Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Mala'iku za su taimaka wa Trump ya ci zaɓe'

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan zaben Amurka da ma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh, Mustapha Musa Kaita and Halima Umar Saleh

  1. ''Mun ninka harajin da muke samu a jihar Kaduna''

    Gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufa'i, ya ce jihar ta tara harajin da yawansa ya kai Naira kusan Naira biliyan 45 a shekarar 2019.

    Hakan na nufin cewa jihar ta samu harajin da ya haura ninki biyu na abin da ta samu a shekarar 2016, wato shekaru huɗu da suka gabata, wato Naira Biliyan 23.

    Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce hakan zai bawa gwamnatinsa damar aiwatar da ayyukan raya ƙasa da jama'a za su mora.

    ''Muna samun ƙaruwar haraji sannu a hankali cikin shekaru hudu da suka gabata, sannan samar da tsarin asusun ajiyar bai ɗaya na VAT ya taimaka ƙwarai wajen samun wannan nasara'' in ji gwamnan.

  2. Za mu nemi ƙasashen Turai su sanya ƙafar wando ɗaya da Turkiyya – Faransa

    Faransa ta ce za ta kai ƙarar abokiyar kawancenta a ƙungiyar NATO wato Turkiyya ƙara gaban kungiyar tarayyar turai don ƙaƙaba mata takunkumi.

    Faransan ta ce za ta buƙaci daukar wannan mataki ne a yayin taron ƙoli na ƙungiyar da za a yi a watan gobe.

    Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya faɗa wa wani gidan rediyon Faransa cewa kalaman Shugaba Recep Tayyip Erdogan na baya-bayan nan game da Faransa sun janyo tashin hankali da kyara da cin zarafi.

    Ya ce ya rage ga mambobin ƙungiyar EU su dauki matakan da suka dace.

    Shi dai shugaba Erdogan ya ce takwaransa na Faransa Emmanuel Macron na bukatar a duba kwakwalwarsa, saboda kalaman da yayi na kare zanen barkwancin Annabi Muhammad, abin da ya janyo ɓacin rai ga musulmai da dama.

  3. An yi jana'izar yara ƴan makaranta da mahara suka kashe a Kamaru

    An yi jana'izar wasu yara ƴan makaranta bakwai da mahara suka kashe a kudu maso yammacin Kamaru.

    Hukumomin yankin sun ɗora alhakin harin a kan ƴan awaren yankin renon Ingilishi, duk da cewa sun musanta hannu.

    Ƴan bindigar sun auka wa makarantu da dama a ƴan makonnin nan a dai-dai lokacin da suka fara buɗewa bayan kullen korona.

    Kisan daliban masu shekaru tsakanin goma sha biyu zuwa sha hudu ya haifar da matukar damuwa da fushi a Kamaru.

    Firai minista, Joseph Ngute, na halartar jana’izar ne a daidai lokacin da gwamnati ke fuskantar kakkausan suka kan gazawarta na kare daliban.

    Mahukunta sun ce a cikin wannan makon ne kawai wasu ƴan bindiga suka kai hari makarantu huɗu kuma har yanzu ba a ga malamai goma sha daya ba bayan sace su a gaban daliban su a arewa maso yammacin kasar ranar Talata.

  4. Zanga-zanga ta ɓarke a Amurka yayin da ake dakon sakamako

    Zanga-zanga ta ɓarke a wasu biranen Amurka yayin da ake dakon sanin wanda ya lashe zaben shugaban ƙasa.

    Zanga-zangar ta kasu kashi biyu, da waɗnda ke son a ci gaba da ƙirga ƙuri'a da kuma waɗanda ke son a dakatar, a daina, a kuma bayyana wanda ya samu nasara a haka.

    Dandazon mutane sun taru a titunan wasu daga cikin jihohin ƙasar kamar New York da Washington da Pennsylvania suna neman a ci gaba da ƙirga ƙuri'un da suka rage.

    Wasu kuwa sun taru a cibiyar ƙidaya ƙuri'u dake jihar Michigan, in da aka bayyana Biden a matsayin wanda ya lashe jihar.

    Da alama masu son a ci gaba da ƙrga ƙuri'a magoya bayan Joe Biden ne, yayin da magoya bayan Trump ke cewa a daina.

  5. Ƙungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun caccaki gwamnonin yankin

    Gamayyar ƙungiyoyin matasan arewacin Najeriya ta bayyana takaici game da taron gwamnoni da sarakuna da sauran manyan jagororin yankin suka yi a Kaduna.

    Matasan na ganin taron ya yi wasarairai da manyan matsalolin da ke addabar al'ummar yankin kamar tashin-tashinar matasa da rashin aikin yi, inda ya ɓuge da zanga-zangar EndSARS da kuma ƙorafi kan shafukan sada zumunta.

    A cewarsu taron ya gaza wajen yin ta-maza ya fayyace matsayinsa kan hare-haren da aka kai wa 'yan arewa waɗanda ba su ji, ba su gani ba a wasu yankunan kudanci.

    Ɗaya daga cikin jagororin matasan, Nastura Ashir Shariff, ya shaidawa BBC cewa abin takaici ne ace jagororin kudancin Najeriya na kwatowa al'ummar yankinsu haƙƙinsu, amma lamarin ba haka yake ba a Arewa.

  6. Ivory Coast na daf da faɗawa yaƙin basasa

    Tsohon shugaban ƴan tawaye da ke gudun hijira da kuma Firaminista a Ivory Coast, Guillaume Soro ya bukaci sojoji su shiga tsakani sakamakon rikicin da ake samu tun bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

    Mista Soro a sanarwar da ya fitar a shafin sada zumunta ya bukaci sojoji su dawo da doka da oda bisa kundin tsarin mulkin kasa.

    An haramta masa shiga takara saboda samun sa da laifin rashawa da kotu tayi a farkon wannan shekara.

    Wasu ƴan hamayya sun kauracewa zaɓen, lamarin da ya bai wa shugaba Alassane Ouattara damar sake nasara a karo na Uku da kuri'u sama da kashi 90 cikin 100.

    Jami'an tsaro sun killace gidajen manyan ƴan hamayyar da suka shiga takara Henri Konan Bedia da Pascal Affi N'Guessan.

  7. An rantsar da John Maghafuli a matsayin sabon shugaban Tanzaniya

    An rantsar da shugaba John Magafuli, a matsayin shugaban Tanzaniya a karo na uku, bayan lashe zaɓe mai cike da ruɗani.

    Shugaba Maghafuli ya samu kashi 84 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa jimlatan.

    Hukumar zaɓen Tanzania ta kare matakinta na sanar da sakamakon wanda ke shan suka daga ƴan adawa da masu sanya ido.

    Jama'a da dama sun taru a babban filin wasa na birnin Dodoma, inda shugaban ya karɓi rantsuwar kama aiki.

    Shugabannin ƙasashe goma sha biyu yawancisu na Afrika sun albarkaci taron da aka gudanar.

  8. An rufe guraren tsugunar da ƴan gudun hijira a Katsina

    Gwamnatin jihar Katsina a Najeriya ta sanar da rufe dukkan sansanonin da ta buɗe don tsugunnar da mutanen da rikici ya raba da gidajensu sakamakon hare-haren 'yan fashin daji.

    Hukumomi sun ce sun mayar da dubban mutanen zuwa garuruwansu ne, bisa hujjar ingantuwar harkokin tsaro a sassan Katsina.

    Sansanonin na ɗauke da sama da mutane dubu 27 a ƙananan hukumomin Andume da Faskari da ƙankara da kuma Jibiya.

    Shugaban kwamitin kula da ƴan gudun hijira na jihar ta Katsina Sani Aluyi Ɗanlami ya shaidawa BBC gwamnatin na daukar matakan yaki da ta'addanci da kan haifar da barazana a jihar.

    Jihar dai na ciki jihohin arewa maso yamma na Nijeriya da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da satar mutane don kuɗin fansa.

  9. Zaɓen Amurka : Me yasa kafafen yaɗa labarai ke bada mabanbantan sakamako ?

    Wataƙila a ruɗa ka idan kana ganin mabanbantan sakamako daga kafafen yaɗa labarai daban-daban game da sakamakon zaɓen shugaban Amurka..

    To dalilin shine wasunsu sun yi hasashen Joe Biden zai lashe jihar Arizona, wadda ke da ƙuri'un masu zaɓe 11.

    To sai dai mu a nan BBC muna ganin cewa har yanzu ya yi wuri mu kira jihohin da har yanzu ba'a kammala ƙoirga ƙuri'unsu ba.

    A wannan shekarar BBC na samun bayananta ne daga kamfanin dillacin labarai na Reuters, kai tsaye daga cibiyar binciken sakamako ta Edison.

    Zuwa yanzu an ƙirga kaso 85 cikin 100 na ƙuri'un jihar Arizona, kuma Joe Biden ne ke gan gaba da kashi 51 cikin 100 na ƙuri'un da aka lissafa zuwa yanzu.

    Abin da kawai za mu ce shine a ƙara haƙuri zuwa yanzu, a ci gaba da kasancewa da mu don sanin halin da ake ciki.

  10. Sarkin waƙa ya kwana a kurkuku

    Fitaccen mawaƙin Hausa Naziru Ahmad Sarkin Waƙa ya kwana a gidan yari a jihar Kano, bayan soke belin da aka bayar da shi da wata kotu a jihar ta yi.

    Ana ƙarar Naziru ne dai kan cewa ya saki wata waƙa ba tare da hukumar tace fina-finai ta Kano ta tantance ba.

    Sharuɗɗan sun haɗa da cewa sai ya kawo wani Maigari da zai tsaya masa da kuma Kwamandan Hizbah na ƙaramar hukuma a matsayin sharuɗɗan beli.

    Wani makunsancinsa ya ce sun cika sharuɗɗan, sai dai kuma ba a samu kai wa ga alƙalin da zai bayar da umarnin ba da belin ba.

  11. Dokar kullen korona ta fara aiki a wasu ƙasashen Turai

    Dokar kulle ta mako huɗu ta soma aiki a Burtaniya, yayin da kasashen Turai ke ƙoƙarin takaita yaduwar cutar korona bayan cutar ta ci gaba da yaduwa a zagaye na biyu.

    Dokar kullen ta shafi wuraren cin abinci da kuma shagunan da bana sayar da muhimman abubuwan amfani ba.

    Sai dai a wannan lokaci akwai wasu muhimman wurare da dokar bata shafa ba kamar makarantu saboda zasu kasance buɗe.

    Bayanai sun nuna cewa an samu mutum ɗari biyar da suka mutu bayan sun kamu da cutar korona a rana a 'yan kwanakin nan a Birtaniya, adadin da aka jima ba a samu ba tun watan Mayun da ya wuce.

    A can Poland kuma za a rufe sinimomi, da gidan adana kayan tarihi da shagunan sayayya daga ranar Asabar, bayan alkaluman mutane da ke kamuwa da cutar sun kusa dubu 24,700 a kullum.

    Akwai kuma yankunan Portugal da tun jiya Laraba suka shiga kulle.

  12. Aniyar ƴan Democrat ta karɓe majalisar dattawan Amurka ta gamu da cikas

    Fatan ƴan Democrats na samun gagarumar nasara a zabukan ƴan majalisa zuwa yanzu ya fuskanci gazawa.

    Jam'iyyar da ke sa ran ci gaba da iko da majalisar wakilai, a yanzu ta dan samu ragi a rinjaye.

    A bangaren majalisar dattijai, Susan Collins ta Republican ta kada abokin hamayyarta ta Democrat Sara Gideon.

    Yanzu haka Democrat na bukatar nasara a kujeru Uku domin cimma burinta na rinjaye a majalisa; zuwa yanzu dai tayi tazara da guda.

    Ana kuma kan kidaya kuri'u a yankuna da yanzu aka zura ido don hakan yada sakamakon zai kaya.

  13. Biden ya lashe jihar Michigan

    Ɗan takarar shugaban Amurka a ƙarƙashin jam'iyyar Democrat Joe Biden ya lashe jihar Michigan, dya daga cikin muhimman jihohin da ake kai ruwa rana a kansu.

    A jihar Wisconsin ma haka abin yake, Joe Biden ya lashe zaben jihar, ko da yake kwamitin yaƙin neman zaben shugaba Trump ya ce zai nemi a sake ƙidaya ƙuri'u.

    Har yanzu akwai sauran jihohi da sakamakon su ka iya sauya abin da ake gani yanzu - ko da yake jami'ai na gargaɗin cewa watakil a dau kwanaki kafin a sanar ko sanin sakamakon karshe.

    Tuni shugaba Trump ya ruga gaban kotu yana neman a dakatar da ƙirga sakamakon zabe a jihar Pennsylvania.

    Yanzu haka zanga-zanga ta barke a wasu sassan ƙasar, in da ake neman ganin an ƙidaya dukkanin ƙuri'un da aka kada.

  14. Buɗewa

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist

    Masu bibiyarmu a wannan shafi barkanmu da safiya da fatan kun wayi gari lafiya.

    Kamar yadda aka saba, mun shirya tsaf domin kawo muku labaran halin da duniya ke ciki, kama daga kan zaɓen shugaban Amurka da ake ci gaba da sanar da sakamakonsa, da kuma abubuwan da ke faruwa a sauran ƙasashen duniya ciki har da Najeriya da Nijar.

    Imam Saleh ke fatan za ku kasance tare da mu.