Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Legas ta rufe makarantu
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Awwal Ahmad Janyau
'Korona' ta yi ajalin tsohon Shugaban Burundi, Pierre Buyoya
Tsohon Shugaban Burundi, Pierre Buyoya ya mutu, kamar yadda shugaban watsa labarai na gwamnatin ƙasar, Willy Nyamitwe ya tabbatar.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce "an tabbatar da mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Pierre Buyoya, kuma babu shakka a maganar".
Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP ya ruwaito iyalan marigayin suna cewa Mista Buyoya ɗin ya mutu ne a Paris bayan ya yi fama da cutar korona.
Mista Buyoya, wanda ɗan ƙabilar Tutsi ne, ya jagoranci ƙasar a matsayin shugaban ƙasa har sau biyu, daga 1987 zuwa 1993, sai kuma daga 1996.
Da 'yan bindiga muka tattauna, ba da Boko Haram ba – Gwamna Matawalle
Gwamna Matawalle ya ce ba a a hannun Boko Haram aka karɓo shu ba, daga hannun Fulani ƴan bindiga aka karbo ɗaliban.
Ya ce a zaman sulhun da suka yi da su, sun gindaya musu wasu matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya wanda kuma aka alƙawarta za a sasanta.
Daga cikin ƙorafin Fulani, akwai yadda ake kashe musu shanu da cin zarafinsu da suke zargin ƴan banga ko ƙato da gora.
Kuma ya ce a shirye yake a ci gaba da ƙoƙari irin wannan wajen sulhu don tsare ƙasa, kuma duk wanda ya ƙi zai fuskanci fushin hukuma, in ji Matawalle.
Mutum sama da dubu suka kamu da korona a Najeriya ranar Alhamis
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 1,145 da suka kamu da cutar korona a ranar Alhamis, mutum guda ya sake mutuwa.
Jihar Legas ce ke da adadi mafi yawa na mutane 459 da suka sake kamuwa da annobar, yayin da Abuja ke bi mata da mutum 145.
Koronar ta kuma kama mutum 80 a Filato, sai Kaduna 138, Katsina mutum 70, a Gombe mutum 52.
Sannan akwai jihar Neja mai mutum 31 da Kano mutum 23, sai Bayelsa mai mutum 21, ita kuma Ondo mutum 18.
Jihar Ribas ma an samu mutum 17, Ogun mutum 12, oyo 12, Edo 8, Nasarawa 8, Ebonyi 7, Osun 6, Ekiti 5.
A jihar Kebbi mutum 5, Borno 4 da Jigawa 3, Akwa Ibom 2, Anambra 1.
A jumulla adadin mutanen da cutar ta kama tun daga ɓullarta zuwa yanzu sun kai 76,207, sai kuma 67,110 sun warke, yayin da 1, 201 suka rasu.
Barkanmu da safiya
Bayani kan maƙala - Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Jama'a barkanmu da safiyar Juma'a, 18 ga watan Disamban 2020. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.