Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Jami'ar Amurka ta nuna takaicinta kan 'yaudarar' da aka yi wa Ganduje

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur

    Gwamnatin Najeriya ta rage farashin man fetur da naira biyar biyo bayan matsin lamba daga haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago.

    Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wata ganawa da ƙungiyoyin NLC da TUC a daren jiya Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa.

    Ya ce an rage farashin ne daga N168 zuwa N162.44 kan kowace lita ɗaya, wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Disamba.

    Ana sayar da man kan N168 yanzu haka biyo bayan matakin da 'yan kasuwa suka ɗauka na ƙara farashin daga N147.67 zuwa N155.17 a watan Nuwamba. Ƙara ya biyo bayan matakin kamfanin da ke kula da kasuwancinsa na ƙara wa 'yan kasuwar farashi.

    Chris Ngige ya ce an kafa wani kwamitin bincike da zai daidaita farashin man, yana mai cewa zai gabatar da rahotonsa ranar 25 ga watan Janairu.

    "Tattaunawarmu ta yi armashi kuma NNPC, wanda shi ne babban kamfanin mai, da 'yan kasuwa sun amince cewa za a rage farashin man da N5 kuma ragin zai fara aiki ne daga Litinin mai zuwa," in ji Ngige.

  2. Shugaba Nana Akufo-Addo ne kan gaba a zaɓen Ghana

    Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u bayan zaɓen shugaban ƙasar Ghana da na 'yan majalisa.

    Sakamakon farko-farko ya nuna cewa Shugaba mai-ci Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP ne ke gaban abokin hamayyarsa na NDC, tsohon Shugaba John Mahama.

    Kazalika, rahotanni sun bayyana cewa NPP ce kan gaba a zaɓen 'yan majalisa, amma NDC ta yi watsi da sakamakon.

    Akasarin zaɓen na jiya Litinin ya gudana cikin kwanciyar hankali, sai dai an samu wasu mutum biyu da aka jikkata sakamakon harbin bindiga.

    Mutum miliyan 17 ne, waɗanda ke da rajistar zaɓe, ake sa ran sun kaɗa ƙuri'a.

  3. Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Joe Biden ya zaɓi baƙar fata a matsayin sakataren tsaro

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce zaɓaɓɓen Shugaba Joe Biden ya zaɓi wani janar ɗin soja mai ritaya kuma baƙar fata, Lloyd Austin, a matsayin sakataren harkokin tsaronsa.

    Idan aka tabbatar da shi, Janar Austin zai kasance bakar-fata na farko Ba'amurke da zai jagoranci ma'aikatar tsaro ta Pentagon.

    Shawarar Mr Biden na zuwa ne mako biyu da sanar da wasu manyan mambobin da zai yi aiki da su a kwamitin harkokin tsaron ƙasa.

    Sai dai Wakilin BBC ya ce tabbatar da Lloyd Asutin a majalisa na iya kasancewa mai sarƙaƙiya duba da cewa ƙasa da shekara baƙwai da suka gabata ya yi ritaya don haka zai buƙaci alfarma na musamman.

  4. Labarai cikin minti ɗaya

  5. Sakamakon zaɓen Ghana

    Tun da ƙarfe 5:00 na yammacin jiya Litinin aka rufe jefa ƙuri'a illa waɗanda ke kan layi lokacin ya riske su.

    Yanzu hankali ya bar rumfunan zaɓe kuma ya koma kan cibiyoyin tattara sakamako, inda aka tattara ƙuri'un da aka kaɗa a cibiyoyin tattara sakamako da ke yanki 16 na ƙasar.

    Shugbar hukumar zaɓe ta ce za su faɗi sakamakon cikin awa 24 bayan kammala jefa ƙuri'a.

    Jam'iyya mai mulki ta National Patriotic Party ta yi iƙirarin zarta jam'iyyar adawa a nata lissafin, inda ta ce ta samu kashi fiye da 50 cikin 100.

    A gefe guda kuma, 'yan sanda sun kama ma'aikatan hukumar zaɓe biyu da aka zarga da ɓata takardun zaɓen shugaban ƙasa a Awutu Senya West da Bawku.

    Kazalika, 'yan sandan sun tabbatar cewa an harbi mutum biyu a Awutu Senya East.

  6. Ƴan adawa sun yi zargin maguɗi a zaɓen Ghana

    Jam'iyyar adawa ta NDC ta John Dramani Mahama a Ghana ta yi zargin maguɗin zaɓe, yayin da ake dakon fitar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisa. da aka gudanar jiya Litinin.

    Duk da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyyar hankali a mafi yawan wurare, an samu wasu lamuran tashin hankali da zarge-zargen yin magudi nan da can.

    Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya iske yadda ya ga wani ya yi ƙoƙarin yin cushe, sai dai jami'an tsaro sun cafke shi.

    Kusan a galibin wurare da aka yi yunƙurin yin cushe ƙuri'u ne da aka dangwala wa jam'iyya mai mulki ta NPP, wanda hakan ya sa ƴan adawa suka farga.

    Kawo yanzu hukumar zaɓen ba ta ce komai ba, amma jam'iyyar NPP ɗin wadda aka yi yunƙurin yin cushen a madadinta ta musanta.

    Shi ma jami'in tsare-tsaren jam'iyyar a mazaɓar Menshiya ta Kudu, Abubakar Alhassan, ya shaida cewa sun samu labarin wannan batu amma gaskiya ba da sanin jam'yyarsu ba ne kuma ba shi ne karon farko da ake ganin hakan ba.

    Ya ce ko a zaɓukan baya ƴan adawa na iya yin komai domin ƙalubalantarsu ko amfani da wannan siga wajen haifar da tasgaro ga sakamakon zaɓen.

  7. An fara yi wa mutane riga-kafin korona a Birtaniya

    Wata dattijuwa mai shekara 90 daga Ireland ta Arewa ta zama ta farko da aka yi wa allurar riga-kafin cutar korona a Birtaniya.

    A yau Talata ne ƙasar ta zama ta farko a Yammacin Turai da ke soma amfani da allurar riga-kafin.

    Dubban ma'aikatan gidan kula da tsoffi da mazaunan gidan ne rukunnin farko na mutanen da za a yi wa riga-kafin, wadda kamfanin Pfizer da BioNTech suka samar.

    A makon da ya gabata hukumomin lafiya a Birtaniya suka amince da buƙatar gaggawa na soma yi wa mutane riga-kafin.

    Mutanen da gwamnati ta fi bai wa mahimmanci su ne tsofaffi da marasa galihu da kuma ma'aikatan lafiya a matsayin mutanen farko da za a yi wa allurar.

    A cikin mako mai zuwa ake sa ran sauran ƙasashen duniya za su fara amfani da rigakafin.

  8. Assalamu Alaikum

    Barkanku da hantsin Talata, tare da fatan kun tashi lafiya.

    Za ku kasance da niUmar Mikaildomin kawo muku yadda take kasancewa a zaɓen shugaban ƙasar Ghana, wanda ake cigaba da ƙirga ƙuri'u.

    Za kuma mu kawo labarai daga sassan duniya musamman Najeriya da Nijar.