Korona: Kaduna ta sanar da ranakun rufe makarantu da jami'o'in jihar
Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Rufewa
Bayani kan maƙala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Talata idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan wasu daga cikin labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.
Korona: Kaduna ta sanar da ranakun rufe makarantu da jami'o'in jihar
Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta umarci makarantun jihar da su tabbatar sun kammala jarrabawa sun rufe zuwa ranar Laraba, 16 ga watan Disamban 2020.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ƙaruwar yaɗuwar korona a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
A wata sanarwa da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar wadda ke ɗauke da sa hannun kwamishinan ilimi na jihar, za a dakatar da koyar da karatu a cikin aji a makarantun sakandare da jami'o'i da kwalejoji da ke jihar inda aka buƙaci makarantun su nemi wasu hanyoyi na koyarwa da suka haɗa da ta intanet.
Gwamnatin jihar ta kuma ce za a ci gaba da koyarwa ta gidan talabijin da rediyo na jihar kamar yadda aka rinƙa yi a lokacin kullen korona a baya.
Asalin hoton, KDSG
An fara shirin tabbatar da nasarar Joe Biden a hukumance
An fara tsare-tsaren tabbatar da nasarar Joe Biden a hukumance yayin da wakilai na musamman dari biyar da talatin da takwas suka kada kuri'arsu.
Masu zabe na kowace jiha suna ganawa ta intanet.
Masu zabe uku na Jam'iyyar Dimokrat a Vermont su ne wadanda suka fara yin zabe sai jihohin Republican - Indiana da Mississippi da Tenesse suka biyo baya.
Gaba a yau ne Joe Biden zai samu tabbacin nasarar da ya samu saboda ba a cika samun batun sauya matsaya ba.
Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya kai ziyara Maiduguri
Asalin hoton, Isa Gusau
Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar III ya kai ziyara Maiduguri, inda ya jagoranci majalisar sarakunan gargajiya ta Najeriya.
A ziyarar da suka kai, sarakunan gargajiyan sun nuna rashin jin daɗinsu kan irin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Borno.
A kwanakin baya ne dai 'yan ƙungiyar Boko Haram suka kai hari a Zabarmari inda suka kashe manoma 73.
Asalin hoton, Isa Gusau
Jami'an tsaro sun gano wurin da Ɗaliban GSS Ƙanƙara suke – Masari
Asalin hoton, @GovernorMasari
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa jami'an tsaro sun gano wurin da ɗaliban makarantar Ƙanƙara suke.
A wani saƙo da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya wallafa, ya ruwaito gwamna Masari ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya damu ƙwarai kan yadda za a ceto ɗaliban, yana mai cewa ya dace ya ziyarci shugaban ƙasar ne kawai don ba shi ƙarin bayani kan halin da ake ciki na ceton.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
A saka malaman makaranta a gaba-gaba wurin rigakafin korona – UNESCO
Asalin hoton, UNESCO
Hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNESCO, na kira da a saka malaman makaranta da kuma ma'aikatan ilimi a faɗin duniya a cikin jerin mutanen farko da za a fara yi wa riga-kafin korona.
Hukumar ta yi kira da cewa ya kamata a saka malamai a matsayin ma'aikata na gaba-gaba, kamar yadda aka saka ma'aikatan lafiya a kan gaba.
Hukumar ta UNESCO ta jaddada cewa yana da matuƙar amfani a bar makarantu da sauran wuraren samun ilimi a buɗe domin kada a kawo cikas a ɓangaren.
Hukumar ta yi ƙiyasin cewa akwai makarantu da ke rufe a ƙasashe 27 a faɗin duniya.
Sama da mutum miliyan 70 korona ta kama a duniya
A daidai lokacin da cutar korona ke ƙaruwa ƙara bazuwa, adadin waɗanda ke kamuwa da cutar a fadin duniya ya haura miliyan 70, inda a yammacin yau, jumullar mutum 72,417,335 aka tabbatar da sun kamu tun bayan ɓullar cutar.
Amurka ce dai a kan gaba da sama da mutum miliyan 16 sai kuma India ce ta biyu da sama da mutum miliyan tara, sai kuma Brazil ta uku da sama da mutum miliyan shida.
Amurkar ce dai kan gaba a yawan mace-mace inda kusan mutum 300,000 suka mutu.
Ƙasashe da dama na ƙara tsaurara dokokin kulle sakamakon abin da suke tunani ɓullar cutar a karo na biyu.
Chelsea za ta fuskanci kalubalen Atletico a Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid za ta fafata da Chelsea a wasan zagaye na biyu a Champions League karawa ta takwas da za su yi a tsakaninsu a gasar Turai.
Atletico ta kai zagaye na biyu a Champions League a wasan ranar karshe a cikin rukuni a gasar bana, bayan da ta doke Salzburg, za kuma ta kara da Chelsea.
Wannan ne wasa na takwas da ƙungiyoyin za su kara a gasar Zakarun Turai, bayan da kowacce ta ci karawa 2-2 da canjaras uku.
A kakar bara ne Atletico ta hadu da Liverpool mai rike da kofin Champions League ta kuma yi waje da ita.
Sai dai Chelsea ta kwan da sanin Atletico ba kanwar lasa ba ce a wasan da za su yi na farko cikin watan Fabrairu da karawa ta biyu cikin watan Maris.
Masari ya kai wa Buhari ziyara a Daura kan ɗaliban Ƙankara
Asalin hoton, Bashir Ahmed
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara garin Daura, kwanaki kaɗan bayan sace ɗalibai sama da 500 a jihar.
A wani saƙon Twiiter da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmed, ya wallafa, ya bayyana cewa Gwamna Masari ya je Daura ne domin ya yi wa shugaban ƙasar ƙarin bayani kan halin da ake ciki dangane da ƙoƙarin da ake yi na gano ɗaliban da aka sace.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
An soma gudanar da riga-kafin korona a Amurka
An fara yi wa kashin farko na Amurkawa allurar riga-kafin cutar korona. Waɗanda za a yi wa rigakafin sun haɗa da ma'aikatan lafiya da tsofaffi da kuma waɗanda suke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Wakilin BBC ya ce zuwan allurar rigakafin na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurka ke fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da annobar korona inda ake samun mace-mace sama da mutum dubu biyu kowace rana.
Maƙasudin shirin shi ne yi wa Amurkawa miliyan ɗari rigakafin cutar nan da Afrilu, amma kamfanin Pfizer ya ce yana tattaunawa kan ko zai iya samar da adadin alluran rigakafin da ake buƙata wajen cimma wannan buri.
Amurka na ɗaya daga cikin ƙasashen da korona ta fi yi wa illa amma bayanai na cewa rabin al'ummar ƙasar ba su gamsu da matakin ba ko kuma ba sa sha'awar samun rigakafin.
An rantsar da Shugaba Ouattara na Ivory Coast a wa'adi na uku
Asalin hoton, EPA
A yau Litinin ne aka rantsar da Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara a wa'adi na uku bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar mai cike da ruɗani da rikici.
Shugabannin ƙasashen Togo da Ghana da Benin sun halraci taron rantsuwar kama aiki .
A watan da ya gabata ne dai ya lashe zaɓen ƙasar bayan 'yan takara daga jam'iyyun adawa sun ƙaurace wa zaɓen.
A jawabin da ya yi na kama aiki a wa'adinsa na uku, ya yi bayani kan halin da siyasar ƙasar ke ciki inda ya bayar da umarnii ga Firaiministan ƙasar da ya haɗa taro da jam'iyyun siyasar ƙasar kafin a gudanar da zaɓen 'yan majalisa a farkon shekara mai zuwa.
Shugaban ya sha alwashin kafa ma'aikatar haɗin kai a yayin da ƙasar ke fama da rabuwar kai daga ɓangarori daban-daban tun bayan zaɓen ƙasar.
An kashe sarakunan gargajiya biyu a Kamaru
Ƙungiyoyin kare haƙƙi a Kamaru sun yi Allah-wadai da yin garkuwa da kuma kisan sarakunan gargajiya da ake yi a yankin rainon Ingila.
A ƙarshen makon da ya gabata, an yi garkuwa da sarakunan gargajiya guda uku a yankin Kudu maso Yammacin ƙasar da kuma wani a yankin Arewa maso Yamma.
An kashe biyu daga cikinsu, a cewar gwamnan yankin Kudu maso Yamma, Bernard Okalia Bilai.
A ranar Litinin, ɗan fafutika kuma lauyan kare haƙƙi, Felix Agbor Nkongho ya bayyana lamarin da cewa "laifi ne ga al'adarmu da ɗabi'unmu".
Gwamnati na zargin 'yan tawayen yankin, sai dai ƙungiyoyin tawayen ba su ɗauki alhakin harin ba.
Sai dai, 'yan tawayen sun sha alwashin sace duk wani basarake da ya goyi bayan zaɓen yankuna irinsa na farko da aka gudanar a farkon watan nan.
Ana kallon waɗannan hare-hare a matsayin cika alƙawarin da 'yan tawayen suka yi.
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Tigray na Ethiopia
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Tigray da ke arewacin Habasha wato Ethiopia, mako biyu bayan da aka fatattaki ƙungiyar TPLF daga Mekelle, babban birnin yankin.
Wakilin BBC ya ce Firaministan Habasha ya kai ziyarar ba-zata zuwa birnin Mekelle ranar Lahadi a ziyararsa ta farko zuwa wajen cikin fiye da shekara ɗaya da rabi.
Abiy Ahmed ya gana da janar-janar ɗin da suka jagoranci samamen kan kungiyar TPLF.
An kuma gyara hanyoyin sadarwar da aka katse tsawon makwanni, sai dai har yanzu babu sabis na intanet.
Sabuwar gwamnatin ta riƙon ƙwarya ta umarci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki.
Sai dai jami'an gwamnatin za su fuskanaci ƙalubalen tsaro da kuma rashin samun goyon bayan jama'a.
'Yan daba sun tarwatsa taron matasan Arewa a Kaduna
Asalin hoton, CNG
Wasu tsageru da ake zargin 'yan daba ne sun tarwatsa taron gamayyar ƙungiyoyin Arewa Coalition of Northern Groups (CNG) a ɗakin taro na Arewa House da ke Kaduna.
Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da suke tsaka da taron ƙara wa juna sani game da matsalolin tsaro da ke addabar yankin arewacin Najeriya.
Nastura Ashiru Shariff, jigo a ƙungiyar CNG, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.
Asalin hoton, CNG
Matasan na Arewa sun shirya taron ne domin lalubo hanyoyin haɗa kai tsakanin mazauna jihohin Arewa 19 da zummar kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga a yankin.
Ƙungiyar ta CNG ta yi barazanar yi wa garin Katsina tsinke domin gudanar da zanga-zanga idan har gwamnati ta gaza ceto ɗaruruwan yaran da 'yan bindiga suka sace a makarantar kwana ta sakandaren GSSS Kankara.
Gwamna Bello Masari na Katsina ya ce yara 333 ne suka ɓace tun bayan kai harin a daren Juma'a da ta gabata.
Manhajojin Google sun gamu da rashin network
Manhajojin Google da suka haɗa da YouTube da Gmail da Docs sun fuskanci ɗaukewar network, inda masu amfani da su suka gaza shiga da yawa daga cikin manhajojin kamfanin da tsakar ranar yau Litinin.
An shafe tsawon fiye da minti 30 ana fama da rashin network daga misalin ƙarfe 12:30 agogon Najeriya kafin su dawo aiki.
Masu amfani da manhajojin Gmail, Google Drive, Android Play Store, Maps sun yi ƙorafi game da yadda suka daina aiki.
Amma matsalar ba ta shafi shafin matambayi-ba-ya-ɓata ba na google search.
Ɗaukewar ta yi tasiri ga miliyoyin masu amfani da google, waɗanda suka dogara da shi wurin gudanar da ayyuka na yau da kullum.
An yi wa manyan ma'aikatun Amurka kutse
Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Amurka ta bayar da wani umarnin gaggawa bayan ta bayyana cewa an yi kutse a ma'aikataun kasuwanci da na baitul malinta.
An umarci dukkanin ma'aikatun gwamnatin tarayya da su sauka daga kan layin intanet na SolarWinds, layin network da wasu "miyagu" suke kai wa hari.
A hukumance, gwamnati ba ta bayyana wanda ya kai harin ba.
Lamarin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan wani kamfanin tsaron intanet mai suna FireEye ya ce an sace masa kayayyakin yin kutse.
Hukumar kula da tsaron intanet ta Amurka mai suna Cybersecurity and Infrastructure Security Agency (Cisa) ta ce harin ya kai girman da zai iya kawo wa harkokin gwamnati cikas.
Kamfanin SolarWinds, wanda ya ƙirƙiri kayan aikin kutsen, ya nemi masu amfani da manhajarsa ta Orion da su sabunta ta cikin gaggawa domin daƙile "matsalar tsaro".
Champions League: Barcelona za ta fafata da PSG
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta ɓarje gumi da Paris Saint-Germain a zagayen 'yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Hakan na nufin Neymar zai fuskanci tsohon kulob ɗinsa karon farko tun bayan da ya bar su kuma ya sake tabbatar da dalilin da ya sa ya bar ƙungiyar.
Kazalika, babu mamaki ya zama wasan zagayen 'yan 16 na Champions League na ƙarshe ga Messi a cikin jesin Barcelona, ganin yadda abubuwa ke rikicewa tsakanin gwarzon ɗan ƙwallon da mahukuntan ƙungiyar ta Catalonia.
A wasa na ƙarshe da ƙungiyoyin biyu suka buga ranar 8 ga watan Maris na 2017, Barca ce ta lallasa PSG da 6-1 bayan PSG ɗin ta ci wasan farko 4-0.
Wani wasan da zai ja hankali shi ne wanda Chelsea za ta kara da Atletico Madrid.
Kazalika, wadda ta fi kowa goshi a gasar wato Real Madrid za ta yi nata wasan da Atalanta ta Italiya.
Sai kuma masu riƙe da kofin Bayern Munich, wadda za ta gwabza da Lazio ta Italiya.
Ƙungiyar Cristiano Ronaldo ta Juventus za ta buga da FC Porto ta Portugal da kuma karawa tsakanin Sevilla da Borussia Dortmund.
Za a buga wasannin farko ranakun 16,17, 23, 24 na watan Fabarairun 2021, kafin daga bisani a buga na biyun a ranakun 9,10,16,17 na watan Maris.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Amurka ta cire sunan Sudan daga cikin masu ɗaukar nauyin ta'addanci
Asalin hoton, Reuters
Amurka ta cire sunan Sudan daga jerin sunayen ƙasashen da ke ɗaukar nauyin ta'addanci, a cewar ofishin jakandacinta da ke birnin Khartoum.
"Wa'adin da aka bayar na kwana 45 ya ƙare kuma Sakataren Harkokin Waje ya sanya hannu kan zare sunan Sudan daga cikin masu ɗaukar nauyin ta'addanci daga yau (14 ga Disamba), wanda za a wallafa a Rajistar Gwamnatin Tarayya," kamar yadda ya bayyana a Facebook.
Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa a watan Oktoba cewa za a cire Sudan daga rajistar sunayen bayan ta biya diyyar dala miliyan 335 ga iyalan Amurkawa da aka kashe yayin harin bam a kan ofisoshin jakadancin Amurka a Afirka.
Firaministan Sudan Abdalla Hamdok ya ce an tura kuɗin.
An saka Sudan cikin jerin ne a 1993 lokacin da shugaban ƙungiyar Al-Qaeda Osama Bin Laden ke zaune a can a matsayin baƙon gwamnatin ƙasar.
An saka sunan nata ne tare da ƙasashen Iran da Koriya ta Arewa da Syria.
Ceto ɗaliban da aka sace a Katsina abu ne mai sauƙi - Ministan Tsaro Bashir Magashi
Asalin hoton, @DefenceInfoNG
Ministan Tsaro a Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi ya ce aikin ceto yaran da 'yan bindiga suka sace a makarantar kwana ta Kankara "abu ne mai sauƙi" kuma cikin "'yan awanni".
Janar ɗin ya bayyana haka ne yayin ziyarar jaje da tawagar Gwamnatin Tarayya ta kai wa Gwamnan Katisna Aminu Masari ranar Lahadi ƙarƙashin jagorancinsa.
"Zuwa yanzu jami'an tsaron da ke wurin sun ba mu bayanai game da halin da ake ciki, abin da muke so shi ne mu san cikakken abin da ya faru kuma insha Allah wannan aikin zai zama mai sauƙi," in ji shi.
"Nan da 'yan awanni za mu tabbatar da cewa mun ceto yaran nan...ba tare da wani (daga cikin yaran) ya ji rauni ba.
"Muna da bayanai game da maɓoyarsu ('yan bindiga) da kuma ayyukansu. Saboda haka wannan aiki abu ne mai sauƙi sosai a wurin sojoji da 'yan sanda. Abin da kawai muke buƙata shi ne addu'a saboda kar abin ya shafi wasu."
Yayin jawabinsa, Gwamna Masari ya gode wa tawagar sannan ya shaida musu cewa yaran da aka sace ɗin sun fito ne daga kowane ɓangare na jihar da wajenta "saboda makarantar kwana ce".
Masari ya ce ya zuwa lokacin da yake magana, yara 333 ne ba a gani ba a cikin 839 da suke makarantar.
'Yan Najeriya na ci gaba da sukar Shugaba Muhammadu Buhari kan rashin halartar wurin da abin ya faru, yayin da yake yin hutun mako ɗaya a jihar, wadda mahaifarsa ce, a lokacin da miyagun suka kai harin na daren Juma'a.
Brexit: Wakilin EU zai yi wa shugabannin ƙungiyar jawabi
Babban wakilin Tarayyar Turai kan batun ficewar Birtaniya daga ƙungiyar EU, Michel Bernie, zai yi jawabi ga wakilan mambobin kungiyar 27 game da tattaunawar.
Bernie zai yi bayani ne kan inda aka kwana a yarjejeniyar kasuwancin da suke ƙokarin ƙullawa da Birtaniya game da gajiyar da ɓangarorin za su ci bayan ficewar ƙasar.
Mako biyu suka rage Birtaniya ta kammala ficewar amma har yanzu ba su cimma matsaya ba ta fuskar kasuwanci da EU.
Birtaniya ta kafe cewa ba za ta sauya tsarin da take da shi ba kan abin da ya shafi dokokin kasuwancinta da kuma kamun kifi.