Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan bindiga sun kashe wani basarake a Kaduna

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Mustapha Musa Kaita

  1. Hatsarin mota ya kashe mutum biyar a Adamawa

    Hukumar Kiyaye Haɗura ta Najeriya (FRSC) ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a Jilima da ke Ƙaramar Hukumar Mayo Belwa ta Jihar Adamawa.

    Hatsarin na manyan tirelolin da ke dakon shanu biyu ya auku ne ranar Asabar a kan babban titin Mayo Belwa zuwa Ganye, yayin da motocin suka bar garin Ngurore zuwa cin kasuwar dabbobi a garin Ganye.

    Kazalika, wasu mutum 32 sun ji munanan raunuka daga cikin 53 da lamarin ya rutsa da su, a cewar jami'in rundunar FRSC reshen Jihar Adamawa Aminu Ibrahim.

    Wani da ya tsallake rijiya da baya ya alaƙanta aukuwar hatsaarin da tuƙin ganganci, inda ya ce direbobin biyu na “tsere ne domin nuna bajintarsu ta tuki”.

    “Gudu da tuƙin ganganci ne suka haddasa hatsarin saboda fasinjojin motocin sun yi ta ziga direbobin tare da yi musu kirari don su yi gudu," in ji Aminu Ibrahim.

    A watan Maris na shekarar 2017 ma sai da hatsarin motar shanu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 35 a garin Ngurore na jihar Adamawa.

    Asarar rayuka sakamakon hatsarin manyan motoci da ke ɗaukar shanu na aukuwa lokaci zuwa lokaci a manyan titunan Najeriya, inda sau da dama hukumomi ke alaƙanta hakan da tuƙin ganganci ko kuma lodin da ya wuce kima.

    Sai dai su kuma direbobin motocin sun fi ɗaura alhakin hakan kan lalacewar hanyoyi.

  2. Gwamnan Oyo ya koka game da rashin ikon gwamnoni kan 'yan sanda a Najeriya

    Gwamnan Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, Seyi Makinde, ya bayyana takaici game da yadda ake yi wa gwamnoni laƙabi da "Shugabannin Tsaro" a jihohinsu wato "Chief Security Officers" a Turance, yayin da kuma ba su da wani iko kan rundunar 'yan sanda.

    A tsarin da Najeriya ke kai yanzu, jami'an 'yan sandan ƙasar na amsa umarnin Sufeto Janar ne, wanda shi kuma yake amsa na shugaban ƙasa.

    Gwamna Makinde ya bayyana takaicin nasa ne a shafinsa na Twitter ranar Asabar, yana mai yin alƙawarin gudanar da bincike kan kisan wani mai zanga-zangar neman rushe 'yan sandan rundunar SARS wato #EndSARS a Ogbomosho ta jihar Oyo.

    Rahotanni sun ce an harbi Jimoh Isiaka yayin zanga-zangar kuma ya mutu a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Bowen. Kazalika gwamnan ya tabbatar da wasu mutum biyar da suka jikkata a zanga-zangar da aka gudanar a sassa da yawa a ƙasar.

    Gwamnan ya ce: "Zanga-zangar #EndDSARS na tabbatar da yadda al'amura suka lalace. Gazawa ce daga waɗanda aka amince wa domin su kare rayuwar 'yan ƙasa.

    "Kazalika, hakan na ɗora alamar tambaya kan dalilin da ya sa ake kiran gwamnonin jihohi da Shugabannin Tsaro a jihohinsu, yayin da kuma ba su da cikakken iko kan 'yan sandan."

    Da ma dai an daɗe ana tafka muhawara a Najeriya kan bai wa jihohi damar ƙirƙirar rundunar 'yan sanda mallakarsu ba kamar yadda tsarin yake ba a yanzu.

  3. Ana ci gaba da jiran sanar da sakamakon zaɓen Ondo

    Bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙaramar hukuma 12, hukumar INEC ta tafi hutu tun ƙarfe 2:30 na dare.

    Ana ci gaba da jira a cibiyar tattara sakamako da ke Alagbaka a birnin Akure.

    Yanzu haka ana sa ran samun sakamakon ƙaramar hukuma 6 idan an dawo daga hutun rabin loƙacin.

    Tun farko jami'an tattara sakamakon sun bayyana cewa za a dawo bayyana sakamakon da ƙarfe 9:00 na safiyar nan.

    Ƙananan hukumomin da aka sanar ya zuwa yanzu su ne:

    • Akoko North-West - APC: 15, 809 - PDP: 10,320
    • Akoko North-East - APC: 16,572 - PDP: 8,380
    • Akoko South-East - APC: 9,419 - PDP: 4,003
    • Akoko South-West - APC: 21,232 - PDP: 15,055
    • Ifedore - PDP: 11,852 - APC:9,350
    • Akure North - PDP: 12,263 - APC: 9,546
    • Ile-Oluji/Okeigbo - APC: 13,278 - PDP: 9,231
    • Akure South - PDP: 47,627 - APC: 17,277
    • Owo - APC: 35,957 - PDP: 5,311
    • Idanre - APC: 11,286 - PDP: 7,499 Ondo
    • East - APC: 6,485 - PDP: 4,049
    • Irele - APC: 12,643 - ZLP: 5,904
  4. Maraba

    Za mu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa a zaɓen gwamnan Jihar Ondo, inda ya zuwa yanzu aka bayyana sakamakon ƙaramar hukuma 12 cikin 18 na jihar.

    Umar Mikail ke cewa ku biyo mu.