ta biya malaman alawus na naira biliyan 40 da kuma biliyan 30 na farfado da kayayyakin karatun jami'o'in.

    Babban abin da ke jawo tsaiko a tattaunawar shi ne maganar albashin malaman da gwamnati ta ki biya na tsawon lokacin da suke yajin aikin, wanda suka ce sai an biya su sannan za su ci gaba da aiki.

    Sai dai gwamnati ta bukaci su ci gaba da aikin kafin a biya su albashin.

  11. 'Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar guda bakwai

    Sojojin Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla sojojin kasa bakwai na Jamhuriyar Nijr ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai musu.

    Maharan wadanda ba a san ko su wane ne ba, sun yi w sojojin kwanton-bauna ne a garin Ouallam da ke Jihar Tillabery.

    Kazalika, 'yan bindigar sun kona mota uku ta jami'an tsaron bayan harin.

    Ya zuwa lokacin hda wannan rahoto, babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

    Baya ga mayakan Boko Haram da ISWAP da ke kai hare-hare a Nijar, kasar ta dade tana fama da 'yan tawaye, wadanda suka kashe sojoji kusan 70 a wani hari a shekarar da ta gabata.

  12. Namadi Sambo zai jagoranci tawagar ECOWAS a zaben Nijar

    Namadi Sambo

    Asalin hoton, @GovKaduna

    Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS za ta tura tawagar wakilai 90 domin sa ido a zabe nshugaban kasar Nijar da za a yi ranar Lahadi mai zuwa.

    Mambobin tawagar karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Mohammed Namadi Sambo, sun fito ne daga kasashe mambobin kungiyar guda 16.

    Kafin su tafi Nijar, Shugaban ECOWAS, Mr. Jean-Claude Kassi Brou, ya jagoranci wata tawagar kwararru domin tattaunawa game da zaben a Yamai, babban birnin kasar daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamba.

    A ranar Lahadi 27 ga wannan watan ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Nijar bayan cikar wa'adi na biyu na Shugaba Mahamadou Issoufou.

  13. Buhari zai gana da kwamitin yaki da cutar korona anjima

    Buhari

    Asalin hoton, @NGRPresident

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da kwamitinsa mai yaki da annobar cutar korona anjima a yau Talata, a cewar fadar shugaban.

    A jiya Litinin ne kwamitin karkashin jagorancin Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya, ya sake bayar da umarnin wasu sabbin matakai na yaki da cutar sakamakon yaduwarta a karo na biyu.

    Duk da cewa babu tabbacin abin da za su tattauna, kwamitin zai gabatar wa da Buhari shawarwari wadanda ka iya kai wa ga fito da wasu sabbin matakan irin na dokar kulle.

    Daga cikin umarnin da kwamitin ya bayar na jiya, ma'aikatan gwamnati daga mataki na 12 zuwa ƙasa za su yi aiki daga gida har nan da mako biyar.

    Sannan duka makarantu a faɗin ƙasar za su kasance a rufe har zuwa watan Janairun 2021.

    Kwamitin ya bayyana cewa gidajen rawa da wuraren shan barasa da kuma wuraren motsa jiki za su ci gaba da zama a rufe a ƙasar.

    Sannan kuma kwamitin ya bayar da umarnin rufe gidajen abinci.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Saudiyya ta kama mutum 16 da fataucin miyagun kwayoyi

    Kwayoyi

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Saudiyya sun kama masu fataucin miyagun kwayoyi guda 16 da ke ayyukansu a babban birnin kasar, Riyadh da Jeddah.

    Hukumar hana fataucin kwayoyi ta General Directorate of Narcotics Control ce ta kama mutanen yayin da suke kokarin shiga da kwayar amphetamine kusan kusan miliyan 20 cikin kasar.

    Jaridar Saudi Gazzette ta ruwaito mai magana da yawun hukumar, Captain Muhammad Al-Najidi, yana cewa 10 daga cikinsu 'yan kasar ne, shida kuma 'yan kasashen waje.

    "Tawagar yaki da shan miyagun kwayoyi ta yi nasarar tarwatsa wani sansanin masu laifi a Riyadh da ya kunshi 'yan kasa mutum biyar da suka kware wurin sayar da kwayoyi kuma an kwace jumillar kwayar amphetamine 9,878,500 daga hannunsu," in ji shi.

    Al-Najidi ya ce an sake kama wasu mutum 10 a Jeddah, inda aka tarar da amphetamine guda 5,827,000 kunshe a cikin wasu kaya a gidansu.

    A wani samamen na daban, an kama wani dan kasar waje a lokacin da yake yunkurin shiga da amphetamine guda 3,228,323 a cikin wani kunshin kayan dankali a yankin Al-Haditha da ke kan iyakar kasar da Jordan.

  15. Sojojin Najeriya sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

    Bindiga

    Asalin hoton, Defense Headquarters

    Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta Operation Hadarin Daji sun ceto mutum 10 da 'yan fashi suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

    Mai magana da yawun hedikwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar John Enenche, shi ne ya bayyaa hakan, inda ya ce an ceto su ne ranar Lahadi.

    Ya ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan dakarunsu sun samu wani kiran gaggaawa daga kauyen Yenyewa cewa an ga 'yan fashi na zarya a yankin.

    Da zuwan sojojin ne kuma masu garkuwar suka tsere suka bar mutanen bayan an fara yi musu ruwan wuta, in ji Manjo Janar din.

    Ya kara da cewa tuni aka hada mutanen da danginsu.

    A wani samamen na daban kuma, dakarun rundunar Whirl Stroke sun kashe wasu 'yan fashin tare da kwace makamansu a Jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.

  16. Hare-haren Boko Haram sun karu da kashi 90 a Kamaru

    Boko Haram

    Asalin hoton, AFP

    Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a Kamaru sun karu a wannan sekarar da kashi 90 cikin 100 idan aka kwatanta da 2019.

    Wani bincike da cibiyar nazarin dabaru a nahiyar Afrika ma suna Africa Center for Strategic Studies, shi ne ya bayyana hakan, wanda ta yi shi a kan harkokin tsaron Kamaru.

    Rahoton ya ce Boko Haram ta kai hari akalla sau 400 a cikin shekara guda a Kamaru tun daga watan Satumban 2019 izuwa na 2020.

    Wannan adadin kuma shi ne adadi mafi yawa na hare-haren da kungiyar take kaiwa a cikin shekara guda a Kamaru.

  17. Ali Jita na fargbar dokar kulle saboda 'ya karbi kudin mutane'

    Ali Jita

    Asalin hoton, @alijitaa

    'Yan Najeriya da dama na fargabar sake shiga dokar kulle irin wadda aka sha ta tsawon makonni a baya, ciki har da mawakin Hausa Ali jita.

    Shahararren mawakin ya bi sahun 'yan Najeriya a shafukan zumunta yana rokon a jinkirta saka doar kullen cutar korona "saboda ba ya son mayar wa mutane kudinsu na waka da ya riga ya karba".

    "A bari sai watan Maris kafin a saka dokar kulle, rayuwar mawaka na da muhummanci, ba zan iya mayar wa da mutane kudinsu ba, na gama shiri da kashe kudi," in ji shi cikin wani sakon Twitter.

    Ya kara da cewa da ma tuni mawaka sunka shiga matsin rayuwa tun daga farkon wannan shekara.

    Dubban 'yan Najeriya ma na ta bayyana ra'ayoyinsu game da dokar kullen, wadda gwamnatin tarayya ta sake bullo da wasu a jiya Litinin biyo bayan karuwar masu kamuwa da cutar korona.

    Kalmar "lockdown" wato "kulle", tana cikin abin da 'yan Najeriya suka fi tattaunawa a kai a dandalin Twitter ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Trump ya kafa dokar kawata gine-ginen gwamnatin Amurka

    Fadar white House

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kafa sabuwar dokar da ke cewa wajibi ne a rika kawata gine-ginen gwamnatin tarayya na kasar a nan gaba.

    Tump ya ce yana so a rika gina su da salo ko siffa irin ta tsoffin ginin mutanen Girka ko Rumawa.

    Dokar ta ce har yanzu da yawa daga cikin gine-ginen gwamnati "ba su da wani ban-kaye", kamar na karnin da ya gabata.

    Ta ce ya kamata ginin gwamnati ya yi kama da "wuraren da aka fi sha'awa" kamar Fadar white House.

    Duk da cewa 'yan gargajiya za su yi maraba da dokar, sai dai akasari ba su ji dadin hakan ba.

    Cibiyar kwararru kan gine-gine ta Amurka, American Institute of Architects, ta ce tana "matukar adawa" da yunkurin.

    Sabuwar dokar - mai lakabin dokar kawata gine-ginen gwamnati wato "Promoting Beautiful Federal Civic Architecture" - ta kafa wani zaure da zai rika bai wa shugaban kasa shawara kan gine-ginen gwamnati na nan gaba.

  19. Korona a Najeriya: Mutum shida sun mutu, 356 sun kamu ranar Litinin

    Cutar korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 356 da suka kamu da cutar korona a ranar Litinin.

    Kazalika, ƙarin wasu mutum shida sun mutu sakamakon cutar.

    Birnin Abuja ne ke da adadi mafi yawa da mutun 79, yayin da Legas ke bi mata da mutum 59.

    Koronar ta kuma kama mutum 56 a Kaduna, sai Katsina mai mutum 37.

    Jihar Nasarawa na da 30, sai kuma Kano mai mutum 25, yayin da a Edo aka samu mutum 18 sai Gombe mai 14.

    Jihar Kebbi na da mutun 12, sai kuma jihohin Akwa Ibom da Sokoto da Rivers masu 7-7.

    A karshen jadawalin, Abia na da mutun 3, yayin da jihohin Ogun da Cross River ke da 1-1.

    A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bullarta zuwa yanzu sun kai 78,790, yayin da 68,483 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,227.

  20. Kun shigo shafin labarai kai-tsaye

    Umar Mikail ne zaikawo labaran na abubuwan da ke faruwa a sassn duniya, muamman a Najeriya da Nijar da makwabtansu.

    Da fatan kun wayi hantsin Talata lafiya.