Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Zanga-zangar EndSars ta rikiɗe zuwa rikici a Abuja

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Ana zargin 'yan sanda da kashe matashi a Kano ranar Lahadi

    Cincirundon matasa sun hau titi a Kano domin nuna ɓacin ransu sakamakon kisan wani matashi da ake zargin 'yan sanda da yi.

    Matasan sun yi zargin cewa 'yan sanda sun je kama mutum biyu a Unguwar Ƙofar Mata, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu sannan ɗayan ya tsere.

    BBC ta tuntunɓi kakakin rundunar 'yan sanda ta Jihar Kano, sai dai ya ce ba zai iya yin magana ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

    Masu zanga-zangar sun ƙona tayoyi a kan titin Ƙofar Mata da ke ƙwaryar birnin Kano. A yanzu haka an rufe hanyar zuwa Kasuwar Kantin Kwari.

    Lamarin na zuwa ne yayin da aka shafe mako biyu a jere ana zanga-zangar Allah-wadai da cin zarafin da 'yan sanda ke aikatawa a kusuan dukkanin jihohin Najeriya, abin da ya haddasa rushe rundunar SARS mai yaƙi da fashi da makami.

  2. El-Rufai ya kafa kwamitin bincike kan cin zarafin 'yan sanda a Kaduna

    Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin shari'a da zai binciki cin zarafin da 'yan sanda suka aikata a jihar.

    Wannan ya biyo bayan umarnin da Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa ta bayar na matakan da za a ɗauka domin yin gyara ga ayyukan 'yan sandan ƙasar kamar yadda masu zanga-zangar #EndSARS suka buƙata.

    Cikin sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, mai taimaka wa Gwamna Nasir El-Rufai kan kafafen yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya ce za a rantsar da kwamitin da ƙarfe 11:00 na ranar yau Asabar.

    Mambobin kwamitin sun haɗa da:

    • Mai Shari'a (mai ritaya) David Shiri Wyom - Shugaba
    • AIG (mai ritaya) Lawal Tanko
    • Rebecca Sako-John - Wakiliyar ƙungiyoyin farar hula
    • Mustapha Jumare - Wakilin ƙungiyoyin farar hula
    • Yakubu Umar Ibrahim - Wakilin ɗalibai
    • Nathenial Sheyi Bagudu - Wakilin matasa
    • Inna Binta Audu - Wakiliyar Hukumar Kare Haƙƙi ta Ƙasa
    • Hajara Abubakar - Wakiliyar Antoni Janar na Jihar Kaduna

    Kaduna ta zama jiha ta huɗu da ta kafa kwamitin, wanda ake sa ran dukkanin jihohi za su kafa domin bincike da kuma biyan diyya ga waɗanda 'yan sanda suka ci wa zarafi a kowacce jiha a Najeriya.

    Sauran jihohin da suka kafa kwamitocin sun haɗa da Legas da Filato da Ogun.

  3. Ba mu muka ce a kama 'yan Najeriya a Masar ba – Gwamnatin Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta musanta hannunta a kamen 'yan ƙasar masu zanga-zangar #EndSARS da aka yi a birnin Alƙahira na Masar.

    Shugabar Hukumar 'Yan Najeriya mazauna Ƙasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa, ta ce hukumomin Masar sun tabbatar da dokokinsu ne kawai game da taron jama'a.

    Ta ƙara da cewa waɗanda aka kama ɗin ba a ofishin jakadancin Najeriya aka kama su ba, amma ofishin zai tuntuɓi hukumomin Masar domin a sake su.

    Zanga-zangar #EndSARS, wadda ke neman kawo ƙarshen cin zarafin da 'yan sanda ke aikatawa, ta yaɗu zuwa sassan duniya, inda mazauna ƙasashen waje ke taya 'yan Najeriya.

    Gwamnati ta rusa rundunar SARS da 'yan ƙasa suka zarga da kashe mutane ba bisa ƙa'ida ba da cin hanci, amma duk da haka masu zanga-zangar ba su saurara ba.

  4. An naɗa mace ta farko a Majalisar Shura ta Saudiyya

    Sarki Salman na Saudiyya ya naɗa Dr. Hanan Bint Abdulrahim bin Nutlaq al-Ahmadi a matsayin mace ta farko da za ta riƙe muƙamin mataimakiyar shugaban Majalisar Shura.

    A Saudiyya, ƴan majalisar Shura ne ke da alhakin gabatar da dokoki domin amincewar masarauta.

    Naɗin nata ya zo ne yayin wasu sauye-sauye da Sarki Salman ya aiwatar a manyan hukumomin ƙasar, waɗanda suka haɗa da Majalisar Shura da sauran harkokin addini.

    Haka ma an naɗa sabon alkalin-alkalan Kotun Ƙoli ta Saudiyyar.

  5. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum biyu a Najeriya

    Ƙarin mutum biyu sun mutu sakamakon cutar korona a Najeriya, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Alƙaluman NCDC sun nuna cewa zuwa yanzu jumillar waɗanda cutar ta kashe - tun daga watan Fabarairu da ta ɓulla a Najeriya - sun kai 1,125.

    Kazalika, ƙarin mutum 133 sun kamu da cutar a jihohi tara da suka haɗa da Legas, wadda ke kan gaba da mutum 90, sai Rivers mai 13 da kuma Kaduna da Abuja masu 8-8 kowaccensu.

    Jumillar waɗanda annobar cutar korona ta kama a Najeriya sun zama 61,440, sannan kuma an sallami mutum 56,611 bayan sun warke.

  6. Maraba

    Sannunku da shigowa wannan shafi. Idan kuka biyo mu za ku samu rahotanni kai-tsaye daga sassan duniya musamman a Najeriya da Nijar da kuma maƙwabtansu har zuwa daren yau Litinin.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a yanzu.