Dakarunmu ne suka ceto ɗaliban makarantar Kankara - Sojojin Najeriya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Ƙasashe a Turai na dakatar da jirage daga Birtaniya shiga ƙasashensu

    Birtaniya

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƙasashe da dama na dakatarwa ko kuma ƙoƙarin dakatar da jirage shiga ƙasashen nasu daga Birtaniya saboda guje wa yaɗuwar sabon nau'in cutar korona da ya ɓulla a ƙasar.

    Tuni Netherlands da Belgium sun hana jirage daga Birtaniya shiga ƙasashensu.

    Ministan Harkokin Wajen Italiya ya nuna cewa gwamnatinsu za ta hana jiragen shiga ƙasarsa. Haka nan, an hana jiragen ƙasa shiga Belgium.

    Faransa da Jamus ma na shirin ɗaukar irin wannan matakin, a cewar rahotanni.

    Sabon nau'in cutar ta korona ya yaɗu cikin sauri a Landan da kuma Kudu maso Gabashin Ingila.

    Firaminista Boris Johnson ya saka sabbin dokokin kulle na mataki na huɗu masu tsauri, har ma aka fasa yin sassauci kan shirin bikin Kirsimeti, wanda gwamnati ta yi alƙawari a baya.

  2. El-Rufai ya umarci ma'aikatan Kaduna su yi aiki daga gida saboda korona

    Gwamna Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, @GovKaduna

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci ma'aikata 'yan ƙasa da mataki na 14 da su fara aiki daga gida daga gobe Litinin sakamakon ɓarkewar annobar korona a zagaye na biyu.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnatin jihar, Muyiwa Adekeye, ya sanya wa hannu a yau Lahadi ta ce an ɗauki matakin ne bayan Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da sabuwar dokar kulle a jihar.

    Da ma tuni gwamnati ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu a jihar, kuma sanarwar ta ce za su ci gaba da kasancewa a garƙame har sai hali ya yi.

    Daga cikin tanadin sabuwar dokar, wuraren motsa jiki da wuraren taron biki da na shaƙatawa za su kulle har sai baba ta gani.

    Kazalika wuraren cin abinci ma za su riƙa sayarwa ne a mazubi domin ci a gida, ba za a ci a wurin ba.

    Haka nan su ma otel-otel za su buɗe amma za su rufe wuraren cin abincinsu, sai dai ɗakunan kwana kawai.

    Sauran abin da dokar ta ƙunsa:

    • Wajibi ne wuraren addini su samar da kayan wanke hannu da bayar da tazara, sannan kuma a rage yawan masu shiga
    • Kar sallar jam'i ko addu'ar coci ta wuce awa ɗaya
    • Saka takunkumi wajibi ne idan za a fita daga gida
    • Taron jama'a haramun ne
    • Dole ne wuraren kasuwanci su tanadi man wanke hannu da kuma na'urar duba zafin jikin mutum
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum 177 a Iran

    Iran

    Asalin hoton, ISNA

    Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Iran ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa a cikin awa 24 da suka gabata, mutum 177 ne suka mutu sakamakon cutar korona.

    Kazalika mutum 6,312 ne suka harbu da cutar kuma an kwantar da 805 daga cikinsu a asibiti, in ji Dr. Sima Sadatollari.

    Ya ƙara da cewa majinyata 5,563 na cikin mummunan hali duk da cewa ana ba su kulawa.

    A cewar alƙaluman gwamnati, jumillar mutum 1,158,384 ne suka kamu da cutar korona a Iran zuwa yanzu.

  4. BBC za ta karrama Rashford da kyauta ta musamman a yau

    Marcus Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau Lahadi ɗan wasan gaban Manchester United da Ingila Marcus Rashford zai karɓi kyauta ta musamman daga kafar yaɗa labarai ta BBC sakamakon ayyukansa na ciyar da yara talakawa a Birtaniya.

    Za a ba shi kyautar ne yayin bikin BBC Sports Personality, wanda za a gudanar da misalin ƙarfe 9:00 agogon Najeriya da Nijar daga Media City da ke Salford, Birtaniya.

    A gefe guda kuma, an saka Rashford mai shekara 23 cikin rajistar sunayen 'yan wasa na musamman ta shekara-shekara mai laƙabin Football Black List.

    BBC za ta haska fim na musamman da aka shirya kan ɗan wasan wanda ya riƙa jawo hankalin gwamnati kan ta ƙara yawan waɗanda take ciyarwa kyauta a cikin shirin 'yan makaranta saboda annobar korona.

    Za a ba shi kyautar ne tare da sauran 'yan wasa na musamman na shekara da rukunin alƙalan BBC ke zaɓa duk shekara, wanda Rashford ba ya cikinsu.

    Tawagar alƙalan ta aminta cewa ya kamata a karrama Rashford saboda ƙoƙarinsa a wajen filin wasa domin ƙarfafa masa gwiwa ganin cewa dokokin samun kyautar ɗan wasa na musamman sun ta'allaƙa ne kan irin nasarorin da ɗan wasa ya samu a shekarar.

    Mutum shida da ke kan gaba waɗanda kuma za a zaɓa a cikinsu su ne:

    • Jordan Henderson (ƙwallon ƙafa)
    • Stuart Broad (ƙwallon cricket)
    • Hollie Doyle (tseren doki)
    • Tyson Fury (damben boxing)
    • Lewis Hamilton (tseren motoci na Formula 1)
    • Ronnie O'Sullivan (wasan snooker)
  5. Dakarunmu ne suka ceto ɗaliban makarantar Kankara - Sojojin Najeriya

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Defense Headquarters

    Ma'aikatar tsaron Najeriya ta yi ƙarin bayani game da yadda aka ceto ɗaliban makarantar Kankara na Jihar Katsina guda 344, tana mai cewa sojoji ne suka ceto yaran daga hannun 'yan bindigar da suka sace su.

    Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da na Katsina, Aminu Masari, sun ce ƙungiyar Miyetti Allah ce ta taimaka wurin shiga tsakanin masu garkuwar da kuma gwamnati kafin sakin 'yan makarantar a dajin Jihar Zamfara.

    Sai dai kuma, mai magana da yawun hedikwatar tsaro, John Enenche, ya ce rundunar soja ce ta ceto yaran a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.

    Kazalika, ma Ahmed Jibrin, tsohon soja kuma mataimaki na musamman ga Ministan Tsaro Janar Bashir Magashi, ya tabbatar da batun da Enenche ya yi, yana mai cewa sojoji sun kashe da yawa daga cikin 'yan bindigar bayan an zagaye su.

    Yayin da ya bayyana ta kafar talabijin ta NTA a jiya Asabar, Ahmed ya ce sojojin ba su iya tarwatsa 'yan fashin ba baki ɗayansu saboda gudun kar a ji wa yaran da suke hannunsu rauni bayan sun yi amfani da su domin samun garkuwa daga sojojin.

    "Bayan an bayar da umarni, dakarun soja sun kewaye masu garkuwar ta ɓangare huɗu, ciki har da ƙarin bataliya da ta zo daga wani sansanin domin a tabbatar an hana su sakat.

    "An kewaye su ruf kuma su ma sun san hakan, suna jin motsin sojoji ta sama da ta ƙasa.

    "A lokacin da suka isa wurin da yaran suke, sojoji sun fuskanci turjiya daga miyagun kuma suka murƙushe su suka ƙarasa cikin dajin.

    "Duk da cewa babu yaron da ya jikkata, an kashe 'yan fashi da yawa saboda a lokacin da sojoji suka yi yunƙurin shiga dajin an yi musu kwanton-ɓauna a wuri biyu. "Hasali ma, a wuri na biyun an fafata sosai saboda a ɓoye suke kuma duk sun kewaye hanyar.

    "Sun kawo wa sojoji tsaiko na awanni kafin su kashe su."

    Ahmed Jibrin ya ce yayin da sojoji ke fafatawa, ana can ana tattaunawa kuma da 'yan bindigar a wani yunƙurin na daban don ceto yaran.

  6. Miyagu za su fara amfani da NIN don cutar 'yan Najeriya

    Katin ɗan ƙasa

    Asalin hoton, NIMC

    Hukumar samar da katin ɗan ƙasa a Najeriya ta National Identity Database in Nigeria (NIMC) ta gargaɗi jama'a da su kiyaye da sabbin saƙonnin da wasu miyagu za su fara turo musu suna masu iƙirarin cewa su ma'aikatan MTN ne ko Airtel ko 9Mobile ko Glo.

    Cikin wata sanarwa da ta wallafa, NIMC ta ce: "Cikin 'yan kwanaki masu zuwa masu zamba za su fara turo muku saƙon cewa an tura muku wani rukunin lambobi na neman tantance lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN, saboda haka ku sake aiko mana da ita."

    NIMC ta ce sake aika musu da lambar ka iya jefa mutum cikin haɗarin cuta, ta yadda za a iya amfani da bayanansa wurin sabunta layin da ya ɓata da kuma yin sayayya da sunansa ta intanet ba tare da ya sani ba.

    "Ba za su tambaye ku lambobin BVN ba ko NIN ko bayanan katinku, saboda za a gano su da wuri. Muna roƙonku da ku share irin wannnan saƙonnin kawai.

    "Idan kamfanin layin da kuke amfani da shi ya kasa tantance lambar NIN ɗinku, za su nemi ku je ofishinsu ne domin yin hakan."

    A makon da ya gabata ne hukumar sadarwa ta Najeriya NCC ta bayar da umarnin rufe duk wani layin waya da ba a yi masa rajista da lambar ɗan ƙasa ba ta NIN cikin mako biyu.

    'Yan Majalisar Tarayyar Najeriya sun yi umarni da a ƙara wa'adin zuwa mako takwas amma hukumar ta ƙeƙashe ƙasa ta ce umarninta mako biyu na nan daram.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da kansiloli a Jihar Gombe

    Muhammadu Inuwa Yahaya

    Asalin hoton, @GovernorInuwa

    Bayanan hoto, Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya

    Hukumar zaɓe ta Jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, Gombe State Independent Electoral Commission (GOSIEC), ta ce jam'iyyar APC mai mulkin jihar ce ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da kansiloli a zaɓen jihar.

    A jiya Asabar ne aka gudanar da zaɓen, inda APC ta cinye baki ɗayan kujerun shugaban ƙaramar hukuma guda 11 da kuma na kansila guda 114 na jihar.

    Shugaban GOSIEC, Saidu Awak, ya shaida wa BBC cewa mutane ne suka yi zaɓen kuma abin da suka zaɓa kenan.

    "A kodayaushe ana nuna damuwa (game da irin wannan sakamakon zaɓen), ni kuma ina faɗa wa mutane cewa ba mu ne muke zaɓen ba, abin da mutane suka zaɓa muke bayyanawa," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

    Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana "cikin kwanciyar hankali".

    Jam'iyya uku ne suka shiga zaɓen, a cewar Saidu Awak, su ne APC da PDP da PRP.

    An sanar da sakamakon ne a gaban ƙungiyoyin farar hula da 'yan sanda da 'yan jarida da kuma wakilan jam'iyyun.

    Ita ma Jihar Kano za ta gudanar da nata zaɓen ranar 16 ga watan Janairu mai zuwa, inda za a zaɓi shugabannin ƙaramar hukuma 44 da kansiloli.

  8. An samu ɓullar sabon nau'in cutar korona mai saurin yaɗuwa

    Cutar korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana tattaunawa da hukumomi a Burtaniya kan ɓullar sabon nau'in cutar Korona da ya fi saurin yaɗuwa da kusan kashi 70 cikin 100 a kan wanda aka sha wahalarsa a karon farko.

    Gwamnatin Burtaniya ta ce tuni sabon nau'in ya fara bazuwa tsakanin al'umma a London.

    Wakilin BBC ya ce mahukunta sun fahimci cewa dole ne su ɗauki sabbin matakai cikin gaggawa lura da yadda sabbin alƙaluman masu kamuwa da cutar ke hau-hawa babu ƙaƙƙautawa.

    A kan haka gwamnati ta sanar da sabbin dokokin kulle da tuni suka fara aiki a daren jiya Asabar.

    Yayin da yake jawabi daga Fadar Downing street, Firaminista Boris Johnson ya ce babu batun sassauci kan bikin Kirsimeti kamar yadda aka yi alƙawari a baya.

    Tuni Netherlands ta rufe ƙofa ga duk wani jirgi da ya fito daga Burtaniya bayan da aka samu wani mutum ɗauke da sabon nau'in cutar ta Covid-19.

  9. 'Yan Sudan sun fusata kan rashin sauyin rayuwa bayan sauya gwamnati

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    An gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar Sudan kan rashin sauyin rayuwa mai kyau da mutane ke kuka da shi shekara biyu bayan juyin-juya halin da ya kawo karshen mulkin Omar al-Bashir.

    Masu zanga-zangar sun yi ta kona tayoyi a lardin kudancin Khartoum kafin daga bisani su yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa suna neman a yi musu adalci.

    Wasunsu na dauke da hotunan mutanen da suka rasa rayukansu a yayin zanga-zangar ta shekarun baya.

    Masu zanga-zangar sun nuna fusatarsu game da abin da suka kira jan kafa a sauyin da suke sa ran samu karkashin wannan gwamnati, musamman matsalar tattalin arziki da tsadar kayayyaki.

    Zanga-zangar ta zo ne yayin biki karo na biyu na tunawa da juyin-juya khalin da ya gudana ranar 19 ga watan Disamban 2018.

  10. Ƙarin mutum shida sun mutu a Najeriya sakamakon cutar korona

    Korona a Najeriya

    Asalin hoton, NCDC

    Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 920 da suka kamu da cutar korona a ranar Asabar.

    Kazalika, ƙarin wasu mutum shida sun mutu sakamakon cutar.

    Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa da mutun 308, yayin da Abuja ke bi mata da mutum 207.

    Koronar ta kuma kama mutum 179 a Kaduna, sai Plateau mai mutum 46, Niger na da 43 yayin da Adamawa ke da 26.

    Jihar Sokoto na da 18, sai Rivers mai 16, Yobe na da 15, Enugu da Kano 13-13, Ogun 12, Delta 10 sai Edo mai mutum 5.

    Osun da Oyo na da mutum 3-3 a jadawalin, yayin da Anambra ke da mutum 2, Ekiti kuma na da 1 tal.

    A jimillance adadin mutunen da cutar ta kama tun daga bullarta zuwa yanzu sun kai 77, 933, yayin da 67,784 suka warke aka kuma samu asarar rayuka 1,218.

  11. Fatan kun wayi hantsi lafiya

    Ku biyo ni Umar Mikail a wannan shafi domin karanta labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya a Nijar da maƙwabtansu.

    Barkanku da wannan lokaci tare da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya lami lafiya.