Zakzaky na nan a raye - IMN

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Nan ne muka kawo ƙarshen labarai da rahotanni da muke kawo muku a wannan shafi a kuma wannan rana ta yau.

    Ni Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu hadu a gobe idan rayuwa ta kai mu domin kawo muku wasu sabbin labarai da rahotannin.

  2. Za a fara tattaunawa tsakanin Sudan da Isra'ila

    GETTY IMAGES

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Ministan harkokin wajen Sudan ya ce kasar za ta tattana da Israel cikin makwani da ke tafe bayan cimma wata yarjejeniyar daidaita hulda tsakanin kasashen biyu.

    Wakilai za su tattauna kan yiwuwa kulla yejejniyoyi kan cinikayya, da shigi da ficen jama'a, da sufurin jiragen sama da kuma sha'anin noma.

    Isra'ila ta ce tuni ma ta dauki haramar aikewa da alkama da ta kai ta dala miliyan biyar ga wadanda ta kira 'sabbin kawayenta na Sudan''.

    Matakin daidaita hulda tsanin kasashen biyu wanda shugaban Amurka Donald Trump ya sanar, ya haifar da fushi a Sudan in da jam'iyyun siyasa suka yi watsi da yarjejeniyar suna masu cewa an tursasa wa gwamnatin Sudan ne.

    To amma wasu sun yi marhabin da yejejeniyar tare da cewa za ta ceto tattalin arzikin ƙasar da ke neman durkushewa.

  3. Zakzaky na nan a raye - IMN

    TWITTER/@SZAKZAKYOFFICE

    Asalin hoton, TWITTER/@SZAKZAKYOFFICE

    Kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a a Najeriya ta ce jagoranta Sheikh Ibraheem Zakzaky na nan a raye bai mutu ba.

    Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Ibrahim Musa ta ce, ya zama dole a gareta ta fito ta yi wa mutane bayanin kan jita-jitar da ake yaɗawa game da mutuwar jagoran nata.

    Cikin sanarwar kungiyar ta ce, ta yi imanin cewa wasu 'yan kanzagin gwamnati ne suke yaɗa wannan jita-jita domin ƙara jefa Najeriya cikin wani ruɗani.

    Sanarwar ta ƙara da cewa wani daga cikin iyalan Sheikh Zakzaky ya ziyarce shi a ranar Asabar 24/10/2020 a gidan yarin da ake tsare da shi a Kaduna.

    Kowa ya sani Sheikh na fama da rashin lafiya mai barazana ga rayuwa sakamakon raunukan da ke jikinsa, wanda wannan ba baƙon abu ba ne, in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa babu shakka wannan jita-jita ta fito ne daga gwamnati, da nufin ƙara gogawa kungiyar Harka Islamiyya ta 'yan Shi'a baƙin fenti, domin ƙara tayar da zaune tsaye.

    Haka kuma ta ce tunda gwamnatin shugaba Buhari ta bijirewa umarnin babbar kotun tarayya na asaki jagoranta a 2016, to duk abin da ya faru ga Sheikh gwamnatin za su ɗorawa alhaki.

  4. An sanya dokar hana fita a jihar Adamawa

    Others

    Asalin hoton, Others

    Gwamnatin jihar Adamawa ta sanya dokar hana fita biyo bayan lalata kaya da kuma yashe kayan abincin da ke cikin dakin ajiya na gwamnati da wasu ɓata gari suka yi.

    Cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sanda na jihar DSP Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar, rundunar 'yan sanda ta jihar ta shawarci mutane da su mutumta kansu su bi wannan doka, domin kare faruwar irin wannan ɓarna a jihar.

    Yayin da rundunar 'yan sanda ta jihar da sauran jami'an tsaro suka mutunta 'yancin al'ummar jihar, suna kuma shawartarsu da su guji aikata duk wani abu da zai iya jawo barazana ga tsaron jihar, in ji sanarwar.

    Haka kuma sanarwar ta ce babu yadda za a yi rundunar ta sanya idanu kan wasu ɓata gari suna aikata ɓarna ba tare da tsawatar musu ba, duk da cewa jami'anta sun yi aikinsu ta yadda ba a samu asarar rayuka ba yayin da suke hana satar da aka yi.

    An kuma kafa wani kwamitin hadin gwiwa na duka jami'an tsaro da za su riƙa zagaye domin tabbatar da cewa al'umma sun bi dokar kamar yadda aka sanya ta.

  5. An kashe mutane da yawa a wani harin bam a Afghanistan

    REUTERS

    Asalin hoton, REUTERS

    A kalla mutum 24 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka jikkata a wani harin bam da ya ritsa da su a wajen ginin cibiyar ilimi da ke Kabul, in ji hukumomin Afghanistan.

    Bam din ya fashe ne a cikin wani gini, wanda ɗalibai ke zuwa karatu ciki da yamma, in ji ministan cikin gida na kasar.

    Mabiya mazhabin Shi'a ne ke cika dakin karatun a al'adance.

    Tuni kungiyar IS ta yi ikirarin kai harin.

    Sai dai a wannan karon ba ta nuna hujjar da ke nuna ita ce ta kai harin ba a shafukan sada zumuntarta kamar yadda take yi a baya.

  6. Bayan shekara 43 jam'iyyar adawa ta ci zabe a Seychelles

    GETTY IMAGES

    Asalin hoton, GETTY IMAGES

    Jami'iyyar adawa ta karɓi shugabanci a Seychelles a karon farko tun 1997, bayan nasarar da ta samu a zaben shugabancin ƙasar.

    Wavel Ramkalawan ya doke shugaba Danny Faure da kaso 54.9% shi kuma yana da 43.5%, kamar yadda sakamakon hukumomi ya bayyana.

    A Victoria babban birnin ƙasar magoya bayan Mista Ramkalawan na ta murna.

    A bayanin da ya yi bayan nasararsa sabon shugaban ƙasar ya ce babu wani wanda ya sha kaye kamar yadda yake babu wanda ya yi nasara.

    ƙasar dai ta samu 'yancin kai ne daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya a 1976.

    Jam'iyyar Mista Faure ta Unity ta karbi shugabanci ne a wani juyin mulki shekara ɗaya bayan samun 'yancin kai, kuma ta ci gaba da jan ragamar ƙasar a siyasance tun 1993 bayan an bayar da damar tsarin jam'iyyun siyasa masu yawa.

    Mista Ramkalawan ya faɗi shugabancin kasar sau shida kafin wannan nasarar da ya samu a yanzu.

    REUTERS

    Asalin hoton, REUTERS

    Bayanan hoto, Mista Ramkalawan yayin kaɗa ƙuri'arsa a 2006
  7. An sanya dokar hana fitar dare a Sifaniya

    REUTERS

    Asalin hoton, REUTERS

    Sifaniya ta sanya dokar taɓaci a faɗin ƙasar da kuma dokar hana fitar dare a ƙoƙarin da take na yaƙi da take yi da bazuwar annobar korona.

    Firaministan ƙasar Pedro Sanchez ya ce dokar hana zirga-zirgar daren za ta fara aiki ne daga karfe 11:00 na dare zuwa 06:00 na safe daga ranar Lahadi.

    A bangaren dokar taɓacin kuma za a haramta tafiye-tafiye tsakanin yankuna.

    Mista Sanchez ya ce zai nemi majalisar dokokin ƙasar ta sahhale ma shi domin ƙara samar da wasu sabbin dokoki daga kwana 15 zuwa wata shida.

    Annobar korona ta yi wa Sifaniya mummunar ɓarna tun farkon ɓullarta a farkon wannan shekarar, wanda hakan ya sanya ƙaƙaba dokokin hana zirga-zirga masu yawa.

    Kamar dai sauran yankunan Turai, ita ma Sifaniya na fama da wannan annoba a karo na biyu.

  8. Muƙaddashiyar Gwamnan Jihar Kaduna ta kai ziyara wuraren da aka yashe a jiya

    Muƙaddashiyar Gwamnan Jihar Kaduna na wata ziyara ta musamman a wuraren da aka fasa aka wawure kayan abinci da magunguna a jihar.

    Bayan kwashe kayan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC ta sanar da cewa da yawa daga cikin kayan sun lalace wasu kuma an haramta amfani da su dan haka za su iya illata duk wanda ya yi amfani da su.

    A jiya Asabar ne wasu mazauna jihar Kaduna suka far wa ɗakunan ajiyar abinci na gwamnati domin neman kayan tallafin annobar korona.

    Sun kwashi kayan abinci da hatsi da kujeru da wasu kayan wutar lantarki masu yawa.

    Hakan ya janyo an sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomin Chikun da Kaduna ta Kudu, daga baya kuma aka mayar da dokar a faɗin jihar baki ɗaya domin tabbatar da doka da oda.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Sojojin Najeriya 'sun kashe' 'yan Boko Haram 16 a Borno

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun rundunar Operation Fire Ball ta sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda 16 a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

    Muƙaddashin shugaban sashen yaɗa labaran rundunar, Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka ranar Lahadi cikin wata sanarwa, yana mai cewa Operation Fire Ball wani ɓangare ne na rundunar Operation Lafiya Dole da ke yaƙi da 'yan ta'adda.

    Birgediya Janar Onyeuko ya ce dakarunsu sun lalata motar bindiga guda huɗu na 'yan ƙungiyar tare da ƙwato akwatun harsasai yayin harin.

    Ya ce a ranar 21 ga Oktoba sun kula da wasu motoci suna bin bayan jerin gwanon motocinsu da ke kan hanyar mayar da 'yan gudun hijira garin Baga daga Maiduguri, suna ƙoƙarin shiga cikinsu.

    A cewarsa, dakarun sun far musu nan take, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da lalata motar bindiga ɗaya.

    Kazalika, dakarun da ke sansanin Army Super Camp a Magumeri sun kashe mutum 11 a wata arangama da suka yi sannan suka kama wasu makaman harbo jirgi guda uku, a cewar Mista Onyeuko.

    Bayan wannan fafatawar ne kuma aka kashe wasu guda biyu yayin da wasu suka tsere da munanan raunuka.

    A jiya Asabar ma sai da jami'an tsaro suka kashe 'yan Boko Haram shida a Jihar Yobe mai maƙwabtaka, yayin wani hari da 'yan Boko Haram suka kai a garin Babban Gida. Ɗan sanda ɗaya ya rasa ransa a fafatawar.

  10. Dubban matasa sun yashe ɗakin ajiyar kayan abinci a Yolan Adamawa

    Yola

    Asalin hoton, Others

    Dubban matasa sun afka wa wurin ajiyar kayan abinci na gwamnatin Jihar Adamawa a birnin Yola yau Lahadi.

    Fusatattun matasan sun karya ƙofar wurin ne da ke Kwanan Waya a wajen birnin Yola, inda ake ajiye da kayan tallafin annobar korona, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

    Mutane da dama sun ɗauki kansu a bidiyo yayin da suke cikin ɗakunan ajiyar tare da sanya wa a shafukan zumunta, suna masu alfahari da ɗibar abin da suka ce haƙƙinsu ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Wani rukunin jami'an tsaro da aka tura wurin bai iya daƙile matasan ba daga abin da suka saka a gaba.

    Hatta babban titin Yola-Numan da ya haɗa Adamawa da Jihar Gombe an toshe shi saboda yawan masu kwasar kayan, in ji Daily Trust.

  11. Alamomin cutar tsananin damuwa

    Bayanan sautiKu saurari shirin ta hanyar latsa hoton da ke sama

    Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.

    Idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni, hakan ka iya jawo mutum ya kashe kansa ko kuma aikata wani mummunan aiki.

    A kan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko wasu ma su ce rashin hakuri ne ko rashin tawakkalin wanda ya gamu da ita.

    Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba shi ne cuta ce kamar ko wace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum.

    Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kanta.

    Karanta cikakkiyar maƙalar a nan:

  12. An kama 'yan ƙungiyar IPOB takwas a Jihar Rivers

    'Yan sandan Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya sun kama 'yan ƙungiyar IPOB guda takwas a yankin Ƙaramar Hukumar Oyigbo ta jihar.

    Labarin kama 'yan ƙungiyar wadda ke son kafa ƙasar Biafra a Najeriya, na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin 'Yan Sanda na jihar, Nnamdi Omoni ya fitar.

    A ranar Juma'a Gwamna Nyesume Wike ya sanar da bayar da ladan naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayyana maɓoyar jagoran ƙungiyar a jihar.

    A watan Satumban 2017 ne Shugaba Buhari ya haramta ayyukan ƙungiyar a ƙasa baki ɗaya.

    A cewar sanarwar, 'yan daban ƙungiyar IPOB kusan 500 ne suka ƙona ofishin 'yan sanda na Afam tare da lalata ababen hawa kusan 15 ciki har da motar silke ta 'yan sanda.

    Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa an kashe 'yan sanda biyu yayin harin.

  13. Victor Moses ya sadaukar da ƙwallon da ya ci ga masu zanga-zangar EndSars

    Victor Moses

    Asalin hoton, @VictorMoses

    Ɗan ƙwallon tawagar Super Eagles ta Najeriya Victor Moses ya sadaukar da ƙwallon da ya ci wa ƙungiyarsa ta Spartak ga masu zanga-zangar EndSars.

    Moses ya ci ƙwallon ne a wasansa na biyu ga ƙungiyar mai buga gasar firimiya ta ƙasar Rasha, inda ta casa Krasnodar da ci 3-1 ranar Asabar.

    An kwashe mako biyu ana zanga-zangar neman gyara da kuma nuna ɓacin rai kan cin zalin da 'yan sanda ke yi a Najeriya, abin da ya jawo aka rusa rundunar SARS mai yaƙi da 'yan fashi. Kazalika, zanga-zangar ta rikiɗe zuwa ƙone-ƙone da sace-sace a wasu sassa.

    "Nasara mai daɗi a yau kuma na ji daɗin cin ƙwallota ta farko ga ƙungiyar," in ji Moses cikin wani saƙon Twitter.

    "Na sadaukar da ƙwallon ga al'ummar Najeriya. Tura ta kai bango. 'Yan Najeriya na da haƙƙin yin zanga-zanga ba tare da an kashe su ba. PrayForNigeria."

    Ɗan wasan mai shekara 29 ya koma Spartak ne a matsayin aro daga Chelsea a farkon kakar wasa ta 2020-21 kan yarjejeniyar shekara ɗaya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Gwamnatin Jihar Taraba ta saka dokar hana fita a Jalingo

    Alhaji Haruna Manu

    Asalin hoton, NAN

    Gwamnatin Jihar Taraba ta saka dokar hana fita a Jalingo babban birnin jihar biyo bayan wawashe wurin ajiyar kayan abinci da matasa suka yi.

    Mataimakin Gwamna Alhaji Haruna Manu ne ya sanar da dokar a daren Asabar yayin wani jawabi ga al'ummar jihar.

    Manu ya koka kan yadda matasan suka ɓalle wuraren ajiyar sannan suka yashe kayan da aka tanada domin tallafa wa mabuƙata.

    "Saboda haka gwamnati ta saka dokar hana fita daga ƙarfe 11:00 na daren Asabar zuwa 8:00 na safiyar Litinin," in ji mataimakin gwamnan.

    Ita ma gwamnatin Jihar Kaduna ta saka irin wannan dokar saboda yashe wuraren ajiyar kayan abincin da dubban matasa suka yi.

    Dokar ta Kaduna wadda ta fara aiki a yammacin Asabar, ta awa 24 ce kuma za ta yi aiki ne a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.

    Tun farko an fara saka dokar ne a Jihar Filato, inda aka ga dubban matasa a Jos na ɗibar kayan abincin da aka ajiye domin bayar da su a matsayin tallafin annobar korona.

  15. An kashe ɗan sanda da 'yan Boko Haram shida a Yobe

    Boko Haram

    Asalin hoton, Boko Haram

    Wani ɗan sanda da kuma mayaƙan ƙungiyar Boko haram shida sun rasa rayukansu yayin wata fafatawa a Jihar Yobe.

    Kakakin "Yan Sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa da Kafar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin a jiya Asabar.

    Lamarin ya faru ne a Babban Gida biyo bayan harin da 'yan bindigar suka kai a cikin motoci ƙirar Toyota Hilux guda huɗu da misalin ƙarfe 4:00 na yammacin Asabar.

    Garin Babban Gida yana da nisan kilomita 50 daga Damaturu, babban birnin jihar.

    Wakilin kafar talabijin ta Channels ya ga dakarun sojan Najeriya na yunƙurin fita domin tunkarar maharan.

    Kazalika, rahotanni sun ce an cinna wa wasu ɓangarori na ofishin 'yan sandan yankin wuta da kuma wani sansanin sojoji.

  16. Tarihin yankin Nagorno-Karabakh da na bangon duniya

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku ji amsoshin tambayoyin

    Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya amsa tambayoyi game da tarihin yankin Nagorno-Karabakh, wanda ƙasashen Armenia da Azerbaijan ke yaƙi yanzu haka a kansa.

    Sai kuma tambaya kan ko da gaske akwai bangon duniya.

    Nabeela Muktar Uba ce ta gabatar da shirin.

  17. Yadda aka ƙirƙiri rundunar SWAT da yadda za ta yi aiki a Najeriya

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama ku saurari ministan ayyukan 'yan sandan Najeriya

    Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya tattauna da Ministan Ma'aikatar 'Yan Sanda a Najeriya kan yadda aka ƙirƙiri rundunar SWAT da yadda za ta yi aiki.

    Muhammad Maigari Dingyadi ya ce 'yan sandan sabuwar rundunar za su karɓi horo na tsawon wata ɗaya.

  18. 'Yan cirani 200 sun ɓata bayan jirgin ruwansu ya kife

    'Yan cirani

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla 'yan cirani 200 ne suka ɓata a gabar tekun Senegal kilomita 80 kafin su isa Ganga.

    Lamarin ya faru ne bayan da kwalekwalen da suke ciki ya kama da wuta ya kuma nutse da su.

    Rahotanni sun ce suna kan hanyarsu ce ta isa Tsibirin Canary da ke Sfaniya a lokacin da ɗaya daga cikin injiniyoyin jirgin ya samu matsala kuma a daidai lokacin da ma'aikatan jirgin ke kokarin gyara shi ne ya yi bindinga.

    Sfaniya ta sha alwashin tsaurara tsaro a Tsibirin Canary da nufin daƙile kwararar yan cirani zuwa Turai.

  19. Ƙarin mutum 48 ne kacal suka kamu da korona a Najeriya

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 61,930 bayan da aka gano ƙarin mutum 48 da suka kamu da cutar ranar Asabar.

    A jihar Legas, an samu karin mutum 18 da suka kamu da cutar sai Abuja babban birnin Najeria mai mutum 13.

    Sauran jihohin da aka samu sabbin kamu akwai Kaduna mai mutum 6, sai Rivers da Ogun da ke da mutum 5-5. Akwai kuma jihar Ondo mai mutum 1.

    Cikin mutum 61,930 da suka kamu da cutar a fadin Najeriya zuwa yanzu, mutum 57,285 sun warke yayin da 1,129 suka rasa rayukansu.

  20. Barka da hantsi

    Barkanku da hantsin Lahadi, da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya yadda ya kamata.

    Ku kasance tare da ni Umar Mikail a yanzu domin sanin yadda duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.