Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 61,882 bayan da aka gano ƙarin mutum 77 da suka kamu da cutar ranar Juma'a.
Haka nan wasu mutum biyu sun mutu a sabbin alƙaluman - adadinsu ya zama 1,127.
A Jihar Legas, an samu karin mutum 71 da suka kamu da cutar sai Kaduna mai mutum 20.
Sauran jihohin da aka samu sabbin kamu akwai Rivers mai mutum 19, Abuja na da huɗu, yayin da Osun ke da mutum uku.
Jihohin Osun da Sokoto da Benue da kuma Kwara na da 2-2 kowannensu, sai kuma Imo da Ogun masu 1-1.
A jumullance mutum 61,882 zuwa yanzu korona ta kama a fadin Najeriya, cikinsu mutum 57,190 sun warke, yayin da 1,127 suka rasa rayukansu.