Rundunar sojin Najeriya ta mayar
da martani kan binciken da Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta
ce za ta yi kan laifukan yaƙi da aka aikata a Najeriya.
A ranar Juma’a ne mai babbar mai
shigar da ƙara ta ICC Fatou Bensouda ta ce za ta yi bincike kan Boko Haram da
sojojin Najeriya kan cin zarafi da laifukan yaƙi da aka aikata a shekarun da
aka kwashe na rikicin Boko Haram.
Sai dai a sanarwar da wallafa a
shafinta na Facebook, rundunar sojin Najeriya ta ce wannan zai yi tasiri ga karya
ƙwarin guiwar sojoji.
“Babu shakka irin wannan bayani
na tunzurawa na iya janye hankalin sojojin Najeriya saboda tasirinsa na karye
masu ƙwarin guiwa. Zai haifar da mummunan tasiri ga ƙwarin guiwar da sojojin
suke da shi da kuma aikin soja ga ƴan Najeriya da haifar da koma-baya ga
dukkanin ayyukan tsaro a ƙasar.”
Sai dai sanarwa ta ce babban
hafsan sojin ƙasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi kira ga sojojin su yi
watsi da abin da ya kira abin da zai ɗauke hankalinsu tare da yin kira ga
sojojin kada su damu ko karaya da matakin.
Rundunar ta ce matakin ICC na
zuwa ne bayan rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International
ta fitar tana neman a gudanar da bincike kan “ta’asar da sojojin Najeriya suka
aikata.”
Fatou Bensouda ta ce ofishinta ya kammala nazari sannan ya gano wasu bayanai cewa ƙungiyar ta Boko Haram da sauran ɓangarorinta da suka ɓalle masu kaifin kishin Islama sun ci zarafin bil’adama.
Laifukan sun hada da kisa da fyaɗe da auren dole da kuma azabtarwa.
Bensouda ta kuma ce binciken da za ICC za ta gudanar ya shafi har da sojojin Najeriya da ƴan sanda.