A yau Asabar masu katin kaɗa ƙuri'a ke zaɓar gwamna a Jihar Ondo da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya domin zaɓar gwamnan jiharsu.
Al'ummar Ondo ba su yi zaɓen gwamna ba lokacin da sauran jihohi suka kaɗa ƙuri'u a 2019 sakamakon wani hukuncin kotu a 2017.
A cewar hukumar zaɓe ta INEC, mutum 1,822,346 ne suka yi rijistar kaɗa ƙuri'a a zaɓen na ranar 10 ga watan Oktoba.
Jam'iyyu 17 ne za su fafata ciki har da APC da PDP, jam'iyyu mafi girma a Najeriya.
Sai dai babu mace ko ɗaya a cikin 'yan takarar.
Gwamna mai-ci Arakurin Oluwarotimi Akeredolu wanda na jam'iyyar APC mai mulki, da Eyitayo Jegede na jam'iyyar PDP, da kuma Agboola Ajayi na jam'iyyar ZLP wanda tsohon kwamishinan shari'a ne, su ne suka fi shahara.
Waɗannan 'yan takarar uku ne mafiya shahara ganin yadda jam'iyyunsu ke da ƙarfi a ƙananan hukumomi 18 na jihar.
Jegede na ZLP na yin takarar ne a karo na biyu bayan ya nema a 2016.
Dukkanin 'yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaɓun sanata uku daban-daban - Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.