Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kalaman Trump sun raba kan 'yan Republican

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. An rantsar da sabbin alƙalan kotun ƙolin Najeriya

    Alƙalin alƙalan Najeriya Tanko Muhammad ya rsantsar da sabbin alƙalai takwas na kotun ƙoli, abin da ya ƙara yawansu zuwa 20 daga 12.

    Alƙalan sun hadar da Lawal Garba daga shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, da M M Sulawa daga shiyyar Arewa maso yamma, da Helen Ogunwumju daga shiyyar kudu maso yamma, da Abdu Aboki daga shiyyar Arewa maso yamma.

    Sauran su ne Adamu Jauru, daga yankin Arewa maso gabas, da Samuel Oseji daga kudu maso kudu, da Tijjani Abdulkadir daga Arewa maso gabas, da Emmanuel Agim daga kudu maso kudu.

  2. Za a ƙara yawan jami'an da ke bai wa Joe Biden kariya

    Rundunar bayar da kariya ta musamman a Amurka ta soma shirin ƙara yawan jami'an da ke tsaron lafiyar Joe Biden, daga ranar Juma'a yayin da ɗan takarar ke kan hanyarsa ta lashe zaɓen shugaban ƙasa.

    Jaridar Washington Post ta ce za a ƙara yawan jami'an da ke bai wa Mista Biden kariya, bayan da kwamitin yaƙin neman zaɓensa ya shaida wa rundunar cewa zai gabatar wa al'ummar kasar muhimmin jawabi.

    Jaridar ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar Catherine Milhoan ta ƙi cewa komai dangane da batun, tana mai cewa hukumar ba ta tattauna batun tsaro ga manyan mutane.

    Har ila yau, masu taimakawa Biden ba su ce komai dangane da batun ba,

  3. Trump na iya lashe zaɓen Amurka

    Har yanzu shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican na da damar iya lashe zaɓen shugaban Amurka da ake shirin sanar da wanda ya samu nasara.

    To sai dai da kamar wuya hakan ta tabbata, domin yana buƙatar lashe mafi yawa daga jihohin da suka rage, ciki har da waɗanda Biden ke kan gaba a yanzu haka.

    A yanzu dai shugaba Trump na da ƙuri'un wakilai masu zaɓe 214 yayin da Biden ke da 253 don haka dole ne Trump ya lashe jihohin da suka haɗar da Pennsylvania in da Biden ke kamo shi a yawan ƙuri'u, da jihar Arizona inda yanzu haka Biden ke kan gaba, da Nevada da Georgia da North Carolina da Alaska.

    Wannan ita ce dama ɗaya tilo da Trump ke da ita, yayin da shi kuma Biden ke da damarmaki da dama.

  4. Jihohi huɗu da za su tantance shugaban Amurka

    Fafutukar lashe zaben shugaban Amurka ta gangaro zuwa jihohi huɗu da ake ci gaba da ƙirga ƙuri;unsu, bari mu nuna muku yadda abin yake.

    (1) GEORGIA - Ƙuri'un wakilan masu zabe 16

    Halin da ake ciki : Trump na kan gaba, amma Biden na kamo shi sannu a hankali.

    Kuri'u nawa ne suka rage? : Akala dubu goma sha biyar, kuma yawancinsu a guraren da Joe Biden ke da tasiri.

    (2) PENNSYLVANIA - Ƙuri'un wakilan masu zaɓe 20.

    Halin da ake ciki : Trump na kan gaba, amma a nan ma Biden na rufe tazarar, abin mamakin shine yadda kwanaki biyu da suka gabata Trump ya yi wa Biden fintinkau da kuri'u sama da rabin miliyan, amma yanzu tazarar bata wuce dubu15 ba.

    Kuri'u nawa ne suka rage? : Akwai fiye da ƙuri'a dubu dari biyar da suka rage, sannan yawancinsu a wuraren da Biden ke da rinjaye.

    (3) ARIZONA - Ƙuri'un wakilan masu zaɓe 11.

    Halin da ake ciki : Biden na kan gaba da ƙuri'a dubu arba'in da bakwai, amma Trump na rage tazarar sannu a hankali.

    Kuri'u nawa ne suka rage? :Akwai akalla kuri'u dubu dari hudu da saba'in da suka yi saura, don haka ba mamaki Trump ya ci gaba da rufe tazarar dake tsakaninsa da Biden.

    (4) NEVADA - Ƙuri'un wakilanmasu zaɓe shida

    Halin da ake ciki : Biden na kan gaba da aƙalla ƙuri'u dubu sha biyu, sannu a hankali adadin na ci gaba da karuwa.

    Kuri'u nawa suka rage ? : Akala ƙuri'u dubu rari da casa'in a cewar hukumomi, yawancinsu a inda Democrat da Joe Biden ke da tasiri.

  5. Rashin abinci mai gina jiki ne ke sa yara a ƙasashe masu arziki ke fin tsayin kafa

    Wata ƙungiyar masana kimiyya ta duniya ta ce rashin abinci mai gina jiki wani ɓangare ne da ke haifar da gibi mai na tsayin centimita ashirin tsakanin matasa daga ƙasashe masu arziki da matalauta.

    Masu binciken karkashin jagorancin kwalejin Imperial dake Landan, sun yi nazarin bayanai daga yara miliyan sittin da biyar a cikin shekaru talatin.

    Sun gano cewa tsayin yaro dan shekara goma sha uku a Netherlands dai-dai yake da na ɗan shekara goma sha tara a Timor-Leste da Laos.

    Masana kimiyyar sun ce yawancin manufofin kiwon lafiya na duniya sun fi mayar da hankali ne kan taimakawa ƴan kasa da shekara biyar, amma ya kamata a kara himma don tabbatar da cewa yaran da suka manyanta sun sami abincin da suke bukata.

  6. An yankewa maharin da ya kashe wata mata a Faransa hukunin daurin rai da rai.

    Wata kotu a Faransa ta zartar da hukuncin ɗaurin rai da rai a kan maharin nan da ya harbe wata mata yayin da yake shirin kai hari wata coci.

    Sid Ahmed wanda ɗan asalin Aljeriya ne ya gurfana a gaban kotun dake Paris a matsayin ɗan tada ƙayar baya da ya tuba bayan da masu iƙirarin jihadi suka yaudare shi tare da sauya masa tunani a ƙasar Siriya.

    Kotun ta bada umarnin tsare shi tsawon shekaru goma 22 a gidan maza, kafin daga bisani a mayar da shi ƙasarta ta asali

  7. Sudan ta rufe iyakokinta da Habasha

    Kasar Sudan ta rufe iyakokinta da Kassala dake gabashin kasar Habasha, biyo bayan karuwar tashin hankali tsakanin hukumomin tarayyar Habasha da yankin Tigray, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito.

    Gwamna Fateh al-Rahman al-Amin ne ya sanar da hakan inda ya ce za a ci gaba da rufe iyakar har sai wani lokaci,

    Gwamnan ya ce zai yi tattaki zuwa garin Wad Al Helew, wani kauye a cikin jihar Kassala da ke kan iyaka da Habasha da Eritriya, domin tantance halin da ake ciki.

    Ya jaddada cewa hukumomin Sudan ba za su kyale wasu mutane ko kungiyoyi su shigo jihar da makamai ba.

    Za kuma a kafa wani kwamiti da zai duba yadda za a yi hulda da fararen hula wadanda za su iya neman mafaka a Sudan.

    A jiya ne Firai ministan Sudan, Abdalla Hamdok ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Habasha Abiy Ahmed, inda ya ce baya jin daɗin abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan.

  8. Zargin shirga ƙarya ya sa kafofin watsa labaran Amurka katse jawabin Trump

    Kafofin yaɗa labaran Amurka da dama sun katse jawabin da shugaba Donald Trump yake gabatarwa kai tsaye kan zaben ƙasar.

    Tashohi irinsu ABC da CBS da NBC duk sun yanke jawabin da suke haskawa.

    Sun shaida wa masu kallonsu cewa shugaban na sharara karya a sanarwar da yake yi.

    Wakilansu na cewa shugaban na son haddasa rudani ta hanyar shaida cewa akwai maguɗin zaɓe a kuri'un da aka kada ta gidan waya.

    Wakilin BBC yace shugaban na wadanan zarge-zarge ba tare da gabatar da hujja ba, ya yi korafin cewa ana aringizo da magudi, kuma wadanda aka tura wa katin zabe har da wadanda suka mutu da wadanda suka bar ƙasar.

  9. Trump ya ruga kotu yayin da Biden ke kan hanhyar samun nasara

    Donald Trump da abokin hamayyarsa ta Democrats, Joe Biden kowanne su ya gabatar da jawabi ga Amurkawa yayin da hankula suka karkata kan sauran jihohin da yanzu ake fafatawa dan kammala sanin sakamakon zaben.

    Mista Trump ya sake korafin magudin zabe, ba tare da bayyana wasu shaidu ko hujja ba.

    A wani jawabin daya gabatar a Fadar white House, ya yi korafi cewa an sace kuri'unsu ta haramtattun kuri'u.

    A jihohin Pennsylvania da Georgia, Trump nasararsa ta soma tangal-tangal bayan soma kidaya kuri'un da aka kada ta akwatin gidan waya.

    Shi kuwa abokin hamayyarsa, Joe Biden ya dage kan cewa komai na tafiya daidai a kidayar.

    A wani sakon talabajin dan takarar ta Democrats ya bukaci a kwantar da hankula da sake haƙuri.

  10. Buɗewa

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiya da fatan kun wayi gari lafiya.

    Imam Saleh ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi da muke kawo muku labarai kai tsaye, da fatan za ku kasance da mu don jin halin da duniya ke ciki musamman dangane da zaben shugaban Amurka da ake dakon sanar da wanda ya samu nasara.

    Za kuma mu rika sanar da ku halin da ake ciki a Najeriya da Nijar.