Ma'aikatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin bayani game da yadda aka ceto ɗaliban makarantar Kankara na Jihar Katsina guda 344, tana mai cewa sojoji ne suka ceto yaran daga hannun 'yan bindigar da suka sace su.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da na Katsina, Aminu Masari, sun ce ƙungiyar Miyetti Allah ce ta taimaka wurin shiga tsakanin masu garkuwar da kuma gwamnati kafin sakin 'yan makarantar a dajin Jihar Zamfara.
Sai dai kuma, mai magana da yawun hedikwatar tsaro, John Enenche, ya ce rundunar soja ce ta ceto yaran a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.
Kazalika, ma Ahmed Jibrin, tsohon soja kuma mataimaki na musamman ga Ministan Tsaro Janar Bashir Magashi, ya tabbatar da batun da Enenche ya yi, yana mai cewa sojoji sun kashe da yawa daga cikin 'yan bindigar bayan an zagaye su.
Yayin da ya bayyana ta kafar talabijin ta NTA a jiya Asabar, Ahmed ya ce sojojin ba su iya tarwatsa 'yan fashin ba baki ɗayansu saboda gudun kar a ji wa yaran da suke hannunsu rauni bayan sun yi amfani da su domin samun garkuwa daga sojojin.
"Bayan an bayar da umarni, dakarun soja sun kewaye masu garkuwar ta ɓangare huɗu, ciki har da ƙarin bataliya da ta zo daga wani sansanin domin a tabbatar an hana su sakat.
"An kewaye su ruf kuma su ma sun san hakan, suna jin motsin sojoji ta sama da ta ƙasa.
"A lokacin da suka isa wurin da yaran suke, sojoji sun fuskanci turjiya daga miyagun kuma suka murƙushe su suka ƙarasa cikin dajin.
"Duk da cewa babu yaron da ya jikkata, an kashe 'yan fashi da yawa saboda a lokacin da sojoji suka yi yunƙurin shiga dajin an yi musu kwanton-ɓauna a wuri biyu. "Hasali ma, a wuri na biyun an fafata sosai saboda a ɓoye suke kuma duk sun kewaye hanyar.
"Sun kawo wa sojoji tsaiko na awanni kafin su kashe su."
Ahmed Jibrin ya ce yayin da sojoji ke fafatawa, ana can ana tattaunawa kuma da 'yan bindigar a wani yunƙurin na daban don ceto yaran.