Za mu magance matsalolin tsaro - Buhari

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Awwal Ahmad Janyau

  1. Rufewa

    Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu gobe idan Allah ya kai mu inda za mu shafe yinin Laraba muna kawo labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Za ku iya zuwa har ƙasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya a yinin Talata.

  2. Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa

    Bayanan sautiLabarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 17/11/2020
  3. Trump zai sake janye dakarun Amurka a Afghanistan da Iraƙi

    Trump a Afghanistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da cewa Shugaba Trump zai kara rage yawan sojojin ƙasar a Afghanistan da Iraƙi yayin da yake kan karagar mulki.

    Yawan dakarun da ke Afghanistan sun kusan kai rabin 2500 daidai adadin sojojin da za su ci gaba da zama a Iraƙi bayan rage yawansu.

    A watan Janairu ya kamata a kammala janye dakarun kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Joe Biden.

    Masu sukar lamirin sun ce wannan za ta iya yin illa ga tsaro a Afghanistan da tattaunawar da gwamnatin Kabul ke yi da Taliban.

    A baya, Sakatare Janar na ƙungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya yi gargaɗin cewa gaggauta ficewar sojojin Amurka zai ƙara jefa Afghanistan cikin hatsarin zama cibiyar ƴan ta’adda a duniya.

  4. An yanke wa wasu mata uku ƴan Najeriya hukuncin ɗauri a Rasha

    An yanke wa wasu mata uku 'yan Najeriya hukuncin dauri a gidan yari a kasar Rasha, wadanda aka kama da laifin ingiza wata yarinya mai kananan shekaru cikin harkar karuwanci a kasar ta Rasha.

    Wannan hukunci dai yana zuwa ne yayin da wata kotun da ke garin Oshogbo na jihar Oshun, ta yanke irinsa kan wata mata, bisa laifin safarar wata yarinyar zuwa kasar waje.

    'Yan Najeriyan da hukuncin ya rutsa da su a kasar Rasha, sun kunshi wasu mata biyu ne, 'yan uwan juna. Vivian Omo-yem-wen Ehiozee, mai shekara 31, da Endurance Ehiozee, mai shekara 37, wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekara 14 a jarun.

    Sai kuma mahaifiyarsu, Helen Ehiozee, mai shekara 54, wadda aka yanke wa hukuncin daurin shekara 10.

    Hukumar hana fataucin bil'Adama ta Najeriya, wato NAPTIP, ta bi diddigin wannan shari'a.

    Masu sharhi kan al'amura dai na ganin zartar da hukuncin dauri, maimakon bayar da zabin biyan tara, kan masu safarar bil'Adama, wani abu ne da zai zama kakkausan ''gani ga wane'', kuma ya taimaka matuka gaya, wajen dakile wannan matsala mai tangan da wata annoba a duniya.

  5. Abin da Buhari ya tattauna a taron majalisar ƙoli kan harkar tsaro

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki duk matakin da ya cancanta domin magance matsalolin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

    Shugaban na magana ne yayin taron majalisar koli kan harkokin tsaro ta kasar da ya jagoranta.

    Gwamnati kuma ta ce za ta dauki matakan gyara al'amurra da zimma tabbatar da ba a koma samun wata tarzoma a kasar ba irin wadda aka yi a watan jiya ta EndSARS.

    Bayan kammala taron, BBC ta tattauna da Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman kan watsa labarai ga shugaban domin jin makasudin kiran taron.

    Bayanan sautiHirar Haruna Shehu Tangaza da Malam Garba Shehu
  6. Babu jirgin da aka harbo a arewa maso gabashin Najeriya - UNOCHA

    Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an harbo wani jirgi mai saukar angulu da ke ɗauke da mutane a ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno.

    UNOCHA ta ƙaryata labarin a shafinta na Twitter inda ta ce babu wani jirgin da aka harbo ko ya yi hatsari a arewa maso gabashin Najeriya.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƴan Boko Haram sun harbo jirgin kusa da garin Banki tare da cewa ana tunanin mutum biyar sun mutu, amma daga baya jaridar ta ce labarin ba haka ba ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Shin tsaron hanyar Kaduna zuwa Abuja ya gagari gwamnatin Buhari ne?

    Tare hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu 'yan bindiga masu satar mutane suka yi a ƙarshen mako inda suka sace mutane da dama sannan suka kashe wasu, ta sake tayar da hankalin jama'a musamman waɗanda ke yawan bin hanyar.

    Ganau sun ce 'yan bindigar sun tare hanyar ce da yammacin ranar Lahadi, inda suka kwashe tsawon lokaci suna harbe-harbe lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 15.

    Kazalika, 'yan bindigar sun sace mutane da dama wadanda har yanzu ba a kai ga sanin adadinsu ba.

    Sai dai a sanarwar da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ta ce mutum biyu ne suka mutu sakamakon harbe-harben da 'yan bindigar suka yi, tana mai cewa jami'an tsaro sun ceto mutum tara daga cikin wadanda aka sace.

    Ku latsa nan don karanta cikakken labarin:

    taswirar babban titin Kaduna zuwa Abuja
  8. Gwamnan Ebonyi ya koma jam'iyyar APC

    Gwamna DAVID UMAHI:

    Asalin hoton, DAVID UMAHI:

    Gwamnan jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya David Umahi, ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC ta shugaba Buhari

    "Na bar PDP saboda rashin adalci," kamar yadda gwamna Umahi ya tabbatar da labarin ficewarsa ga mutanen Abakaliki babban birnin Ebonyi .

    An ta jita-jitar cewa gwamnan zai fice daga PDP, inda wasu ke cewa yana shirin fitowa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APC.

  9. Saliyo da Najeriya sun tashi babu ci a Freetown

    An tashi wasa babu ci tsakanin Super Eagles na Najeriya da kuma ƴan wasan ƙasar Saliyo a wasan neman gurbin gasar cin kofin Afirka.

    A karawa ta farko a birnin Benin na Najeriya ƙasashen sun tashi ne 4-4.

    Sai da Najeriya ta ci 4-0 daga baya Saliyo ta farke kwallayen.

    Najeriya ce ta jagoranci rukuninsu da maki 8, a wasanni huɗu da ta buga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. UNESCO ta sa gasar sake gina masallacin Mosul da IS ta tarwatsa

    Masallacin Mosul

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kare al'adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya Unesco ta kaddamar da wata gasa ta duniya kan sake gina masallacin Mosul mai tsohon tarihi , wanda mayaƙan IS suka tarwatsa.

    Hukumar ta sa gasar ne ga masu fasahar zanen gini da injiniyoyi na duniya waɗanda ta buƙaci su gabatar da tsarinsu na sake gina masallacin ciki da wajensa.

    A 2017 ne IS ta tarwatsa masallacin na Mosul a Iraƙi kafin dakarun Iraƙi su kore su daga yankin.

    Masallacin wanda aka bayyana ya haura shekara 800 a nan ne shugaban IS Abubakar Baghdadi ya taɓa yin huɗuba.

    An buƙaci masu sha'awa sake gina masallaci su shigar da tsarin zanen da ya dace da tsarin ginin masallacin na asali.

  11. Najeriya na fafatawa da Saliyo

    Najeriya na fafatawa da Saliyo a yanzu haka, a wasan neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka

    An tafu hutun rabin lokaci babu ci a wasan da ƙasashen biyu ke kece raini a Free Town.

    A karawa ta farko Saliyo ta rike Najeriya ne ci 4-4.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. An kusa kammala shirin zaɓen Nijar - CENI

    Hukumar zaɓe ta jamhuriyyar Nijar CENI, ta ce shirye-shiryen zaɓen ranar 13 ga watan Disamba har ma da sauran zaɓuɓɓukan sun kusa kammala.

    A wata tattaunawa da mataimakin shugaban hukumar zaɓen Aladoua Amada ya yi da wakiliyarmu Tchimma Illa Issoufou a Yamai, ya ce abun da ya rage musu bayan sun kammala kai katin zaɓen a faɗin ƙasar shi ne na buga takardun zaɓen masu ɗauke da hotunan duka ƴan takarar, shi kuma suna jiran kotun tsarin mulki ne ta gama amincewa da ƴan takarar.

    Maitaimakin shugaban hukumar zaɓen ya fara da bayyana mata cewa tuni suka kai katunan zaben duk inda ya dace.

    Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirar tasu:

    Bayanan sautiHira da mataimakin shugaban hukumar zabe a Nijar Aladuawa Amada
  13. Mutum shida sun mutu a harin bam a kantin cin abinci a Mogadishu

    somali bomb

    Asalin hoton, AFP

    Mutum shida ne suka mutu wasu biyar kuma suka jikkata bayan da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a wani kantin cin abinci mai yawan hada-hadar ja,a'a a kusa da Mogadishu babban birnin Somaliya.

    Mayaƙan Al-Shabab sun ce su ne suka kai harin wanda ya faru da tsakar ranar Talata. Cikin waɗanda suka mutun har da ɗan ƙunar baƙin waken da sojoji biyu.

    Ana iya hango hayaƙin da ya turnuƙe sararin samaniya a lokacin da motocin asibiti suke ƙoƙarin isa wajen a gundumar Hamar Jajab da ke kusa da tashar jiragen ruwa.

    Harin na zuwa ne bayan da rundunar sojin Somaliya ta ce ta kama wasu manyan kwamandojin a--Shabab a wani harin soji da aka kai yankin Hiraan da ke tsakiyar ƙasar.

    Ƙungiyar ta'addancin tana yawan kai hare-haren bam a Mogadishu da wasu wuraren a Somaliya a wani ƙoƙarinta na kifar gwamnatin ƙasar.

  14. Wasu ɓata gari na yin damfara da sunan Ali Ƙwara - Danginsa

    Wasu makusantan fitaccen mai kama ƴan fashi da makamin nan da ya rasu a makon da ya gabata Ali Ƙwara, sun nesanta mai gidan nasu da mutanen da suka kira ƴan damfara da ke zagayawa suna karɓar kuɗaɗe a hannun wasu bayin-Allah da sunan marigayin ne ya ba su laƙani.

    Nazif Babaji Aliyu, wani makusancin marigayin ne kuma hadiminsa, a hirarsu da Zahraddeen Lawan a Kano ya ce ba su yi mamakin irin waɗannan mutane ba kasancewar tun lokacin da Ali Ƙwara yana raye akwai waɗanda ma ke ikirarin cewa su ne shi.

    Sai dai ya ce ba da yawun su ake wannan al’amari ba.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron hirarsa da Zahraddin Lawan:

    Bayanan sautiHira da Nazif Babaji ɗan uwan Ali Kwara
  15. Janye dakarun Amurka daga Iran zai iya yin mummunar illa - NATO

    Jens Stoltenberg

    Asalin hoton, AFP

    Sakatare Janar na Ƙungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya yi gargaɗin cewa yadda Amurka ta yi gaggawar janye dakarunta daga Iran ba tare da bin tsari ba zai iya yin mummunar illa.

    Kalamansa na zuwa ne bayan rahotannin da aka samu cewa Shugaba Trump na shirye-shiryen ƙara rage sojojin Amurka a ƙasar.

    Cikin wata sanarwa, Mista Stoltenberg ya ce Afghanistan ta sake yin kasadar zama wani dandali ga masu tayar da ƙayar baya su shirya hare-hare.

    Ya ce ƙasashe mambobin NATO sun shiga Afghanistan tare a don haka ya kamata su fice lokaci guda cikin tsari.

  16. Iran ta ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta idan ta kai mata hari

    Khomeini

    Asalin hoton, AFP

    Wani mai magana da yawun gwamnatin Iran ya ce Amurka za ta ɗanɗana kuɗarta matuƙar ta kai wa Iran hari.

    Ya faɗi hakan ne bayan da aka ruwaito cewa a makon da ya gabata, Shugaba Trump yana tunanin kai hari kan babbar cibiyar nukiliyar Iran.

    Mai magana da yawun gwamnatin Iran ya ce "wataƙila akwai yunƙurin kai wa Iran hari amma fa wannan ra'ayina ne ba na mai magana da yawun gwamnati ba.

    "Ni a karan kaina ba na hasashen faruwar hakan. Ba na ganin akwai yiwuwar za su so haifar da matsalar tsaro a duniya da kuma yankin," in ji shi.

    Kalaman na Ali Babei wanda aka wallafa a shafin intanet mallakin gwamnatin Iran na zuwa ne bayan wani rahoto da jaridar New York Times ta buga da ke cewa Mista Trump ya nemi manyan mataimakansa kan sha'anin tsaron ƙasa su yi masa ƙarin bayani game da zaɓin da ake da shi, da kuma yanayin da za a iya kai wa Iran hari.

    An bayar da rahoton cewa a ƙarshe Trump ɗin ya yanke shawarar dakatar da aniyarsa saboda haɗarin ruruwar rikici a Gabas Ta Tsakiya.

  17. Labarai cikin minti ɗaya

    Latsa hoton da ke ƙasa domin sauraron Minti Daya Da BBC na Rana 17/11/2020 tare da Nasidi Adamu Yahaya da Bilkisu Babangida.

    Bayanan sautiMinti Ɗaya da BBC na Rana 17/11/2020
  18. An ɗage haramcin sauka a Najeriya kan wasu kamfanonin jirgin ƙasashen waje

    Lufthansa

    Asalin hoton, @lufthansa

    Gwamnatin Najeriya ta ɗage haramcin da ta saka wa kamfanonin jigin Lufthansa da Air France da Qatar Airways na sauka a ƙasar.

    Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika ne ya sanar da hakan cikin wani saƙon Twitter a yau Talata.

    Kazalika, ministan ya nuna cewa akwai yiwuwar sake buɗe filayen jirgin sama na Kano da Enugu da Fatakwal kafin shekara ta ƙare.

    "Muna tattaunawa da Ma'aikatar Lafiya da CACOVID da PTF domin buɗe filayen jirgi na Kano da Fatakwal da Enugu kafin ƙarshen shekara," in ji ministan.

    "Kuma an bai wa Lufthansa da Air France/KLM damar cigaba da ayyuka. An sahale wa Qatar Airways ya fara sauka a Abuja."

    Kwamitin yaƙi da cutar korona ya haramta wa kamfanin zirga-zirgar jirage guda 10 shigowa Najeriya a watan Satumba bayan an ci gaba da harkokin sufuri na ƙasashen waje sakamakon annobar korona.

    A loƙacin, Hadi Sirika ya ce an haramta mausu sauka ne saboda "an hana masu bizar yawon shaƙatawa shiga ƙasashen kamfanonin".

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Pakistan za ta 'daina amfani da kayan Faransa' saboda zanen ɓatanci

    Pakistan

    Asalin hoton, EPA

    Wata ƙungiyar addinin Musulunci ta ce ta dakatar da zanga-zangar neman a ƙaurace wa amfani da kayan Faransa saboda gwamnatin Pakistan ta goyi bayan zanga-zangar tasu.

    An yi ta zanga-zangar ne bayan Faransa ta kare zanen ɓatanci da wata mujallar ƙasar ta yi wa Annabi Muhammadu SAW.

    Shugaba Macron ya kare tsarin ƙasarsa na ba ruwanta da addini yayin hatsaniyar da ta jawo fille kan wani malamin makaranta saboda ya nuna wa ɗalibansa hotunan zanen a cikin aji.

    Hakan ya jawo ɓacin rai daga ƙasashen Musulmin duniya.

    Mambobin ƙungiyar ta Tehreek-e-Labaik Pakistan (TLP) sun fito da takardu ɗauke da saka hannun ministocin gwamnati biyu.

    Sai dai Pakistan ba ta ce komai ba a hukumance zuwa yanzu game da kiran ƙaurace wa kayayyakin Faransar.