Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a ƙaramar hukuma biyu

Wannan shafin na kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Rufewa

    Nan za mu rufe wannan shafin da muka shafe yinin Asabar muna kawo labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu gobe Lahadi inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Za ku iya zuwa har kasan wannan shafin domin karanta abubuwan da suka faru.

  2. Habasha ta caccaki Trump kan Kogin Nilu

    Kasar Habasha ta ce ba za ta amince da kowaceirin barazana bakanbabbar madatsar ruwa da ta ke ginawa a Kogin Nilu, bayan Shugaba Trump ya yi barazanar cewaMasar za ta tarwatsa shi.

    Ministan harkokin wajen Habasha ya fada wa jakadan Amurkacewa abin kyama ne gawani shugaban Amurka mai ci,ya yi kokarin haddasayaki tsakanin Habasha da Masar.

    Tarayyar Turaita ce an cimma yarjejeniya kan madatsar ruwan, kuma yanzu ba lokaci ba ne na kara haifar da wani tashin hankali.

    Kasashen Sudan da Masar na fargaba kan aikin madatsar ruwan da Habasha ke yi, zai haifar da ƙafewar ruwan da suke samu daga kogin na Nilu.

  3. Erdogan ya ce Macron na buƙatar gwajin ƙwaƙwalwa kan manufarsa ga Musulmi

    Erdogan da Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya caccaki takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, kan manufofinsa ga Musulmai, inda ya ce shugaban na bukatar "binciken kwakwalwa".

    Kalaman sun biyo bayan alƙawarin da Macron ya yi ne cewa zai kare al'adun ƙasarsa na rashin bin kowane addini daga masu tsaurin addini bayan kisan wani malamin makaranta da ake zargin masu tsaurin kishin Musulunci da aikatawa.

    Shugaban ya sanar da sabbin matakai ciki har da tsaurara saka ido kan tallafin da masallatai ke samu daga ƙasashen waje.

    Haka nan Erdogan ya soki wani bincike da aka yi kan wani masallaci a birnin Berlin, wadda aka yi shi a kan harkokin kuɗin masallacin.

    Ya ce tauye haƙƙin 'yan ƙasa Musulmai ne, sannan ya kira shi da mulkin son-kai.

  4. Trump ya kaɗa kuri'arsa a zaɓen Amurka

    Shugaban Amurka Donald Trump ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen shugaban ƙasar na Nuwamban 2020.

    "Yanzun nan na jefa ƙuri'a. Abin alfahari!" Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter.

    Kundin tsarin mulkin ƙasar ya bayar da damar fara kaɗa ƙuri'a tun kafin ranar zaɓe.

    Abokoin hamayyarsa na Dimocrat Joe Biden bai kaɗa tasa ƙuri'ar ba tukunna.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Labarai da dumi-dumi, Gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana fita a ƙaramar hukuma biyu

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta saka dokar hana fita a wasu yankuna na ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da kuma Chukun na jihar ta tsawon awa 24.

    Dokar za ta yi aiki ne a unguwannin Barnawa da Kakuri da Television, waɗanda ke Kaduna ta Kudu.

    Sai kuma Maraban Rido da Sabon Tasha da Narayi da Unguwan Romi da ke Chukun.

    Wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar ta ce dokar za ta fara aiki ne nan take.

    Aruwan ya yi kira ga mazauna jihar da su guji tayar da tarzoma da kauce wa faɗawa tarkon masu tayar da husuma.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. 'Yan bindiga sun kashe yara shida a Kamaru

    Kamaru

    Aƙalla yara shida ne aka kashe a wani hari da 'yan bindiga suka kai a wata makaranta da ke kudu maso yammacin Kamaru.

    Majiyoyi da dama sun shaida wa BBC cewa mayaƙa 'yan tawaye sun kutsa kai cikin makarantar Mother Francisca a Fiango sannan suka buɗe wuta.

    Wasu yaran 12 sun jikkata yayin harin.

  7. Ba za mu taɓa ja da baya ba kan madatsar ruwan Kogin Nilu - Habasha

    Habasha

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Habasha ya ce ƙasarsa "ba za ta taɓa miƙa wuya ba" bayan Shugaban Amurka Trump ya nuna cewa Masar ka iya lalata madatsar ruwan da Habashar ke ginawa a Kogin Nilu.

    Madatsar ruwan da aka yi wa laƙabi da Grand Ethiopian Renaissance Dam, ta haddasa taƙaddama tsakanin ƙasashen Habasha da Masar da Sudan.

    Trump ya ce Masar ba lallai ne ta ƙyale madatsar ba kuma akwai yiwuwar ta lalata ta.

    Habasha na ganin cewa Amurka na goyon bayan Masar ne a turka-turkar.

    Amurka ta sanar a watan Satumba cewa za ta katse wasu daga cikin tallafin da take bai wa Habasha bayan ta fara cika wata ma'ajiyar ruwa da ruwa, wadda ke bayan madatsar a watan Yuli.

  8. Gwamnatin Filato ta tabbatar da wawashe wuraren ajiyar kayan abinci a jihar

    Jos

    Asalin hoton, Others

    Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da rahotannin wawashe ɗakunan ajiyar kayan tallafin annobar korona da dubban mutane suka yi a Jos, babban birnin jihar.

    Sai dai ta ce ba gaskiya ba ne batun da ake yaɗawa cewa ɓoye kayayyakin ta yi, tana mai cewa zanga-zangar EndSars ce ta tilasta dakatar da raba wa mabuƙata.

    Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai Dan Manjang ya fitar a yau Asabar, an yashe wuraren ajiyar abinci na Jos da Bukuru ranar Asabar 24 ga Oktoba.

    An ga dubban mutane a wasu bidiyo daban-daban da suka karaɗe shafukan sada zumunta suna ɗibar kayayyaki daga wurin ajiyar abinci a Jos.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    "Gwamnati ta yi tur da wannan aiki sannan tana jaddada cewa ba ɓoye su ta yi ba," in ji sanarwar.

    Ta ƙara da cewa a ranar 16 ga Oktoba Ministar Ma'aikatar Agaji, Cigaban Al'umma da Kare Afkuwar Bala'i, Sadiya Umar Farouk, da Ministar Mata Dame Paullen Tallen, suka kai kayan tare da ma'aikatan da za su raba su.

  9. Fusatattun matasa sun wawashe gidan sanata a Najeriya

    Teslim Folarin

    Asalin hoton, @teslimkfolarin

    Wasu fusatattun matasa sun afka gidan sanata mai wakiltar Mazaɓar Oyo ta Tsakiya, Teslim Folarin, inda suka wawashe kayayyaki.

    Jaridar Premium Times ta ruwaito a yau Asabar cewa matasan sun yi awon gaba da babura da firji da injinan niƙa da sauran kayayyaki na tallafa wa mutane a gidansa na Ƙaramar Hukumar Oluyole ta Jihar Oyo.

    Kazalika, jaridar ta ruwaito yadda aka wawashe gidan tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai Yusuff Lasun a Jihar Osun.

    Haka nan wasu matasa sun yi yunƙurin shiga ginin Arts and Culture da ke Area 10 a Abuja domin ɗebe kayan abinci na tallafin annobar korona da suka ce an ajiye a ciki.

  10. 'Yan sanda sun harba bindiga a Abuja don hana matasa ɗibar abincin tallafi

    Rahotanni na cewa jami'an tsaro sun yi harbe-harbe domin tarwatsa wani cincirundon matasa da suka taru don wawashe wurin ajiyar abinci a Abuja.

    'Yan Kasuwar UTC da ke Garki Area 10 sun ji harbe-harbe yayin da mutanen suka yi yunƙurin shiga ginin Arts and Culture, suna iƙirarin cewa gwamnati ta jibge kayan abincin tallafin korona a ciki.

    Wasu bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna matasan carko-carko a ƙofar ginin amma suka tarwatsae bayan sun ji harbin bindiga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Waɗanda aka kashe a yaƙin Nagorno-Karabakh sun ƙaru zuwa 963

    Nagorno-Karabakh

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar tsaro ta yankin Nagorno-Karabakh da ƙasashen Armenia da Azerbaijan ke yaƙi a kansa ta ce 'yan Armenia da aka kashe sun ƙaru daga 27 zuwa 963.

    kamfanin dillancin labarai na Interfax ne ya ruwaito na ma'aikatar na bayyana hakan a yau Asabar, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

    Yaƙi ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu a ranar 27 ga Satumban 2020 kan yankin wanda 'yan Armenia ke iko da shi a cikin Azerbaijan.

    Rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta har biyu da Rasha ta jagoranta sun sa ana matuƙar fargabar kawo ƙarshen yaƙin.

  12. Mawaƙi Hassan Wayam ya rasu

    Hassan Wayam

    Asalin hoton, Bello Wayam

    Allah Ya yi wa mawaƙin Hausa na gargajiya Hassan Wayam rasuwa a daren Juma'a.

    Ɗan marigayin mai suna Hassan Wayam Bello, ya shaida wa BBC mahaifin nasa ya yi fama da jinya kafin rasuwarsa kuma tuni aka yi jana'izarsa a garin Zariya, Layin Zomo a safiyar yau Asabar.

    Marigayin ya rasu ya bar 'ya'ya 13 da kuma mata ɗaya.

    Hassan Wayam

    Asalin hoton, Bello Wayam

    Duk da cewa babu tabbas kan ranar haihuwarsa, Hassan ya ce mahaifin nasu ya shida musu cewa zai kai shekara 75.

    An haifi Hassan Wayam a garin Gwadda da ke Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

    Kafin rasuwarsa, Wayam makaɗin kukuma ne kuma ya yi waƙoƙi da dama irin na gargajiyar Hausa.

  13. Gwamnan Jihar Cross River ya saka dokar hana fita

    Ben Ayade

    Asalin hoton, @senatorbenayade

    Gwamnan Jihar Cross River a kudu maso kudancin Najeriya, Ben Ayade ya saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar.

    A cewar wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai Christian Ita ya fitar a jiya Juma'a, dokar ta fara aiki ne nan take.

    Sanarwar ta ce an saka dokar ne saboda tashin hankalin da wasu suka haifar da sunan zanga-zangar EndSars.

    Bayan ya nemi mazauna jihar da su bi dokar sau da ƙafa, Christian Ita ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya saɓa ta jami'an taro za su kama shi.

    Tuni Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya sassauta dokar hana fita da aka saka sakamakon zanga-zangar da ta rikiɗe zuwa ƙone-ƙone da satar kayan jama'a ranar Talata.

    Su ma jihohin Osun da Ondo sun ɗage dokar.

  14. Gwamnan Rivers zai biya ladan miliyan 50 ga wanda ya faɗi inda shugaban IPOB yake

    Gwamna Nyesom Wike

    Asalin hoton, @GovWike

    Gwamnan Jihar Rivers a kudancin Najeriya ya jaddada haramta ƙungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB) a jihar, wadda ke fafutikar neman kafa ƙasar Biafra.

    A watan Satumban 2019 ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan wani umarnin gwamnati da ya haramta ƙungiyar da ayyukanta a ƙasa baki ɗaya.

    Gwamna Nyesom Wike wanda ya bayyana haka cikin wani jawabi da ya yi wa jama'ar jihar a daren Juma'a, ya ce daga yanzu an haramta dukkanin wata zanga-zanga da ƙungiyar za ta gudanar a faɗin jihar.

    Gwamnan ya ayyana Stanley Mgbere a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa jagorantar zanga-zangar da ta haddasa tashin hankali da lalata dunkiya a Ƙaramar Hukumar Oyigbo ta jihar.

    Kazalika, Wike ya ce zai bayar da naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Stanley Mgbere da gurfanar da shi a gaban kotu.

    "An umarci jami'an tsaro da su daƙile duk wata zanga-zangar IPOB a Rivers ko wani ɓangare na jihar tare da kama duk wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗan ƙungiyar," a cewar wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati za ta yi dokar da za ta jaddada haramcin ƙungiyar.

  15. Shugaban Poland ya kamu da cutar korona

    Shugaban Poland Andrzej Duda

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Poland Andrzej Duda ya kamu da cutar korona, a cewar wani ministan gwamnatinsa.

    Mista Duda mai shekara 48, bai nuna alamun cutar ba, wanda gwaji ya nuna ya kamu da ita ranar Juma'a, kamar yadda Blazej Spychalski ya sanar a yau Asabar.

    Shugaban ya bi sahun 'yan kaɗan daga cikin shugabannin duniya da suka kamu da cutar - Donald Trump na Amurka da Boris Johnson na Birtaniya da Bolsonaro na Brazil na daga cikinsu.

    Poland na fuskantar ƙaruwa a yawan masu kamuwa da cutar, inda aka samu mutum 13,600 na mafi yawan adadi a ranar Juma'a.

    A yanzu ƙasar ta saka dokar kulle maras tsauri wadda ta haɗa da rufe makarantu da wuraren cin abinci.

  16. Jakadan Indiya a Najeriya ya ziyarci Fadar Sarkin Kano

    Kano

    Asalin hoton, @india_nigeria

    Bayanan hoto, Ƙaramin jakadan Indiya a Najeriya ya kai wa Sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ziyara
    Kano

    Asalin hoton, @india_nigeria

    Bayanan hoto, Abhay Thakur ya kai ziyarar ne ranar Juma'a
    Kano

    Asalin hoton, @india_nigeria

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Ƙarin mutum 83,000 sun kamu da cutar korona a Amurka a rana guda

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Cutar korona na ci gaba da ratsa sassan Amurka, yayin da aka samu adadi mafi yawa da suka kamu da ita a rana guda.

    Alƙaluman da aka samu daga cibiyoyin lafiya na yankuna sun nuna cewa mutum 83,010 ne suka kamu da cutar ranar Juma'a.

    Likitan fiɗa Jerome Adams ya yi gargaɗin cewa adadin waɗanda ake kai wa asibiti na ƙaruwa amma ana samun raguwar waɗanda ke rasuwa saboda kyakkyawar kulawa da ake ba su.

    Wannan lamari na faruwa ne yayin da kamfanonin AstraZeneca da Johnson & Johnson suka ci gaba da yin gwajin rigakafin cutar bayan an sahale musu yin hakan.

    Bugu da ƙari, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa ƙasashen Yammacin Duniya na cikin "haɗari mai girma".

  18. Dubban mata sun yi zanga-zangar hana zubar da ciki

    Poland

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban mata sun gudanar da zanga-zanga a birane da dama na ƙasar Poland domin nuna adawa da matakin kotu na hana zubar da ciki.

    Sai dai hukuncin ya yi sassauci kan cikin da ya samu ta hanyar fyade ko kuma idan zai iya jefa mai dauke da shi cikin haɗari.

    Ana gudanar da zanga-zangar duk da tsauraran matakan kullen korona da ke ci gaba da aiki a faɗin Poland.

  19. Cutar korona ta kashe mutum biyu a Najeriya ranar Juma'a

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 61,882 bayan da aka gano ƙarin mutum 77 da suka kamu da cutar ranar Juma'a.

    Haka nan wasu mutum biyu sun mutu a sabbin alƙaluman - adadinsu ya zama 1,127.

    A Jihar Legas, an samu karin mutum 71 da suka kamu da cutar sai Kaduna mai mutum 20.

    Sauran jihohin da aka samu sabbin kamu akwai Rivers mai mutum 19, Abuja na da huɗu, yayin da Osun ke da mutum uku.

    Jihohin Osun da Sokoto da Benue da kuma Kwara na da 2-2 kowannensu, sai kuma Imo da Ogun masu 1-1.

    A jumullance mutum 61,882 zuwa yanzu korona ta kama a fadin Najeriya, cikinsu mutum 57,190 sun warke, yayin da 1,127 suka rasa rayukansu.

  20. Maraba

    Umar Mikail na muku barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Idan kuka biyo mu za ku san yadda take ciki a yau Asabar musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Mu je zuwa!